Skip to content
Part 8 of 13 in the Series Fitsarin Fako by Sanah Matazu

A gajiye liƙis ta koma gida, ba ta samu mutum ko ɗaya ba a gidan, kuma dama ta tsammaci hakan. Rigarta ta ajiye tare da zama jagwam. Abin linzamin talabin (tv remote) ta ɗauka tare da rage muryar da ta cika fallon. Murya ta ware tana kiran Baba Laure,

“Baba”

“To uwargijiyata ya aka yi ne? An dawo za a ishe ni da kira ko?”

“Dan ma kin samu zan ci abin cin na ki ba ni abinci yunwa ƙishirwa ciwon kai ni komai ma ji nake”

Dariya ta yi tare da tafa hannu,

“Yau kuwa za ki ci hadda tukwici domin mutuminki na yi.”

Ware idanu ta yi tana kaɗa harshe. A gabanta ta ajiye mata kwanon tuwo da miyar ga kuma kunun tsamiya. Babu wanda ya faɗo mata sama da mahaifiyarta, tana tsaka da ci Baba Barista ya dawo dan haka tare suka cinye tas. Bayan sun gama take bayyana masa abin da ya faru. Sosai ya ji daɗin abin da ta yi tare da ƙarfafa mata gwiwa. Ba su tashi wajen ba sai da ya yi mata alƙawarin ba ta kuɗaɗɗe domin siyama wannan mabuƙatan kayan amfani.

*****

Washegari da wuri ta tashi kai tsaye station ɗin da matar ta yi mata kwatance ta nufa. Cikinsa kuwa ta yi katarin samun wannan jami’in da ta ba wa lambar mota. Bayan sun gaisa ne ta nemi su keɓance, ƙureshi ta yi da ido tuni ya shiga nutsuwarsa sakamakon kwarjinin da ta yi masa,

“Ashe haka abu ya faru kuma?”

Kame-kame ya soma yi,

“Ba haka ba ne Hajiya….”

“Babu matsala, ba sai ka rantse ba, amma ina son saninka na daƙile muryar da aka zallunta da amsa kuwar amon ‘yanci.”

Haɗe fuska ya yi,

“Turke ni kika zo yi ko me?”

“Ba turkeka na zo yi ba, amma ka sa ni rayukan al’umarka amana ne gareka. Ka yi rantsuwa kan kare dukkan haƙƙin al’umarka, amma saboda son zuciya da son mallakar abin da ba zai amfane ka da komai ba kana neman halakar da kanka.”

Jikinsa ne ya yi sanyi,

“Ba haka ba ne (barrister) wallahi mutumin yana da haɗari, ya yi min baraza ne a kan iyalina.”

“Waye shi?”

“Sunansa Muddasir kuma ɗa ne ga Alhaji Labaran Tanimu.”

“Kum….”

Hannu ta ɗaga masa,

“Ya isa, hakan ma na gode ni zan wuce amma ka ji tsoron Allah a duk in da ka kasance!”

Tana fita ya ɗauki wayar hannunsa, kira ya yi bayan wani ɗan lokaci aka ɗaga,

“Akwai wata ƙaramar kyanwa da take yunƙurin farautar ɓerayanku ka yi gaggawar sanar da oga!”

“Wace ce ita mene ne bayani a kanta!”

“Sunanta Aufana Halima….”

“Sajan!”

A ka faɗa da murya me amo,

“Zan maka gargaɗi na farko kuma na ƙarshe, wannan maganar ta zama sirri kada ka sake yallaɓai ya san da wanzuwarta!”

“Amma yallaɓai Kam…”

“Umarni na baka!”

Datse kiran ya yi yana mamakin abin da ya sa Gundul dakatar da shi. Kodai ya san yarinya ne? Amma kuma ai shi Alhaji ya ɗora kan duk matsalar da ta taso a sanar da shi shi kuma zai magance ta kafin ta isa wajensa idan kuma ta yi ƙamari ne zai sanar da Alhajin. Girgiza kai ya yi kawai tare da sakin murmushi.

