Skip to content
Part 12 of 32 in the Series Hakabiyya by Fulani Bingel

“Wai ni kike cewa na taimake? Yanzun ke dan jakanci duk darasin da na dinga baki ba ki kiyaye ko guda ba? Ba ki tuna ranar da na baki ƙyalle ba? Na baki ne da niyya biyu shiyasa har na ambato miki malami ne ya bani ayi asirin da kuɗi zasu dawo. A zatona kalmar asiri da na ambata zai sa ki tsorata ki gujeni ko da na dawo miki duk abinda zan furta miki ba za ki ji ƙaina ba balle ma ki sake saurarata, da ace kin yi haka da yanzu ba na nan inda kike. Kina tuna ranar da na kai ki wannan gidan? Na kai ki ne da biyu, na farko na gabatar da aikina kan ki, na biyu kuma zan dawo da ke gida cikin rashin saninki. Shin ke dabbar ina ce da ba za ki fahimci Ni abin tsoro ba ne? Shin ba da kanki kika je neman gidan kika rasa shi ba? Shin Iya ba ta ce miki minti 30 kika yi kika dawo ba. Shin baki tuna ko kukan da kika tafi kina yi a hanya kafin mu haɗu ya ci minti talatin ɗin. Shin baki tuna ranar da muke tsaye kika ji ana kiran suna na ba, shin ko ba taimako ba ne a ranar da na barki kina ta bulayin nemana aka tabbatar miki babu ko me irin sunana a anguwar, shin ko ba taimako ba ne a ranar da zan bayyana gabanki a garin da aka ɓoye ki saboda ni ba tare da ke kin kwatanta mini ba, ko kuwa Hadiyyar da na miki ƙarya da ita ta san gidan Iya na Kadunan tasan inda aka ɓoye ki? To waye ya kawo ni gidan da kike?”

Ta shiga jijjiga kanta da sauri tana toshe bakinta da ƙarfi cike da tarin nadama.

“Huzaif kai fa ka ce ko Babanka ne shugaban masu yankan kai na duniya ba za ka taɓa fansar da kaina gare ka ba. Ka tuna ranar?”

Ya numfasa yana jijjiga kansa.

“Shin yanzun ba da kanki kike magana ba, ko ba ga kan naki nan a jikin ki ba? A saboda kar na bada kan naki na nemi abinda ya fiye mini sauƙi ko ta gurin zunubi. Abinda bansan zai zame mini nadama. Haba Hamdiyya, idan Iya girma ya kamata na zauna na juyar mata da tunani, ke ɗanyar yarinya ce shakaf me kwalin sakandire da aka gama koya muku darussan lissafi a wannan lokacin da ba kowa ke barin yaronsa karatu ba.

A cikin tafiyar nan na taimaka miki iya yina zuciyarki da kwakwalwarki da basu san kome ba sai soyayyar banza su suka durƙusar da ke a banza a wofi, abu guda za ki gane ni ba zan iya rabuwa da ke ba sai dai ke ki rabu da ni. Kuma kar ki ɗauka so ne ya sa na dinga nuna miki waɗannan hanyoyin, ko kusa! Abu ne dana sani ko ba ke bace yarinyar da za mu gabatar da aikinmu da ma zan je ne da wannan niyyar, idan mutum ya fahimta ya tsira, idan bai fahimta ba na tsira.

Ta sake rushewa da ihun kuka tana bubbuga kanta jikin gado. Ya tallafo Kan nata yana leƙa idanuwanta da suka gama rinewa ya sakar mata da wani malalacin murmushi.

