Skip to content
Part 4 of 13 in the Series Fitsarin Fako by Sanah Matazu

Kwanci ta shi babu wuya wajen ubangiji, Aufana ta yi ɓul da ita sakammakon kulawar da take samu. Sosai Abdallah yake kulawa da mu. A ɓangare ɗaya kuma mun maida hankali sossai wajen ganin mun kawo ƙarshan Alhaji Labaran amma abin ya ci tura domin duk wata kafa ya kangeta.

Gabaɗaya Abdallah ya fita a hayyacinsa ya rame ya zabge, ba mu ƙara shiga tashin hankali ba sai da muka wayi gari gidansu Abdallah an kuna masa wuta cikin dare komai ya ƙone. Da ƙyar Abdallah ya sha, bai tsira da komai ba sai waya da Atm da kuma takardunsa na makaranta waɗanda gabaɗaya suna wajena.

Babu wanda bai tausayawa halin da ya sami kansa ba. Abin mamaki sai kuma ga takardun sammaci daga banki wai ana bin Abba kuɗi. Wanda Abdallah ya tabbatar min da duk shirin Alhaji Labaran ne.

Duk wata dukiya da ya mallaka sai da ta zamo babu ita domin Alhaji Labaran ya bi ta ƙarƙashin ƙasa ya handame komai inda ya fitar da takardun bogi na shaidar kuɗaɗen da yake bin Abbansu Abddallah masu yawa.

Babu wata shaida da Abdallah zai gabatar komai ya ƙone. Abu ɗaya ya dogara da shi lauyan mahaifinsa sai dai abin da ya ɗimautashi shi ne, samunsa a matsayin lauyan Alhaji Labaran dole muna ji muna gani muka zubawa sarautar Allah idanu amma ba mu fasa faɗawa Ubangiji ba.

Sai dai ganin yanayin da yake ciki hankalina ya yi mugun ta shi matuƙa. Abdallah ba shi da nutsuwa, sai ya zamana ganinsa ya soma yi min wuya rayuwa ta soma yi mana ƙunci.

Domin komai Yaya Kamala zai shigo da shi ina ƙoƙarin ganin ban ci ba kuma ɗiyata ma ba ta ci ba. Rashin samu daga Abdallah ya sa na yanke shawarar dawo da sayar da abincinmu da muka watsar da sauran abin da ya rage mana domin bana buƙatar in gina rayuwar ɗiyata da haram.

Na lura Inna na yawan ƙorafi kan ciwon yaya Kamala yadda yake kwan gaba kwan baya, sai ya yi kamar ya warke amma wasu lokutana idan ya tafka shirme sai Allah. Saka damuwar da ta yi a ranta ya saka hawan jini me zafi ya kamata. Dalilin hakan ɓarin jikinta ya shanye.

Jinyar da Inna ta kwanta sai ya sa na watsar da batun karatun da na so farawa. Na tsira da ɗan abin da na koya daga Abdallah. Amma Hausa na iya raɗam babu abin da bana rubutawa na kuma karanta. Karin magana kuwa tamkar jakar Kano.

*****

Wata safiya Aufana ta tashi da zazzaɓi ga shi Abdallah bai shigo ba, domin ko ba komai yana ƙoƙarin ganin ya yi kange-kange ya samo mana abin da za mu buƙata. Inna ta lura bana cin abincin gidan sai wanda Abdallah ya kawo ta kuma matsa mini da son jin dalili. Sai dai na gagara sanar da ita domin bana son ɗaga mata hankali.

A wanan safiya na shiga ɗakin yaya na same shi yanata sauri,

“Yaya magana na zo mu yi da kai”

“Magana a kan me Lantana?”

“So nake na san wane aiki kake yi wa Alhaji Labaran.”

“Bai shafe ki ba kuma sanin hakan ba zai ƙareki da komai ba.”

“Ko da kuwa safarar miyagun ƙwayoyi da makamai ne?”

