Rashin Sani Ya Fi Dare Duhu
Sosai Abdallah ya mayar da kai wajen aikinsa. Nan da nan sunansa ya zagaye alƙarya sakammakon duk shari'ar da ya sa gaba sai ya cimma nasara. Kuma ba ya tsayawa kan rashin gaskiya. A wanan tsakanin ne maganar aure ta kankama tsakanina da shi. Aufana ta fi kowa farinciki da walwala.
Yaya Kamala kuwa ƙiri-ƙiri ya nuna ba ya murna da hakan. Katon gida ya gina mana mai kyau da tsari. Bayan an ɗaura aurena da shi aka yi gajeriyar walima mai. . .