*****

Kai tsaye Aufana gida ta nufa zuciyarta cike da takaicin abin da yake addabar ƙasarta. Idan kintacenta ya zama gaskiya Alhaji Labaran babban mai laifi ne. Lokacin da ta isa gida kawunta kaɗai ta samu. Damuwar da take kan fuskarta ta gaza ɓoyuwa tun kan ta kai ga zama ta soma ƙwala kiran,

“Baba! Babana ka na ina?”

Shiru babu shi, Kamala da ke zaune ya gimtse dariyarsa,

“Ni da ba ki nema ba ni ne a gidan ‘yar rainin wayau.”

Turo baki ta yi a shagwaɓe,

“Kawu ba haka ba ne wallahi kai na ne ya ɗauki caji.”

“Me ya faru ne?”

Sanin ba ya tare da muradinta ya sa ta yi niyyar ɓoye masa sai dai ba ta san me ya ja hankalinta ba kai tsaye ta tambaye shi.

“Kawu waye Alhaji Labaran Tanimu ko ka san wani abu game da shi?”

Ras! Gabansa ya faɗi, wani gumi ne ya soma tsattsafo masa. Sai dai sanin wannan wata dama ce da zai nisanta Aufana da sharinsu ya sanya shi muskutawa tare da furta,

“Na san shi na taɓa yi masa wani aiki a kan kuskure, me ya haɗa ki da shi, kuma me kike buƙata game da shi?”

Wani tsalle ta yi tsabar murna, kusa da shi ta dawo ta zauna tare da riƙe hannunsa. Tiryan-tiryan ta bayyana masa abin da yake faruwa. Bai yi mamaki ba saboda sanin da ya yi masa dan haka ya dube ta da kulawa,

“Me kike so?”

“Bayani game da abin da ka sani a kansa.”

“To buɗe kunnuwanki ki ji ni da kyau, kuma ina fatan jin waye shi zai ba ki damar fita daga sha’aninsa domin tsira da martabarki. Alhaji Labaran Tanimu Me gaskiya wasu da yawa na kiransa da ɗan majalisa me gaskiya. Mutumin da idanu da yawa suke ba shi ƙima da mutuntakar da ba su san matsayinta ba. Ɗan siyasa ne da ya yi ƙaurin suna ta fannoni daban-daban. Sunansa na yanka ya ɓoyu  sai me gaskiya sakammakon yadda ya yi ado da mutuntakar gaibu, ya sanya rigar da ta ɓoye duk wani munin ɗabi’arsa.

Mutum ne wanda yake gudanar da rayuwarsa babu tausayi babu imani. Amma kuma yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen fito da kyawawwan ɗabi’u a idanun talakawansa. Waɗanda kuma riga suka fahimci waye shi sun sa ni.

Da farko shi ɗin kansila ne amma tsabar iya munafurci da kutungwilar siyasa ya dinga kutsawa cikin manyan ‘yan siyasa, yanzu haka yana da matsayin ɗan majalisan jaha ne. A gefe ɗaya  kuma siyasar tasa ma ungulu da kan zabo yake yi mata. Domin yana ɗaya daga cikin masu haddasa husuma tsakanin jam’iyun siyasa guda biyu.

 Ɗan majalisa me gaskiya shi ne sunan da ya yi fice da shi, duk harka ta haramci matuƙar za ta kawo masa kuɗi to yana maraba da ita. Shi ne fasa ƙwaurin miyagun ƙwayoyi, shi ne fataucin ƙanannun yara zuwa ƙetare ta kai ta kawo yanzu yana shirin fara harkar garkuwa da mutane.

 Ya iya allonsa shi ya sa yake cikin karansa ba tare da babbaka ba. Sannan kuma gwani ne wajen yin ɗingishin kwaɗo tare da aron sawun keke. Yana da manyan wurare a wajen gari da ya gina ake yi masa haya da su, amma ba tare da barin ko da sawu ɗaya da zai bada tabbacin nasa ba ne. Domin wurare ne da ake gudanar da haramtattun ayyuka irin su; gala, harƙalar koken, da sauransu.

