Yaraf! Ta faɗa kan gadonta tana sakin gunshekeken kuka ta ma rasa kalar tunanin da za ta yi. Allah ya sani ta tsani mutumin nan tun kafin tasan waye balle yanzu da taji yana shirin rabata da farin cikinta. Shin ko taje gun Zawwa ta ce mata a nemo abokin Baba ta idasa cutar kanta ko kuwa ta ci gaba da nacewa Huzaif yana tura mata Mahaifinsa? Ta tuna fuskar mutumin sa’adda suka haɗa ido ya kafe ta da kallo. Kenan daga lokacin ya fara sonta har ya zo gidansu cikin mota yana cewa ta dinga. . .