Skip to content
Part 17 of 32 in the Series Hakabiyya by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Wani asibiti da ke cikin birnin na Bauchi ya yi da su. Ba wahala aka karɓe su, sai dai fa su kansu hankalinsu ya tashi da yanayin Innar Hameedu dan sun gano ciwon zuciya ne ya mata mummunan riƙo, gashi ba su da wadatattun kayan aiki, asalima kaf asibitin oxygen ɗaya gare su, haka suke sawa Hameedu su cire su sakawa Inna da wasu mutum biyu. Dan haka suka bashi shawarar da lalle za su yi iyayinsu amma washegari ya ɗauke ta zuwa Kano akwai wani babban likitan zuciya a asibitin Murtala.

Hakan aka yi washegari bayan Hameedu ya farfaɗo an ɗinke masa kafaɗar ya ɗan ji dama-dama Alhajin ya ɗauke su da wani likita suka yo Kano. Anan ma likitan ya daɗe yana faɗa na yadda aka barta abin ya tsananta wanda dole yanzu idan har ana son ta samu lafiya gabaɗaya sai an fita da ita waje, zai dai yi iya nasa ƙoƙarin na ganin bata ƙara shan wahala ba.

Satinsu biyu anan asibitin Inna ba ta farfaɗo ba duk da kome ya nuna tana da sauran rai. Hameedu tun yana sakata a gaba ya yi ta kuka har ya fara saduda sai dai ya yi lamo a jikin gadon da take kwance, ya manta gida gabaɗaya kai baya tunanin zai iya barin Inna ko na minti talatin ne dan zuwa wani gun. Ya sani indai Huzaifu ne Bawa zai karɓe shi, haka yaron yana da wayon da zai faɗawa kowa Inna ce ba tada lafiya Babansa ya tafi da ita.

A haka wataranar da take daidai da cikarsu wata guda a asibitin Alhajin ya zo ya same shi da cewar shi zai tafi garinsu dan shi a Lagos yake harkokinsa, a sannan ma akwai abubuwan da ya gabatar a Kano shi ya sa ya kawo wannan lokacin.

Hankalin Hameedu bai tashi da tafiyarsa ba sai da ya ji yana umartarsa da sauran bill ɗin da bai biya ba har na sati guda ya faɗa musu shi zai bayar, ya manta shaf ana biyan kudi, kai bai ma tuna da hakan ba tsabar kidimewar da ya yi.

“Alhaji ka taimaka mini dan Allah, wallahi ba mu da kome da za mu biya na wannan asibitin, gashi Inna ba ta motsi balle na ɗauke ta na maidata ƙauye a ci-gaba da yi mata wanda ake matan.”

Hameedu ya furta a bayan ya saka gwuwowinsa a ƙasa a gabansa.

Wani murmushi mutumin ya yi, a karon farko tun shigowarsu asibitin da ya zare baƙin tabaron idonsa ya shiga ƙarewa Hameedu kallo, kafin kuma ya sauke idanuwansa kan Innar yana nazari. Sai kuma ya janye idanuwan yasa hannu ya miƙar da Hameedu tsaye.

“Da gaske ba kada komen da za ka yiwa Innarka magani?”

“Ba ni da, da ina da da ba ta kawo I wannan matsayin ba.”

“Idan na ce zan taimake ka Innarka ta samu lafiya, kai kuma da me za ka taimaka mini?”

A gigice Hameedu ya durƙushe gabansa.

“Zan maka duk abinda kake so, zan zama yaronka idan kana so, idan ma bawa kake so na zama gareka zan zama. Ka taimaka mini Inna ta miƙe, domim Allah ka taimaka mini ita kaɗai gareni!”
Mutumin ya haske shi da wani bushasshen murmushi.

“Ba wannan nake son ji ba, abinda nake so ba lalle ka yarda ka mini ba. Amma tabbas wannan abin shi ne fansar maganin Innarka duk da a tafiyata babu marar lafiya dubawa zan yi na gani. Wace ma ƙasa likitan yake ba mu shawarar mu kaita?”

Bakinsa na rawa ya ce masa India.

“Yauwa to zan kaita can na mata magani da gumina da ƙarfina Idan har ka yarda.”

“Me kake so? Na rantse da girman Allah zan maka ko da kuwa ace shi ne abu na ƙarshe da zan yi ya kai ni ga kushewata lna yarda zan maka.”