“Ba yanzu ya kamata ki yi kuka ba kina buga kai ki bari na faɗa miki ɗayan da son zuciyata da ƙaunar jin ƙan ƙi ya jawo mini, ni ya kamata na yi kuka saboda rashin hankalin da kika sanyani ciki bansan girmansa ba. Hamdiyya kina ɗauke da cikina na tsawon wata biyu, ko kin tuna ranar da na fara jan ki gidana? To a ranar ne na baki wata ƙwaya na kwanta da ke, ai kina tuna duk bayan wata sai na kai ki gidana? To a cikin wata ukun nan da muka yi tare sau uku ina aikata zina da ke cikin rashin hayyacinki. Kamar yadda na faɗa miki a wancan lokacin zan aure ki bayan wata biyu, to ina nufin zan ɓace daga rayuwarki bayan na kwanta sau uku da ke cikin wata uku.

A lokacin da nake shirin ɓacewa daga rayuwarki ne Oga ya sake ba ni umarnin yana buƙatar jininki ɗan kaɗan cikin sirinji uku zai ƙarasa aikinsa da shi, a yau na kawo ki nan ne dan ya ɗebi jinin ki kama gabanki, sai na tuna ciwon da ya ce ina da makusanta nama za su iya ɗauka, ni na nemo likita dan ya gwada mini ke ko kema kin ɗauka, a sannan ya ce mini kina da ciki, cikin da bana tababa zai zame mana masifa daga ni har ke. Hmm! Kar ki wani damu, yanzun zan baki kwayar da za ki haɗiya ya zube, zan buɗa miki hanya ki tafi can ki ɓace kafin Ogana ya hangi kome, shawara ɗaya, ki tabbata duk inda za ki gidan manyan malamai ne.”

Ya ƙarasa yana mamayarta ya afa Mata kwayoyin a baki ya matse bakin. Ta fara shure-shure kafin Allah ya bata sa’a ta haure shi a mafitsara, ya cikata cikin azaba ya yi gefe.

Ta miƙe tsaye a zabure ta dawo da kwayoyin ta yi gun wata ƙofa ta buɗe ta, ta ɗaga ƙafa za ta yi waje ta ji ya danƙota ta yo baya.

A sannan idanuwanta suka hango wajen, ashe babu kome sai wani ƙaton rami a gaban ɗakin, sai sannan ta fahimci a tsakiyar dokar daji gurin yake.

Ya kewayo ta bayanta cikin raɗa ya ce, “me kika gani? Ƙaton rami ko? Nan ne inda ake kawo duk wani da kwaɗayinsa ya kawo shi, wato masu ganin kuɗi ko Alewa a ƙasa su tsinta, wasu ƙaton kogi ma suke, wasu wuta na ci ganga-ganga, wasu ma manyan dawa suke gani na tanɗar harshen nama ya zo, irinsu Kura da Damisa kenan. Ki sake gwada gudu ba tare da izinin mai ɗakin ba!”

Ta matsa daga kusa da shi tana sake ƙanƙame cikinta cikin tsananin tashin hankali, zuwa yanzu hawayen sun ƙafe dan zallar masifa, ta gama jim abinda za ta ji, ta kuma fahimci shi ajali idan ya yi kira ko babu ciwo sai anje, ita nan ne ajalinta, asalima hanyar da za ta bi ta gudu rami ne, kenan babu wani hal sai karɓar dukkan abinda ya zo mata banda a guda! Ta nisa tana sake shafa cikin da aka ce tana da shi, wai kuma aka ce ta zubar da shi ta gudu. Wani murmushi mai ciwo ya kuɓce mata, ta kallo Huzaif da ya yi sororo yana dubanta ganin ta zame masa mahaukaciya. Ta kalli cikin idanuwansa ba ta hango kome ba sai dole da ke ɗawainiya da rayuwarsa. Ta sake murmushi ita kaɗai tana girgiza kanta. Sai kuma ta matsa kusa da shi ya yi azamar yin baya bakinsa a buɗe da zallar mamakinta.