 Duk ƙwaƙwar masu bincike sun buga sun ƙyale shi. Mutum ɗaya ne yake neman ganin ya kai shi ƙasa ta kowace hanya. Sosai suke takun saƙa tsakaninsu domin dai masu iya magana kan ce kifi na ganinka mai jar koma.

 Ba kowa bane wannan mutumin face wani haziƙin lauya. Kuma amini ne ga amintacen likitan gidansa. Sai dai kasancewar shi ma likitan nasa babu Allah a zuciyarsa ko da wasa ya ƙi ba wa wannan barrister damar da yake nema na kafawa Alhajin tarko.

Akwai tuhuma da dama da yake da ita akansa, musamman fanin yawan ɓacewar ‘yan matan da suke aikin wanke-wanke a gidansa. Ba sa gaza watanni biyar zuwa takwas za a ce an wayi gari babu yarinya. Ko kuma an haike mata. Da zarar ya shiga batun kamar gaske sai kuma a watsar da lamarin baki ɗaya. Ba za ki sake jin maganar ta ɗaga ba.

Wannan (barrister) ya kutsa sosai cikin rayuwarsa, yana son bankaɗo duk wasu munannan ɗabi’u na Alhajin amma hakan ya ci tura. Takun saƙa suke sosai saboda ya kasance shi ɗin ɗa ne abokin karawarsa ta ƙungiyar hamayya wanda aka tabbatar da su suka kashe shi tare da dukkan iyalansa sai wannan (barrister) kaɗai ne ya kuɓuta.

Shi ya sa sai yake alaƙanta duk wata tuhuma ta (barrister) da yarfe ne irin na siyasa. Hakan ya sa duk wani ƙwarin gwiwa nasa yake sagewa saboda da wannan damar yake yi masa ƙafar angulu.

Dan haka Aufana ina gargaɗinki da ki shiga hankalinki ki ƙoƙari wajen fita sha’anin wannan mutumin domin ba shi da imani.

Zai iya yin komai saboda Muddasir shi kaɗai ne ɗan da ya mallaka da tsohuwar matarsa wadda ta kasance tana nan a cikin gidansa ba ta da maraba da ‘yan aiki. An samu tabbacin cewar shi ya tsaface ta saboda wani sirri nasa da ta gani, kawai a zaune take ba ta magana, kuma ba ta motsa kowace gaɓa ta jikinta.”

Da idanu ta ƙure shi daga lokacin da ya soma magana zuwa lokacin da ya gama ta lura da abubuwa da dama tare da shi, akwai wani miki da ta lura yana motsawa a ƙirjinsa ta sanadin ƙwallar da yake ƙoƙarin ɓoyewa,

“Kawu na tabbarar tun da har ka iya ba ni wannan gamsassun bayani, za ka iya yi min hanyar shiga gidan Alhaji Labaran matsayin mai aiki, lallai ina buƙatar hakan. Domin ina son ganawa da tsohuwar matarsa. Sannan ina so ka haɗa ni da wannan (barrister) ɗin matuƙar yana raye.”

Kaɗuwa da mamaki ne suka kamashi lokaci ɗaya, daga bayansu kuma aka saki tafi, raf! Raf!! Raff!!! Ba kowa ne ya yi hakan ba face Baba Barista,

“Da kyau jarumar ɗiya lallai yau kin tabbata jinin Halimatu!”

“Aufana kina da hankali kuwa” Kamala ya yi furucin cikin rawar murya. Kallonsa ta yi tare da sakin murmushi me ma’anoni da yawa.

“Ina da hankali kawu, yaƙin duka namune matuƙar kana kishin al’ummarka.”