Na furta ina tsare shi da idanu. Kallona ya yi a tsorace yana girgiza kai,

“Kada ki ce mini da gaske kin ji tattaunawar Alhaji da Salisu wanda suka tabbatar min da cewar shi ne sillar haihuwarki.”

“Wa ya faɗa maka hakan?”

Na faɗa ina dubansa, “Su suka sanar da ni domin su ne suka sakaki a mota kafin Inna ta fito kuma sun ba ni tabbacin bakinki ya furta wasu kamalai cikin fitar hayyaci. A saboda haka suka yi amfani da ke matsayin garguwata. Ba ke ba ma, hatta Inna da Aufana suna cikin haɗari matuƙar na bijire wa aikinsu.”

Gurfana na yi a kan ƙafafuna ina kuka,

“Yaya Kamala don girman Allah ka haƙura da wannan haramtacen kasuwancin. Kasan rayuka nawa su Alhaji suka salwantar saboda son zuƙatansu. Mu yi ni sa da garin nan kawai.”

“Lantana ko ina muka je suna biye da mu, domin su ne ƙasar ki yi haƙuri na yi miki alƙawarin duk runtsi babu abin da zan bari ya taɓa lafiyarku.”

“Daga lokacin da ka samu matsala game da ciwon mantuwa na shiga tashin hankali yaya amma a yau na gwammaci ace mutuwa ka yi muka ga gawarka da wannan rayuwar da kake yi lallai kana cikin ɓata mabayyani ka ci amanar tarbiyar Inna da kuma Baba. Ka sa ni daga yau na ɗaura ɗamara da yaƙi da kai kuma in shaa Allahu sai na ga bayanku.”

Ficewa na yi daga ɗakin ina sharar ƙwalla. Maganin da na je in samu kuɗi wajensa kuwa fasawa na yi domin na lura ya yi nisa kuma ba ya jin kira. Da magarba Abdallah ya zo mun ji ma muna tattaumawa a nan ya shirya min hanyoyin da za mu bi mu shiryawa Yaya gadar zaren da jami’an tsaro za su kamashi. A tunaninmu idan yaya ya ji wuya zai bayyana su waye suka saka shi aiki.

Sai dai abin da ba mu sani ba cikin jami’an ma rabi duk mutanansu ne. A ranar da aka turowa yaya inda zai je karɓo kaya a ranar ni kuma na saci wayarsa na turawa jami’an tsaro wajen. Tare da goge message ɗin dana tura.

Lokacin da yaya ya je hannu ya sha matuƙar wahala, daga baya Alhaji Labaran ya yi yadda ya yi ya karɓoshi ta hanyar shaidar takardun asibitinsa na rashin lafiya. Inda aka juya lamarin aka alaƙanta shi da yarfan siyasa tun da an san yaya yaronsa ne. Nan da nan gari ya ɗauka kan ana yi masa baƙinciki ne. Bayan yaya ya dawo da kwana uku aka shigo har gida a gaban idanunmu aka kashe Inna.

Lamarin da ya yi matuƙar gigita tunaninmu. Muna ji muna kallo Hamana yaron Alhaji Labaran ya yi mata yankan rago, ranar Yaya baya nan. Ban sake sanin abin da ya faru ba sai farkawa na yi na mata cike da ɗakin Inna. Ban iya cewa komai ba, daga ni sai Allah sai Aufana da ko maganar kirki ba ta iya ba tun da lokacin tana da shekaru biyar a duniya.

Lokacin da Yaya ya iso ko ɗaga kai ban yi na kalle shi ba, haka aka gama makoki ba tare da kanzil ya shiga tsakanina da shi ba. Alhaji Labaran ya sa an kashe Inna ne saboda ya nunawa Yaya da gaske yake mu ɗin garkuwarsa ne shi ya sa aka kashe Inna da suka kira da ƙarasata kawai suka yi dama gawa ce. A tunanin Alhaji Labaran Yaya nada hannu a zuwan jami’an tsaro bai san duk shirina ba ne.

