Ƙauyen Tandau, 1997
Cikin talatainin daren mai gauraye da hadari baƙi ƙirin take ta ratsa gonaki da kwazazzabai. Zuciyarta a bushe babu alamar tsoro ko kaɗan, sai ma idan ta ci karo da marmara ta sa ƙafa ta dake ta da ƙarfi kamar ita ke ƙara mata nisan tafiyar. Ba ta dakata ba har sai da ta isa bakin wasu bishiyoyi biyu da suka zama kamar ƙofa ga maƙabartar.
Ta tsaya ƙyam! Tana ƙare wa cikin maƙabartar kallo, ta ɗaga kanta sama ta ga yadda baƙin hadarin ya lulluɓe hasken farin. . .
Allah yakara basira
Amin
Dakyau, fatan alheri. Allah ya sa an fara a sa’a.
#haimanraees
Thank you! So much, wnn labarin ya tuna mn da wani film dana kalla na chineese, yana kamanceceniya dashi.