Daga haka ta miƙe akan duga-duganta ta wuce ɗakinta.Tana bada baya Baba Barista ya buga ƙafa tare da sheƙewa da dariyar data ƙular da shi,

“Rana dubu ta ɓarawo…. Ai dama na faɗa maka akwai ranar ƙin dillaci ga shi dai kasa kanka da kanka a tarko.

Tunda ta koma ɗaki babu abin da take sama da tunanin mene ne tsakanin kawunta da wannan azzalumin mutumin da har yau bata taɓa ganinsa ba sai a fasta. Lallai akwai lauje cikin naɗi. Tasan tabbas Baba Barista yasan wani abu dan haka zata tsaurara bincike wajan gano ainihin gaskiya.

*****

Kamar kodayaushe cikin shigar kayan aiki ta shigo gida, Baba Barista ta samu yana duba wasu takardu ta zauna suna hira jefi-jefi. Tun lokacin da ta sanar da kawunta ƙudurinta bata sake sakashi cikin idanunta ba kimanin kwana uku kenan. Haka ma wayoyinsa basa shiga, cikin dabara ta yi hikimar sako batun,

“Baba ni fa ban sake ganin kawu ba!”

“Aufana kin sa kawunki a tsaka mai wuya ta ya ya za ki ganshi?”

“Amma Baba nasan kai ma ka san wani abu game da mutumin nan ni jikina ma na bani kai ne baerister ɗin da kawu yake magana akai…”

Kallon da yake mata ne ya sa ta gimtse sauran maganar. Idonta ne ya sauka kan littafin da kawu ya ƙwace a hannunta dan haka ta yi dabarar ɗora takardun hannunta a kansa. Hikimarta idan ta tashi miƙewa ta haɗa da shi ba tare da Baba Brr ya fahimta ba.

Haɗe fuska ya yi,

“Amma kin san bana yi miki wasa ko Aufana?”

“Hakane Baba amma ga wannan ka duba”

Ta faɗa tana gyara zamanta tare da tura masa file ɗin da shi ne maƙasudin zamanta a wajen, janye glass ɗin idanunsa ya yi tare da dubanta da sauri,

“Ɗiyata me nake gani haka?”

Murmushi ta yi tare da gyaɗa kanta,

“Kina nufin ke zaki tsaya domin kare haƙƙin ɗiyar mabaraciyar nan?”

“Haka na yanke Babana.”

“Batun Sadiya fa?”

“Ita ma lokaci na bata, na yi bincike kan wannan mutumin da dama babu bakin da ya faɗamin alkhairinsa sai wanda suka san shi da ɓoyayyar fuskarsa. Yana da hatsari Baba dan haka zan haɗa bincike biyu ne a lokaci ɗaya kowane zai yi min amfani so nake sai na kaishi ƙasa da izinin Allah na tsani zallunci.”

“Kina ganin za ki iya?”

“Ƙwarai kuwa Baba tun ranar da na ga rasuwarta da abin nake kwana na ke tashi. Sai dai lokacin dana samu bayanin abin da ya faru daga mahaifiyarta na ji zuciyata ta amince da karsashin tsaya mata wajen ƙwatar ‘yancinta.

Ba ita kaɗai ba duk wani mabaraci irinta a shirye nake wajen ƙwatar masa ‘yancinsa. Sannan ina son ka taimakamin mu buɗe wani fundation wanda zamu taimaka musu koda da abin da ba shi da yawa ne.

 Rayuwa ta sauya ba dole sai kana da kuɗi zaka tallafawa naƙasa da kai ba, akwai hanyoyin sadarwar da yawa wanda zamu yi kokke duk duniya ta dubemu. Ga mamakinta wani irin gumi ta ga yana keto masa ta saman goshi, ya buɗe baki zai sake magana kawu ya shigo a fusace. File ɗin ya warta tare da yagashi gida biyu.

“Wallahi matuƙar ina raye ba zan yi wasa da rayuwar Aufana ba.”