Muna cikin wannan taradaddin takardar samun damar ci gaba da karatun Abdallah ta fito, inda zai tafi ƙasar egypt domin ƙarin karatu. Sosai hankalinmu ya tashi, sai dai muna duban hakan kamar wata ƙofa ce gare mu ta kawo karshen Alhaji Labaran.

Kuɗin da suka rage wa Abdallah gabaɗaya ya damƙa mini da sunan kula da Aufana ta hanyar faɗaɗa harkar abincina. Tafiyar Abdallah da sati biyu na soma wani tunani a raina. Sosai na sauko na nunawa Yaya komai ya wuce, nan da nan muka soma shiri da shi. Sosai ya saki jiki da ni baya ɓoye mini dukan damuwarsa.

A wannan lokacin na fahimci matsi da tilastawa da yake fuskanta daga Alhaji Labaran. Abu ɗaya na soma yi shi ne na yi yunƙurin ankarar da shi daina karɓar magani daga hannun Dr Badamasi sai dai ya je asibitin da aka dubashi tun farko ya karɓo. Ya yi na’am da wannan shawarar kuma cikin ƙanƙanin lokaci ciwonsa ya yi sauƙi sossai. Babu zafin ran da yake yi a baya. Da wannan damar na samu abubuwa da yawa game da su Alhaji Labaran ta hanyar wayar yaya Kamala ba tare da ya ankare ba na kuma ɓoye su ɓoyo mai kyau.

Sai ya kasance yaya ba shi da burin da ya wuce kyautata mana, duk lokacin da ya kawo kayan abinci ina karɓa amma sai na bayar da su sadaka. Da kuɗina na saka Aufana makaranta kuma alhamdullilahi tana fahimta babu laifi.

*****

Kamar ɗaukewar ruwa haka Salisu da Alhaji Labaran suka ɗauke ƙafafu daga gidanmu tun bayan rasuwar Inna. Yaya kuwa bai fasa yi musu aiki ba. Kasancewar lokacin siyasa ya matso sosai ya samu sassauci daga aikin safarar da yake masa.

Wata ɗaya biyu uku shiru babu Abdallah babu labarinsa, ko wayarsa ma gabaɗaya mun daina samu. Hankalina ya tashi sosai. Ga mugayen mafarkai da nake yawan yi a kansa. Ban gushe ba ina kai wa Ubangiji kukana.

Cikin ikon Allah bayan shekara biyu na samu wayarsa, ranar har sadaka na yi saboda murna da farinciki. Sosai ya kwantar mini da hankali tare da nuna mini wayarsa ce ta ɓace a hanyar zuwa kuma sai da ya yi swap na layinsa ba shi da lambobinmu ba shi da wanda zai samu ya ba shi a ranar ma ni ce ina gwada kira kamar yadda nakan gwada lokaci zuwa lokaci na yi sa a ta shiga.

Aufana ita ce wadda ya soma tambaya daga nan ya ɗora da batun karatuna. Ban ɓoye masa ba na bayyana masa bana karatu. Faɗa ya yi min sosai daga bisani muka yi sallama.

*****

Kwanci ta shi babu wuya wajen ubangiji, Yaya Abdallah dai bai dawo Nijeriya ba sai da Aufana ta cika shekaru goma sha biyu a duniya. Domin shekaru biyar ya kwashe yana karatu inda ya fito da kyakkyawan sakammako.

Take kuma gwamnatin ƙasar ta buƙaci ya zauna ya yi aiki da su koda na shekara biyu ne. Bai musa ba duk da zuciyarsa na cike ƙudurin fansa amma ya san hakan wani ci gaba ne kuma zai ƙara gogewa a harkar aikinsa sosai. Ya soma gudanar da aiki cikin nasara.

Haƙuri shi ne abin da ya ba ni lokacin da na yi masa ƙorafin hakan. Cikin ikon Allah ya jagoranci shari’a da dama wanda hakan ya sa aka yi masa ƙarin matsayi. Bayan dogon lokaci kuma ya soma shirin dawowa ƙasarsa cike da ƙarfin guiwar san tallafawa na ƙasa da shi.

