Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Gidan Gado by Zainab Muhammad

“Yaya Heesham wallahi yunwa nakeji.”

Suka ji muryar Nasreen ƙanwar Heesham ɗin tana faɗar haka.

Ɗago kai Heesham ya yi yana kallon ƙanwarsa, ta rame tai baƙi sai haske data ƙarayi da kyau domin suna kama da yayan nata, amma ko ƙafar ƙafarsa bata kamaba a kyau.

Buɗe baki ta yi da ce wa, “Nasreen ki yi haƙuri ban samo komai ba yau,amma ki yi haƙuri zan nemo miki wani abun ki ci.”

“To yaya Ubangiji Allah ya sa ka dace idan ka fita?”

Nasreen ta faɗa idonta na kawo kwallah.

“Ameen ameen ƙanwata, amma kuma mene na kukan?”

Heesham ya faɗa yana miƙewa tsaye daga zaunan da yake.

Nasreen cikin muryar kuka, ta ce, “Yayana ina matuƙar tausaya maka, yaya bai kamata ace kaine mai wahala damuba, yaya wahalarmu tai maka yawa.”

Sai kuma ta fashe da kuka, take zuciyar Ammi da Heesham ta karye, suma suna son yin kukan.

Amma dake ɗaya baya son ya ga hawayen ɗayan, shi yasa Heesham yai musu sallama nare da neman addu’ar dacewa, kafin ya fice.

Koda ya fita ba abinda ya samu sai wahala ma daya ɗebo, a hanyar dawowarsa gida ne yaga wani yaro ya fito da abinci a kwano zai bada sadaka ga almajiri, da sauri Heesham ya ƙarasa ya ƙarɓa ya juye tare da yiwa yaron godiya ya nufi gida.

Zuwansa ƙofar gidansu keda wuya sai ya same shi garƙe da mukulli, tsayawa ya yi turus yana tunanin ina kuma Ammi da Nasreen suka je?

Muryar wani yaron maƙotansu mai suna Khaleed ya ji yana cewa, “Yaya Heesham an tafi da Amminku police station.”

Kirjinsa ya ɓada wani irin rasss zuciyarsa tana bada wani irin bugu mai ƙarfi.

Juyawa ya yi ya kalli Khaleed kafin, ya ce, “Khaleed police s tation kuma? Me tayi da za a kaita wajan ƴan sanda?”

“Nima ban sani ba kawai dai anzo an tafi da ita”

Khaleed ya faɗa.

Heesham ya ce, “Wannan police station ɗin aka kaita?”

Khaleed ya ce, “Na ji ance wai na Mandawari ne.”

“Innalillahi wa inna ilaihirraju’un! Allahumma ajirni fil musibati wa aklifni kairan minha! Na shiga uku ni Heesham”

Heesham ya faɗa yana mai juyawa dan tafiya wajan ƴan sandan, suna da ɗan nisa tsakanin su domin su su Heesham a wajan bakin asibiti suke.

Ya yi tafiya mai nisa kan ya isa wajan ƴan sandan.

Yana zuwa ya hango Nasreen takuɓe jikin wani banci, ƙarasawa ya yi yana mata magana ɗagowa tayi idanunta duk ya jike da hawaye abinka da farar mace fuskarta duk tayi ja.

Yana ƙarasawa ta faɗa jikinsa tare da fashewa da wani kukan,”Yaya wai Ammi aka kowa ƙara akan bashi.”

Rarrashinta Heesham ya shiga yi,bayan tayi shiru ne yace mata bari yaje ta tambaya ina su ammin suke,wajan ƙan sandan dake ƙarɓar ƙorafai ya nufa.

Yana zuwa ya tambayi wani cooper,nuna masa office ɗin d.p.o ya yi kai tsaye heesham ya nufi cikin office ɗin.

Saboda yana cikin tashin hankali ko sallama ma bai tsaya yiba ya shiga, duk suka ɗago suka kalleshi Ammi tana daga can gefe a tsugune.

Ɗauke kansa ya yi daga kallonta saboda ba zai iya jure ganin halin da take ciki ba.

“Yallaɓai me mahaifiyata tai maku kuka kamata?”

Kallonsa D.P.O yai kafin ya nuna wata mata dake zaune akan kujera kafin ya ce,

“Wannan matar ce ta kawota ƙara akan ta hanata bashin da take binta yau shekara ɗaya kenan”

“A’a yallaɓai ba hanata akai ba halin bata ne babu.”

Ya faɗa yana mai juyawa dan ganin matar, domin shi bai san ma sanda akaci bashin ba dan ya hanasu cin bashin kowa matuƙar basu da nasu.

A razane yake sake kallon matar kafin ya ce.

“Anty Kubra ke ce kika kawo Ammi wajan ƴan sanda?”