Sororo ta yi tana dubansa, ya nuna Baba Brr da yatsa,

“Abdallah ya isa haka, ba zan yadda na kuma sakaci kwatankwacin na baya ba.”

Yanayin da tagani a tare da su gaba ɗaya ya bata mamaki. Amma kuma yagamata file ya fi yi mata ciwo. Batan san akan abin da suke magana ba amma adalci be bada damar a yagamata file ba.

“Ƙarya ka ke Kamala a wannan gaɓar dole ka yi haƙuri. Tabbas zan cika burin Halima ta hanyar amfani da damata da kuma ƙarfin ikona akn Aufana. Koda bata raye ba zan bari burinta ya mutu ba!”

“To mu zuba ni da kai shege ka fasa!”

“To zamu gani!”

Zuwa lokaci ta shaƙa iyakar shaƙa ta kuma fahimci akwai abin da suke ɓoyewa da ya bayyana murarran a idanu da ƙwaƙwalwarta. Batasan ta yi magana da tsawa ba,

“ya isa haka ya isa, me ku ke duƙunƙunewa ne cikin rayuwata. Na tabbar kuna da abin da ku ka sani game da mutumin nan?”

Gaba ɗaya suka juyo a firgice suna kalonta, bata damu da kaɗuwarsu ba ta cigaba,

“wallahi mudin ina raye sai na tabbatar da gaskiya kan me ita kuma zan tuhumi duk wanda yake da hannu kan kisan yarinyar nan koda kuwa ɗaya daga cikinku ne”

 Miƙewa ta yi bayan ta ɗauki takardunta, Tana jin wani iri a ranta. Sai dai bata manta da batun ɗaukar littafin nan ba kuma ta yi nasarar hakan. Dan haka tana shiga ɗaki ta yi masa kyakkyawar ajiya.

*****

Cikin kwanaki biyu rashin jituwa ya yi tsamari tsakanin Baba da kuma kawu, ta ɓangarenta kuma Baba be fasa bata ƙwarin gwiwar bincikenta ba. Da taimakonsa aka samar mata da sabon file tare da gargaɗi me girma kan kula da shi.

A gefe guda kuma ta yi nasara kan mahaifiyar Sadiya yarinyar da aka tsinci gawarta ɗaya daga cikin masu aiki gidan Alhaji Labaran. Har zuwa lokacin mahaifiyar tata tana aiki a gidan. Da nasiha da wayau ta yi duk yadda za ta yi ta shiga jikinta har ta kaita gidan matsayin ɗiyar ƙanwarta.

Komai ya zo mata da sauƙi domin dai Baba Ladi mahaifiyar Sadiya ita ce me kula da matar Alhaji Labaran. Takan bi ta ne a ranakun Asabar da Lahadi da sunan ta ya ta aiki bayan ta sauya kamaninta da kayan aiki irin na su. Ɓat kamarta ta ɓa ce domin cika bakinta take yi da baki ta rambaɗa kwali. Ga wani makeken tabo da take yi a kunci. Ta kuma sauya sunanta zuwa Sabira.

Dabara ta farko da ta soma yi shi ne cire na’urar kai rahoto ta ɓangaren Hajiyar wato (CC Camera). Cikin iya taku take gudanar da komai. Ta je musu a mace me tsananin sakarci ga wasa da dariya, bata taɓa yadda ta haɗɗu da Alhajin ba duk da duk safiya ya kan shigo amma Muddasir sukan haɗuwa sossai duk da babu abin da yake haɗasu face kyara da zagi.

Cikin ƙanankin lokaci ta shiga ran kowa. Da wannan damar ta soma zama da matar Alhaji Labaran. Kalmar tsafi da kawunta ya furta mata ita ce ram a tunaninta dan haka da shirinta ta shigo duk wani ruwa da abin ci da Baba Ladi take bata sai da ta tabbatar suna zuba ruwan addu’a. Yayinda idan sahu ya ɗauke ta ke zuwa ta na yi mata wasu addu’o’i a kunnuwanta ta kuma shafa mata wani ruwan a ƙafaffu da hannunwanta.

