Skip to content
Part 15 of 32 in the Series Hakabiyya by Fulani Bingel

Haka rayuwarsu ta miƙa, Hamdiyya babu ranar da za ta fito ta wuce ba tare da ta yiwa Huzaif tayin guduwa ba, sai dai koda wasa bata ɗau hankalinsa ba. Haka ita kaɗai take kwana a gun bai taɓa kwana inda take ba, wani bin ma sai ya yi sati bai zo ba, sai da oga Tunjim ya gargaɗe shi da hakan yana tada mata hankali tukunna ya zo yana zuwa duk bayan kwana biyu.

Bata rasa kome na ci da sha ba haka ta bangaren lafiyarta kome da zai ƙarawa Baby lafiya yana kawowa haka za ta zauna ta suɗe abinda tas! Ta kora da ruwa.

Hankalinsu bai fara tashi ba sai da cikinta ya tsufa sosai ita kanta har ta manta lissafin cikin. A sannan ne take yawan matsa masa da koken su tafi haka tana jin a kowane lokaci Babynta zai iya zuwa duniya. To shi kansa hankalinsa a tashe yake. Allah ya sani zuwa lokacin ba abinda yake ji da ƙauna irinta, burinsa a rasa Babyn ko ita za ta rayu, a tsakankanin lokacin ne yake ta nuna mata hanyar da za ta gudu amma sam bata fahimta.

To, a yau ma da ya shigo mata da Kankana tsayawa  kawai ya yi yana kallonta ganinta acan lungu tana hawaye. Jikinsa ya daɗa sanyi, ya matso kusa da ita da sauri ya duƙa gabanta yana kiran sunanta.

Ta lumshe idonta ta buɗe ƙaunarsa da dukkan wasu lamuransa na sake zauna mata a rai. Ta buɗe baki za ta yi masa magana wasu ambaliyar hawaye masu ɗumi suka yi cikin bakinta. Ta miƙa hannu ta jawo hannunsa tana mai ƙanƙame shi tare da tulun cikin jikinta.

“Huzaif! Ya isa haka!! Ka nawa Allah ka ƙaunace ni dominsa, ka nawa Allah ka tabbatar mini da gaskiyar zuciyarka a yau. Ka nawa Allah ka ƙaunace ni ko domin halittar jininka da ke mahaifata.”
Ya zare hannunsa a hankali yana mai tura shi cikin aljihunsa.

“Haba Hamdiyya? Zuwa yanzu ya kamata ki yarda ban taɓa son ki ba. Shin me zan yi ne da zai tabbatar miki da dukkan soyayyar da na gwada miki shekarun baya ƙarya ce? Me zan yi da zai tabbatar miki da mummunan ƙudurin da na samo ki? Wai ke me zanyi ne da za ki tsaneni da gasken-gaske? Ba ki ga abinda na miki ba ne? Ba ki ga yadda na kacalcala rayuwarki ba na rabaki da danginki, ko kuwa baki tuna haiƙe miki na yi? Ba ki tuna cikin wata uku sau uku  ina aikata zina da ke a cikin rashin saninki? Wai ke a ina aka dasa zuciyarki ne da hankalin da zai na ƙubutar da shashashan tunaninki kaina, a ina kika taɓa ganin wanda ya furta ƙaunarka ta haƙiƙa zai kai ka ga halaka? Wai baki yadda na kawo ki nan ba ne a zuƙe mini jininki domin maganin laruruta? Wai meyasa ne baki ƙyamata? Me yasa ne baki tuna kin kusa mutuwa? Me yasa ne baki tausayin abinda ke cikinki sai damuwarki? Me yasa ne ba za ki yi abinda zai tseratar da?”

“Me yasa ne ka damu zan mutu? Me yasa ne a cikin idanuwanka nake hango girman tsoron da kake ciki?Me yasa ne kake jin ciwon abinda ka aikata. Me kuma yasa har yau baka bawa mutanen naka damar kasheni ba, me kake jira ne Huzaif?”

“Ni na faɗa miki ina jin ciwon abinda na aikata? Ni na faɗa miki zan taɓa nadama kan hakan?”
“Hmm!” Ya duƙa gabanta wani guntun murmushi na bayyana a fuskarsa.