(Anty kubra ƙanwar Ammi ce uwa ɗaya uba ɗaya, amma dake wani zumunci sai a hankali shine ta kawota wajan ƴan sanda, Allah yasa mu dace ameen).

Wata uwar harara Anty ta bugawa Heesham, kafin ta ce,

“Dallacan rufawa mutane baki wane yace taci? Ko gani take dan taci nawa taci bulus?”

Juyawa Heesham ya yi ya kalli D.P.O bai ko sake kallon Anty Kubra ba.

Ya ce, “Yallaɓai yanzu ya ake ciki?”

D.P.O ya ce,

“Abinda ake ciki shine abinda wadda ta kawo ƙara zatace.”

Sannan ya dubi Anty Kubra ya ce, “To hajiya ya kike ganin za’ayi?”

Yatsina fuska Anty Kubra ta yi kafin ta ce, “Ni dai yallaɓai kawai a karɓarmin haƙƙina domin wallahi bazan batta da Allah ba.”

D.P.O ya ce, “Faɗi suji da kunnan su nawane kuɗin naki duk da nasan sun sani.”

“3k ne kuɗina.”

Anty Kubra ta faɗa cikin gadara.

D.P.O ya juya kallonsa ga Heesham kafin ya ce, “to kaji abinda tace me ka ke gani kai?”

Ajiyar zuciya Heesham ya sauke kafin ya ce, “A bani lokaci insha Allahu zan kawo kuɗin.”

D.P.O ya ce, “Ok zamu baka sati 2 ka kawo idan ba haka ba kuwa sai an ƙara kama wannan mahaifiyar taka”

Runtse ido Heesham ya yi kafin ya ce”insha allahu zan kawo”

Nan d.p.o yai ɗan rubuce-rubucensa kafin ya bawa heesham biro yace yasa hannu.

Ƙarɓar biron heesham ya yi a sanyaye yai signature sannan aka sallamesu suka tafi gida.

A hanya Ammi sai kukan zuci take yi tana cewa ina ma mahaifinsu Heesham yananan da basu shiga wannan halin ba, duk da ƙaddara tana iya sauyawa dan adam amma da abin zaizo da sauƙi.

Kuma ko mene ne ya samesu sanadin gidan gado ne gidan jaraba gidan da bata marmarin sake tunkararsa koda a wane hali take. Har suka isa gida tana tunani.

Bayan sun buɗe gidan sun shiga ne Nasreen ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa musu suka zauna, sannanta ta ɗauko kwano ta buɗe ledar da yaya Heesham ya bata a police tation dama bata ciba dan lokacin bata cikin hayyacinta ta juye a kwanan,kafin

Ta ce, “Ammi yaya Heesham muci abinci”

Kallon tuhuma Ammi tai mata, kafin ta ce, “Mamana a ina kika samu abinci?”

Murmushi Nasreen tayi kafin ta ce, “Amma bafa ni na samo ba ya Heesham ne ya bani tun muna waja  ƴan sanda.”

Sakin fuska Ammi tayi kafin lokaci guda kuma fuskarta ta sauya zuwa ta damuwa, sai kuma idanunta suka fara kawo hawaye masu ɗumi tasa gefan zaninta tana gogewa.

Duk halinda ta shiga akan idon Heesham ne amma ba zai iya hanata ta zubda hawaye taji daɗi ba, domin rage raɗaɗi zatai na abinda yake damunta (domin Hausawa sunce kuka ma rahmane ga wanda yake cikin wani hali.

Yunƙurawa ya yi zai tashi daga kan tabarmar, Ammi tai saurin tsaida shi ta hanyar ce wa, “A’a Babana ina zuwa kuma bakaci abincin ba?”

Ɗan murmushi Heesham ya yi kafin ya ce, “Ammi baƙin cikina ɗaya ne ace yau kun wayi gari keda Nasreen baku da abinda zaku ci har zuwa wani safiyar, Ammi hankalina yana matuƙar tashi duk sanda na ganku a wannan yana yi. Amma farincikina shine koyayane naga kun samu kunci.”

“Duk da haka Babana ka samu ka ɗanci, dan nasan kaima ba wani abu ka samu ka saka a cikinka ba.”

Ammi ta faɗa tana mai kallon fuskarsa, idanunsa sunyi zuru-zuru irin na mai jin yun wa.

“Amma Ammi…”

Ammi ta dakatar da shi da ce wa, “Kar kace komai, dan allah kaci koyayane.”

Jin haka kuma gashi baya son yiwa Ammi musu, yasa hannu yai ci biyu sannan ya cire hannunsa yaje ya wanke.

Itama ammi tsame hannunta tayi tabarwa Nasreen ragowar.

“Assalamu akaikun”

Suka ji sallamar wata ƴar maƙotansu mai suna Hajara.

Tana Karasowa ta tsugguna ta gaida Ammi, kafin ta juya ga Heesham ta ce, “Ya Heesham ina huni?”