“Idan ka ga na bar cikin nan ya zube to bana numfashi. Ka ce Cikinka gare Ni, kai ɗin da nake so ka yi mini Cikin, sai kuma na zubar saboda ina tsoron mutuwa? To na rantse da Ubangiji Mai Girma idan ma kai musulmi ne ko kafiri ne ai dai kasan girman rantsuwa da ALLAH ko? Ba zan zubar ba, zan yi kome wurin ganin na haife cikin nan na bar bayana, zuri’ar Babana ba za ta ƙare daga kaina ba…”

Sai kuma ta yi ƙasa da murya tana matsawa kusa da shi sosai.

“Huzaif ka nawa Allah ka zo mu gudu tare idan guduwar ne, mutanen nan ba inda za su kai ka sai halaka, ina ƙaunarka kome za ka aikata mini ƙaunar nan ta domin Allah na nan a ƙasa ruhina, ka zo mu gudu ka ga idan ta ciki ne Iya za ta fahimta, wallahi ina son abinda ke…”
Bai san ya yarfa mata mari ba sai da ya ganta zube a gabansa tana gurshiƙeken kuka, bai san yarinyar ta ci sunan jakai ba sai da ya jita ta rarrafo ta riƙe ƙafarsa tana sake roƙarsa wai da su guda tare saboda gashi Kawu ƙanin uban da ya haifi ubanta. Cikin azabar zuciya ya sanya ƙafa ya haureta a cikin ta yi can baya tana sakin ihun azaba jin mararta ta tamke, a sannan ne sautin kiran sunansa ya ratsa ɗakin. Ya juya da gudun bala’i a bayan ya maida mata zoben nan ya ƙara ga ɗan toilet ɗin da ke cikin ɗakin ya shige ciki domin amsa kiran Oga.

*****

“Kana ji waccar yarinyar da kuke tare ya kuke da ita ne?”

Huzaif ya yi wani ɓoyayyen murmushi yana sanya hannu ya sosa ƙeyarsa cike da kunya.

“Abba Ɗaliba ta ce…”

“Au to to to.”

Abba ya furta yana ɗaga hannu ya zare hular kansa ya ajeta saman mota.

“Ka daɗe kana fatar ganina cikin farin cikin da zai a dawwama a rayuwata, haka ka daɗe kana begen ganin wacce za ta zame maka madadin uwa a mahallinmu, idan har da gaske kana mini fatar mutuwa cikin salama, to ka shige mini gaba na samu waccar Ɗalibar taka a matsayin mata, wa billahil azim ita kaɗai nake so nake muradin ƙarasa sauran rayuwata da ita.”

Huzaif ya yi tsai kansa a ƙasa yana kokawa da bugun zuciyarsa da ke ƙoƙarin fallasa abinda yake dannewa. A sannu ya ɗago da idanuwansa da suka fara kaɗawa ya dubi Abbansa da ke ta washe baki yana leƙen Haƙabiyya da ke can nesa. Zai iya rantsuwa da Allah rabon da ya ganshi cikin farin ciki irin wannan tun bai fi shekaru tara ba. Zai iya rantsuwa da Allah rabon da ya tsaya ya masa magana mai tsayin wannan tun kafin ya gama secondary, tun tasowarsa bai taɓa ganinsa da wata mace ko ya nuna muradinsa kan wata ko da kuwa a tv ne bai taɓa ba, kai ya sha ɗaukar wayarsa ya duba contact ko zai ga number ta wata mace guda ɗaya tal! Bai yi katari da hakan ba. Da shi kaɗai ya tashi a tare suka gabatar da kome na rayuwarsu ba tare da tallafin wata ɗiya mace ba. Kai a cikin idanuwansa yake hango ranakun da suka gabata Abban nasa ke masa wanka ya haɗa masa abinci ya kai shi makaranta. Ya masa duk wani abu da uban da ya amsa sunansa na uba zai yi, bai  tauyeshi ta ko’ina ba bai kuma taɓa shiga rayuwarsa daidai da kwayar zarra ba. A yau ga rayuwa ta kawo su inda Abbansa zai dubi cikin idanuwansa ya rantse masa da girman mahaliccinsa yana son wata, to shin waye shi da zai hana mahaifinsa abinda yake buƙata? Waye shi da zai yi tsaye a cikin farin cikin mahaifinsa? Wacece Haƙabiyya a zuciyarsa da ba zai hana zuciyar tasa ita ba? Wacece Haƙabiyya a duka rayuwarsa da ba zai iya sallama masa ita ba? To menene ma zai saka shi tsayawa dogon tunani akan abinda ya haramta a gare shi a tun lokacin da mahaifinsa ya furta muradinsa kanta?menene ma zai saka shi tsayawa yana jajantawa kansa? Wane irin so ne yake mata da zai rufe masa ido harda ƙoƙarin kwalla dan mahaifinsa ya ce yana so? Wane irin so ne da ba zai iya sadaukarwa da Mahaifin nasa shi ba? Ya godewa Allah ya daɗa gode masa da bai kai ga furta mata abinda ke zuciyarsa ba, bai kuma yi wani abu da za ta fahimci yana cikin ƙaunarta ba, ya yi tur da abinda zai saka shi yiwa mahaifinsa baƙin ciki, ya yi Allah wadai da shaiɗanin da ke sake ƙawata masa ita cikin zuciyarsa.