“Hamdiyya ba ke ce ta farko ba, na ɓatawa wanda ya fiki sau dubun dubata har yau ban ji kome ba!”
Ta dube shi a yayin da idanuwanta suka ƙara girma, ta shiga girgiza masa kai tana jin hawayen na ƙafewa cikin idanuwanta. Ta yunƙura ta miƙe tsaye a yayin da wani jiri ya kwasheta ta yi taga-taga za ta faɗi ya yi saurin tallofota jikinsa. Da ɗan sauran ƙarfin da ya rage mata ta fincike jikinta daga nasa.
“Huzaif na ji na yarda baka taɓa ƙaunata ba, na ji na yadda baka fara nadama ba, amma domin girman mahaliccinka ka zo mu gudu daga gurin nan, ka zo muje ka nemi gafarar mahaliccinka da duk wanda ka ɓatawa, ka ji tausayinmu domin Allah ka ji tausayin yaronka da yake ciki…”

“Ba na buƙatar shi, ba na buƙatar kome sai wannan halittar da kome zan yi ba zan maida mata kwatankwacin abinda ta mini ba. Ya kamata ki gane biyayya ga maganarki na nufin yin bankwana da dukkan wani abu da nake so ciki harda dalilin da ya kawo ni gare ki. Ke idan har da gaske kina ƙaunata to ki barni a yadda kika ganni tunda dai ni ba Kawu ba ne jinin Babanki, idan har kina son in bar wannan abin da nake yi to ki yi wani abu guda ɗaya wanda shi ne ki haƙa rami ki binne kan ki. Babu abinda nake zame miki ba kuma zan taɓa zame miki ba…”

“Amma wannan ya haɗa…?”

Ta furta tana nuna masa cikin jikinta cikin ƙarfin hali.

Ya saki wani murmushi yana jijjiga kansa.

“Yaro-yaro ne, saboda baki san sau nawa na sha baki maganin da zai saka shi bin rariya ba? Baki san sau nawa kika sha maganin barci likita ya wuni cur! Kan ki domin cire shi da ke cikin jaraba ne ya ƙi fita. Hamdiyya abubuwa da yawa ke kika jawowa kanki da har kika zaɓi abinda bai zo duniya ba akan taki rayuwar.”

Ta yi masa wani murmushi mai ciwo tana komawa baya.

“Wannan ke nuna maka abinda ke cikina rayayyeni a bayan raina ko naka…”

“Ba za ki haife shi ba, ba kuma za ki ga koda kalarsa ba! Wannan shi ne alƙawari na biyu da na miki da ba zan iya cikawa ba, ba zan iya kuɓutar da abinda ke cikin…”

Ganin yadda ta durƙushe tana riƙe saitin mararta ya saka shi ƙarasawa gareta da sauri yana riƙe ta. Sai a yanzu ya kula da jinin da ke bibiyar ƙafarta. Hankalinsa ya tashi ya fara waige-waigen neman abinyi sai dai ya rasa, a wannan halin ya ji ta sanya hannu a hankali ta shafo kuncinsa, ta buɗe baki cikin azabar ciwo ta fara magana… “Ba na nadamar zan rasa rayuwata ta dalilinka, sai dai ina nadamar da har zan tafi ba tare da na tabbatar da ƙaunarka gare ni ba. Ba na nadamar saninka da kuma son rayuwa da kai, sai dai ina nadamar da har zan tafi kana aikata wannan zunubin mai muni, domin Allah ka tuba ko zan iya rayuwa da kai cikin Aljanna. Domin Allah ka kuɓutar da jininka ko hakan zai sanyaya mini raina, domin Allah ka ƙaunace ni a bayan raina ko hakan zai sanyani farin ciki a yayin da nake kushewata. Domin Allah ka faɗa mini gaskiyar wannan soyayyar da nake maka nake jin rabuwa da kai abu ne da babu shi a shafin ƙaddarata, nake jin a kullum kwanan duniya ana sake ƙyanƙashe sonka da ƙaunarka cikin zuciya, ta gaske ce ko kuwa ita ma da tsafi aka ƙirƙira mini ita?”
Girgiza mata kai ya yi alamar a’a, a sa’ilin da ya yi maza ya maida kwallar idonsa.

Ta yi murmushi mai sauti tana sauke wata irin ajiyar zuciya.

“Huzaif kana so na da gaske ka gafa kwalla kake yi… Ba za ka nemi yafiyata ba har yanzun?”
Ta furta tana miƙa hannunta saitin idonsa ta shafo kwallar… A sannan ne ƙofar ɗakin ta buɗe, wani haske mai ƙarfi ya dallere musu ido, kafin kuma a hankali hasken ya yaye mutumin da basu zaci ganinsa lokacin ba ya bayyana, a bayansa Ado Maɗaci ne da Alhaji Hashim a wani irin mummunan yanayi. Huzaif bai san sa’adda ya saketa ya miƙe tsaye yana mai duƙar da kansa ƙasa ba.
Fuskarsa murtuk! Ya dube shi. “ Kasan ta fara naƙudar shi ne ba za ka mini ishara ba?”

Ya ƙara sunkwi da kansa alamun neman afuwa.

Ya kai kallonsa ga Alhaji Hashim da ke tsaye gefensa tsirara. “Ba ni ƙoƙon.”

Ya taho tunɓur-tunɓur ya miƙa masa ya koma baya.

Ya waiwaya ya dubi Maɗaci da ke tsaye bayansa.

“Ɗauketa ka kaita can maqabartar da ta bayyana gare mu, ka haƙa rami ka jefeta ciki ka maida ƙasar. Ko da za ta haihu kafin ku isa ka binneta ita da abinda ta haifar. Ka kula ba na buƙatar kowane irin kuskure a wannan ranar! Ka kula ba na buƙatar kowane irin ganganci a wannan ranar!!

