A gajiye liƙis ta koma gida, ba ta samu mutum ko ɗaya ba a gidan, kuma dama ta tsammaci hakan. Rigarta ta ajiye tare da zama jagwam. Abin linzamin talabin (tv remote) ta ɗauka tare da rage muryar da ta cika fallon. Murya ta ware tana kiran Baba Laure,
"Baba"
"To uwargijiyata ya aka yi ne? An dawo za a ishe ni da kira ko?"
"Dan ma kin samu zan ci abin cin na ki ba ni abinci yunwa ƙishirwa ciwon kai ni komai ma ji nake"
Dariya ta yi tare da tafa hannu,
"Yau kuwa za ki ci. . .