Satinsu uku da somawa nasara ta samu domin dai babu gaɓar da bata motsi a jikinta, a ranar Aufana ta bayyana mata ita wace ce da kuma ƙudirinta na zuwa gidan ta kuma roƙeta da kadda ta yi wani motsi zai tona musu asiri. Da ka kawai ta bawa Aufanan amsa a zuciyarta tana tunanin inda tasan me irin fuskar.

Bata shafe wata biyu ba sai da ta tabbatar da samun lafiyarta garau, ta kuma samu duk abin da take buƙata daga gareta sallama suka yi wa juna bayan ta tunasar da ita muhimmancin riƙe addu’a. Ranar da ta samu Baba Barista da hujojin da ta samu har kuka ya yi saboda da murna. A ranar ne ya sanar da ita zai bata wani littafi ta karanta domin zata sami ƙarin hujoji akan Alhaji Labaran.

*****

Kwanaki uku kenan yana neman littafin amma ya gagara samunsa, tunaninsa ya tafi kan ko Kamala ne ya ɗaukeshi. Ga shi kwata-kwata yanzu Kamalan ba ya zama gidan babu me sanin shigowarsa ko kuma fitarsa. Dan haka ya ƙudiri sai ya jirashi komai dare. Yana nan zaune yana jiran gawon shanu har ɗaya da rabi ta yi, yana shirin miƙewa sai ga shi ya shigo, ɗan jim ya yi kamar ba zai ƙaraso ba sai kuma ya gimtse ya nufi shiga ciki.

“Kamala ina littafin da ka ɗaukarmin?”

Kalmar ta dake shi, amma sai ya gimtse,

“Ban san me ka ke magana ba kuma ban ɗauka ba.”

Sa’insar da suka soma yi ce ta fito da Aufana wadda dama idonta biyu tana kan darduma. Muryarta cike da gajiya da abin da yake faruwa ta furta,

“Dare ne fa kawu.”

Juyowa ya yi ya zuba mata ido, ta rame sossai kamar ba ita ba kuma yasan hakan nada nasaba da ƙulafucin case ɗin da ta saka a gabanta. Wasu lokutan yakan ji kamar tasan Alhaji Labaran nada hannu a ruguza rayuwarta shi ya sa take wannan haƙilon. Kai ya girgiza kawai,

“Ban ɗauki littafinka ba Abdallah ka sake bincike!”

Ya faɗa yana shirin juyawa ya kaiwa wuyansa damƙa, kuka ta saka tare da fitowa sarari sossai hakama Baba Laure da hayaniyarsu ta tasota,

“Wai Baba littafin na gwal ne da ku ke neman kashe kanku?”

“Littafin rayuwar mahaifiyarki ne!”

Kalaman suka daketa tare da kwance duk wani notika na gaɓɓanta, lallai zata so sanin wannan wane littafi ne, ras gabanta ya faɗi,

“Kawu ko shi ne wanda ka kwace a hannuna kwanaki?”

Kai ya gyaɗa mata zuwa lokacin da ƙyar yake numfashi,

“Ya na wajena.”

Ta yi furucin da ƙarfi sai ya sakeshi ya faɗi ƙasa sharaf. Da gudu ta yi kansa tana tattaɓashi tana kuka. Ko motsi be yi ba da gudu ta kwaso ta ɗebo ruwa ta watsa masa,

“Sannu kawu dan Allah ku daina wannan tsamar tsakaninku wallahi bana jin daɗi” “Aufana Babanki ya fi ni gaskiya a zahiri amma kuma a baɗini ni ɗin katanga ne ga rayuwar dukkaninku. Ki je ki karanta labarin mahaifiyarki ki dawo gareni ni kuma zan ɗora miki dukkan abin da yake da giɓi cikin rayuwarta.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fitsarin Fako 7Fitsarin Fako 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×