Zuwa lokacin ya yi saboda Aufana sosai ita ma haka. Ba ta da magana sai Baba Brr komai na ɗawainiyarta shi ne, account guda ya buɗe da sunanta. Tabbas Abdallah mutum ne domin sai da ya tabbatar Aufana ba ta san rashin mahaifi ba. Aufana ta taso yarinya mai tsanin wayo, fahimta, kaifin hankali da saurin riƙe abu. Ta sha tambayata mai ya sa take amfani da AUFANA HALIMA LABARAN amma amsa ɗaya nake bata,

“Tasirina ya fi tasirin kasantuwar mahaifinki a bigiren!”

Takan ce min,

“Amma me ya sa ba zan yi amfani da sunan kawu ko Baba barista ba kin ce shi ne mahaifina ba.”

A wannan gaɓar ne take ƙureni sai in koreta ko kuma in sakata yin wani aikin da zai ɗauke hankalinta. Sai dai nasan gudun ɓacin raina ne yake sa ta haƙura amma akwai muradin sanin ainihin sunan mahaifinta a ranta.

Aufana yarinya ce me shiga rai da son a kyautata mata. Tana san ta kusanci inda Yaya Kamala yake amma ba ya sakar mata fuska, hasalima gaisuwa ce kawai take haɗa su. Sai dai a ƙasan ransa yana matuƙar ƙaunarta tsoron Alhaji Labaran ya fahimci haka ya hana shi yin kataɓus. Ɗauke ƙafa da Alhaji Labaran ya yi ya yi masa daɗi, domin bai san rayuwar da muke ciki ba. Tsakaninsa da yaya kawai waya ce.

*****

Lokacin da Abdallah ya kammala shekara biyunsa ya dawo ba zan iya cewa ga yanayin da nake ba. Idan na ce ban yi farinciki ba ƙarya nake. Aufana kanta sai da ta shaida hakan. Sosai ya ware kuɗi aka yi abinci aka yi sadaka yadda ya kamata.

Dawowar Abdallah ba ƙaramin daɗi ta yi mana ba. Bayan ya dawo da sati biyu ne ya soma cuku-cukun neman yin karatunsa na shekara ɗaya a law school. Inda zai ƙara gogewa kan abin da ya shafi ƙasarsa, dokokinta da abin da tsarin kundin dokokinta ya gindaya.

Wannan ƙa’ida ce ta ƙasa, matuƙar a wata ƙasar ka yi karatu to sai ka yi wannan shekara ɗayar a ƙasarka domin tsarin kundin dokokin kowacce ƙasa daban da na wata ƙasar. Bai sha wahala ba kasancewar yana da ido a gwamnati nan da nan ya soma karatunsa cikin nasara tare da dafawar ubangiji ya sami sakammako me kyau.

Ya cigaba da jagorantar shari’a manya ɗa ƙanana. Kuma cike da tausayi da tallafawa wanda aka zallunta. Nan da nan sai ga tauraruwarsa na haskawa. Allah da ikonsa sai ga Abdallah da matsayin (SAN) saboda ƙoƙari da jajircewarsa. Matsayin da ya ɗaga darajarsa fiye da tunaninmu domin sai da ya zamana yana da alfarma a inda bamu taɓa zato ba.

Bayan gama karatunsa da watanni  ya samu aiki a gwamnatin tarayya, sai da ya raba ƙafa ne yana da office nasa na kansa na lauya mai zaman kansa. A wannan lokacin muka soma yunƙurin dakatar da Alhaji Labaran da miyagun ayyukansa da jiki da zuciyarmu. Cikin hikima taka tsantsan da kuma tsagwaron jajjircewa.

<< Fitsarin Fako 3Fitsarin Fako 5 >>

5 thoughts on “Fitsarin Fako 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×