Da wannan ya ɗaga ƙafarsa cikin hanzari yana mai buɗe ƙofar motar ya jawo hannun Abban nasa ya tura shi cikin motar, ya duƙa saitinsa ya masa kyakkyawan murmushi, ba tare da ya tuna wacece ita gare shi ba, ba kuma tare da ya tuna jarabar son da take masa ba ya cewa Abba da ya tafi idan har shi Malamin Haƙabiyya ne da take matuƙar girmamawa to kuwa ya sameta ya gama. A yanzun zai je ya faɗa mata saƙonsa, zai kuma raka shi har gidan da take su ga mahaifinta.

Abba ya yi dariya yana gyara zaman babbar rigarsa, ya kalle shi ya daɗa kallonsa ai sai ya rarumo hannunsa ya rungume, ji yake tamkar an masa albishir da aljanna, kai yama manta rabon da ya ji shi a cikakken mutum irin yau.

“Na gode Huzaifuna, Allahu ya maka albarka ya cika maka dukkan buri. Gidansu ai na sani, tun rannan na ganta a ƙofar gidanka hankalina ya kasa kwanciya sai da na bibiyi har gidansu, wannan yaron Zakari nasa ya binciko mini inda take, sai dai ban bayyana gabanta ba ina shakkar waɗannan ‘yan matan na zamanin Buhari sai a hankali…”

Sai kuma ya nisa ganin Huzaif ɗin ya zuba masa ido da siffar mamaki.

“Aw gidanka da na ambata ko…?”

Ya danyi murmushi yana sosa goshinsa.

“…Ai ina shiga jefi-jefi idan baka nan, ina da mukallayen duk wani gida naka daka sani, kasan aje matashin yaro kamar ka mai girman gwauro sai ana yi ana bibiya, ka sani ba na son shashanci ko kaɗan.”

Huzaif ya murmusa yana raba jikinsa da motar.

“Shi kenan Abba ka je, bari na koma na mata bayani.”

“Yauwa to ka bita a hankali dai, ka fa faɗa mata ba tsoho ba ne Ni, kar taji ka ce Babanka ne ni ta razana, kasan ba za ta duba kai ɗin nawa kake ba shekaru za ta ɗebo ta yaɓa mini, Ka mata bayani sosai ka sanar mata shekaru hansin gareni da ‘yan wasula.”

Dole tasa Huzaif yin dariya har haƙoransa suka bayyana.

“Abba kar ka damu fa, za ta fahimta ai.”

“To ai shi kenan, amma ni idan ba ganinta na yi gidan can ba damuwa yanzu na fara, jeka Allah yasa a dace, yauwa ka ce mata ta sanarwa tsohonta gobe za mu shigo.”

Da haka ya tada motar ya tafi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Hakabiyya 11Hakabiyya 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×