Kamar baya son amsawa ya ce, “Kin yini lafiya?”

Bai jira abinda zata ce ba ya shige ɗakinsa domin samun hutu.

Ita kuma Hajara suka fita da Nasreen zuwa makarantar islamiyya.

Domin duk da halin da suke ciki bai hana Heesham sakata a makarantar boko da islamiyya ba.

Dama shi tun mahaifin su yana da rai ya kammala degreen sa ci gabane dai bai samu ba rayuwa tai musu juyi.

*****

Nufaisat ce zaune akan tabarma a tsakar gidan tana cin abinci hannunta ɗauke da note book ɗinta na makaranta da alama karatu take, Ihsan (ƴar autar su Nufaisat ce) ce ta zauna kusa da ita tare da fusge littafin ta gudu wajan Mama dake zaune a ɗaki tana sallah.

Miƙewa Nufaisat tayi ta bita ganinta jikin Mama bai hanata daketa ba sannan ta kwace book ɗinta ta fice, kuka Ihsan ta saka tana burgima.

Mama data idar da sallah ta fito ta sami Nufaisat aikwa ta rufeta da faɗa ta inda ta shiga ba tanan take fita ba.

“Tsabar rashin mutuncin ki biyo yar har gabana ki dake ta, to wallahi idan baki wasa ba saina saɓa maki shashasha!”

Dagowa Nufaisat ta yi tana kallon Mama har ta gama maganar, miƙewa tayi cikin fushi ta a jiye abincin tai ɗaki sai kuma tasa kuka.

Haka taita kukanta Mama kuwa ko kallonta bata yi ba, sai da lokacin tafiya makarantar magriba ya yine ƙawarta ta biyo mata sannan ne mama ta shiga ɗakin. Kwance ta sami Nufaisat ɗin akan gado idanunta a rufe kamar mai bacci amma Maman ita ta san ba baccin take ba.

“To ki tashi ki fita ga Rahma can ta biyo miki makaranta.”

Cikin dashashshiyar murya ta ce, “Ba zani ba”

Mama ta dubeta kafin ta ce, “Me ki ka ce?”

“Ba zani ba kaina kemin ciwo.”

Nufaisat ta faɗa lokacin da hawaye suka gangaro daga fuskarta.

Mama ta kau da kai gefe, sannan ta ce, “To wane ya sa maki ciwon kan, kinga ki tashi ki fito tana jiranki.”

Tana faɗar haka ta fice daga ɗakin.

Mikewa Nufaisat ta yi riƙe da kanta saboda kukan da ta sha ta ɗauki hijab ɗinta ta fito, ko sai mun dawo ba ta ce da Mama ba ta bi bayan Rahma suka fice.

A hanya bata ce da Rahma komai ba har suka isa makarantar.

Suna zuwa suka gaida malamai sannan suka shiga aji.

Saida aka kusa tashi sannan wani yaro ya shiga ajin su Nasreen ya ce wai tazo inji Malam Jabeer.

Sai da tai kamar ba zata ba, sai kuma ta tashi ta fita. A can inda malamai suke zama idan ba aji zasu shiga ba ta same shi akan tabarma.

Sallama tai sannan ta zauna tare da gaishe shi, ɗagowa ya yi ya kalleta ya ga fuskar nan a ɗaure.

“Nufaisat me akai maki kika zo yau ba fara’a alhalin keda idan kika zo sai kowa yasan sa zuwanki?”

Malam Jabeer ya tambayeta.

Kanta a ƙasa ta ce, “Malam ba komai.”

Malam Jabeer ya sake cewa, “To amma yau me ya sa bako ɗuriyarki ba a ji?”

Ta kalle shi sannan ta ɗauke kai da cewa, “Kaina ne yake ciwo shiya sa.”

Malam Jabeer yace, “To shikenan Allah ya sauwaƙe, ta shi ki koma aji naji ana addu’a.”

Miƙƙewa ta yi ta koma aji akai musu sallama aka tashe su.

Gidan su maryam ne a farko dan haka ta riga nufaisat shiga gidan.

Da sallama Nufaisat ta shiga gidansu, Mama dake zaune kan tabarma ta amsa.

Ɗaki Nufaisat ta shige ta aje hijab da jakarta sannan ta fito falo tai shimfiɗa ta kwanta.

Washe Gari

Da sassafe Nufaisat ta tashi daga bacci dan ranar za su fara zana jarrabawarsu ta NECO (wato jarrabawar fita daga secondary) bayan ta gama shiryawa ne Mama ta bata ɗari tace ta sayi akwara taci kafin su dawo.

Haka suka tafi makarantar jarrabawar ba tayi wata wahala ba dan da nan suka gama suka dawo gida.

Wannan kenan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Gidan Gado 1

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×