"Yaya Heesham wallahi yunwa nakeji."
Suka ji muryar Nasreen ƙanwar Heesham ɗin tana faɗar haka.
Ɗago kai Heesham ya yi yana kallon ƙanwarsa, ta rame tai baƙi sai haske data ƙarayi da kyau domin suna kama da yayan nata, amma ko ƙafar ƙafarsa bata kamaba a kyau.
Buɗe baki ta yi da ce wa, "Nasreen ki yi haƙuri ban samo komai ba yau,amma ki yi haƙuri zan nemo miki wani abun ki ci."
"To yaya Ubangiji Allah ya sa ka dace idan ka fita?"
Nasreen ta faɗa idonta na kawo kwallah.
"Ameen ameen. . .