Haka rayuwarsu ta miƙa, Hamdiyya babu ranar da za ta fito ta wuce ba tare da ta yiwa Huzaif tayin guduwa ba, sai dai koda wasa bata ɗau hankalinsa ba. Haka ita kaɗai take kwana a gun bai taɓa kwana inda take ba, wani bin ma sai ya yi sati bai zo ba, sai da oga Tunjim ya gargaɗe shi da hakan yana tada mata hankali tukunna ya zo yana zuwa duk bayan kwana biyu.
Bata rasa kome na ci da sha ba haka ta bangaren lafiyarta kome da zai ƙarawa Baby lafiya yana kawowa haka. . .