Yanzu miƙo mini ita nan gabana.”

Ya taho kanta gadan-gadan, ta ɗaga kanta ta dubi Huzaif da ya ɗauke kansa. Ai sai ta fasa ihu tana matsawa can baya.

“Huzaif kana gani fa, ka ce musu su bari na haihu! Huzaif ɗan ka fa za a kashe!!”

Tana ganin sa’adda ya sake juyar da kansa baya ma kallo sashin da take. A lokacin ne Maɗaci ya cimmata ya fara janta tana tirjewa. Yana gabda danƙata hannunsa ne ta daddage ta gartsa masa cizo a yatsansa ya cika ta ba shiri. Baya tayo da gudu tana faɗawa jikin Huzaif, ta dunƙule hannayenta tana dukan ƙirjinsa da ƙarfi. Maɗaci ya yunƙuro zai ƙara yo kanta Alhaji Hashim ya ɗaga masa hannu da ya dakata. Suka zuba musu ido kawai ganin magana take masa.

“Ba za ka iya ƙuɓutar da ɗanka ba? Huzaif ka faɗa mini menene naka a gurinsu da ya fi jinin ɗanka, ka amsa mini tambayar da na sha yi maka wanene kai?Me waɗannan mutanen ke zame maka?”

Kauda kansa gefe ya yi yana matsawa daga kusa da ita, ta sake binsa ta juyo da fuskarsa saitin tata. Ta riƙe mararta cikin azabar ciwo tana cije baki.

“Shi kenan, shi kenan na fahimceka, sai dai zan roƙe ka wani abu guda, ka dubi girman Allah ka amsa mini tambaya biyu da zan maka tunda tafiya zanyi inda ba a dawowa, babu wani amfani da boyewar zai maka. Wannan labarin daka ba ni a tun baya na ciwon Ummanka, shi ma yana cikin labarun da ka kirkira dan samun zuciyata?” Ya fi ƙarfin second 40 kafin ya girgiza mata kai alamun a’a.

Fuskarta ta wadatu da wani irin annuri, cikin shesshaƙa ta ƙara dubansa tana rasa dalilinsa na ƙin buɗe baki ya mata magana.

“Shi ne dalilin kome da ke faruwa?”

A hankali ya gyaɗa mata alamun “E.” 

“Menene sunanka na gaskiya?Ban yarda Huzaif ba ne tunda ka ce kome da ka yi amfani da shi domin samuna ƙaryane, hatta nasabar da ka zo mini da ita.”

Ya ɗago idanuwansa da suka ƙara kaɗawa jajur ya sauke cikin nata. Sun fi ƙarfin rabin minti suna duban juna har ta fara fidda tsammanin zai faɗa mata. Sai can bakinsa ya buɗe a hankali ya ce mata.
“Hameed Siddiqu.”

Hameedu!. Sunan ya fito tun daga ƙasan zuciyarta yana bayyana a saman laɓɓanta.

A sannan ne hannun Maɗaci ya danƙota ya fara janta ta bi shi ba tare da ta ƙara neman agajinsa ba, ba kuma tare da murmushinta ya kau daga fuskarta. Wannan wani abu ne da ta bar masa mai wahalar gogewa cikin ƙwaƙwalwarsa.

A kan idanuwansa biyu Oga Tunjim ya fiddo wani kakkaifan alkamashi da aka tsafance shi ya sanya a tsakanin yatsunta ya tsarga saitin jijiyarta da ke gudanar da jini ya tara ƙoƙon hannunsa jinin na zuba a ciki. A kuma cikin kunnuwansa ya ji sautin ihunta tana ambaton sunan Allah kafin kuma ya ji shiru a yayin da duhu ya lulluɓe cikin idanuwanta duhun da ba zai taɓa yayewa gareta ba.

Har sa’adda aka fita da ita yana hasko murmushinta.

Har kuma sa’adda Maɗaci ya dawo ya ba shi tabbacin ya binneta bai bar jin sautin kukanta cikin zuciyarsa ba.

Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana kallon muhallin da take zaune a ɗazu kaɗan. Wata sassanyar kwalla ta sauko masa ya sanya bayan hannunsa ya share yana tuna ‘yancin da ya samu.

Ga mamakinsa sai ya ji dukkan tunaninsa ya tsaya ya cik! Ya waiga ya ƙara waigawa ya ji gabaɗaya ma ya rasa me yake yi anan gurin.

Da sassarfa ya ɗaga ƙafarsa yana mai ficewa daga ɗakin. Ɗakin da har yau ya rasa a irin duniyar da aka gina shi, dan kuwa ya ɓace masa ɓat! Har a cikin tunaninsa baya iya hasko muhallin da yake bi ya isa ga ɗakin!!.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Hakabiyya 14Hakabiyya 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×