Mutumin ya numfasa har yanzu da bushasshen murmushin a fuskarsa. A hankali ya taka ya tsaya a saitin kunnensa.

“Akwai sharaɗi, idan har na riga na furta maka baka isa ka ce a’a ba, idan ka kuskurewa wannan maganar dukkan abinda ya faru gare ka kar ka yi kuka da ni, ka yi da kanka, a kuma nasiha ɗaya da zan maka irin wacce ba zan ƙara tuna maka ita ba, kana da damar da za ka barwa Allah kome Innarka ta warke ba tare da wani taimakona ba, ka sani duk da ina son abu gare ku, duk da ina tunanin za ku iya cika mini burina, Ni ban jawoka gare ni ba kai ka nemi taimakona…”

Shiru ya yi yana yin baya jin wani tsoro na mamayarsa a karon farko, haka ya gaza fassara da yawa-yawan kalaman Alhajin, ya ƙara taku guda ta baya dan ya nisanta kansa da shi ko ya samu damar tunani ya ji ya ci karo da gadon Innar.

“… Kar ka damu, a yanzu da ban riga na furta maka ba zan iya tafiya. Allah Ya bata lafiya.”

Ya maida gilashinsa ya juya, sai dai taku biyu ya yi Hameedu ya riƙe rigarsa ta bawa.

“Na yarda da koma menene idan har Inna za ta samu lafiya shi ne burina. Na ɗade ina roƙon Allah da warkewarta ina ga shiyasa na haɗu da kai dan ka zama sila, ka sani Ubangiji mai yawan jin ƙan bayinsa ne. Na yarda na fansar da rai na gareta ita uwa ce a gare ni da ba zan taɓa maida mata wahalar dakon cikina da rainona da ta sha ba!”

Mutumin ya juyo da wani yanayi mai kama da sanyin jiki, akwai wani abu da ya bayyana a fuskarsa sai dai kafin ya farga ya maye gurminsa da wannan bushasshen murmushin nasa.

“Ka yi tunanin mai kyau yaro.

Abu guda biyu nake so a gare ka, zan faɗa maka na farkon yanzu, na biyun kuma sai nan da awanni biyu za ka ji, wanda shi ne mai wahalar…”

Ya numfasa yana sanya hannu cikin aljihunsa ya zaro wani ɗan ƙaramin almakashi ya miƙa masa.
“Karɓi wannan ka datso mini ƙarshen gashin Innar taka…”

“…Kar ka damu, shi ne tsanin samun maganinta…”

Hameedu ya yi baya taga-taga ya dafe bango yana danne saitin zuciyarsa da yake ji za ta fasa allon ƙirjinsa ta fito tsabar razana. Wani sassannyan gumi da ya yanko tun daga tsiron gashinsa na farko ya ji ya wuce cikin bakinsa ya ji ɗanɗanon gishirin har tsakiyar kansa, ya lumshe ido ya buɗe yana sauke su a hannun Alhajin da ke ɗauke da Almakashin, ya zarce da su kan fuskarsa da ke haske shi da murmushin da a yanzu ya zame masa na baƙin kumurci. Ya fi ƙarfin minti biyar a wannan yanayin ba tare da ya yi wani kwakkwaran tunani ba. Can yaja wani zazzafan numfashi ya fesar kafin kuma ya miƙa hannunsa a hankali ya karɓi almakashin ya taka gaban Inna ya zare ɗankwalin kanta.

Ba tare da ya tsaya hora zuciyarsa da tunani ba ya sanya alkamashin ya yanko gashinta, hannunsa na rawa ya juya ya miƙa masa.

“Sunana Alhaji Hashim Abraham…”

Alhajin ya furta yana miƙa masa hannu bayan ya tura gashin cikin Aljihunsa.

“…Wancan sunan, Idrisa, da na faɗa maka ba shi ne nawa ba, wannan ne na haƙiƙa. Ina maka maraba da sanya rayuwarka da kayi cikin tawa. Na tafi, nan da awa biyu za mu haɗu.”

Daga haka ya juya akan takunsa mai ƙarfi ya fice daga ɗakin.

Hameedu ya bi bayansa da kallo kafin kuma ya sauke idanuwansa kan hannunsa da ya haɗa dana Alhajin.

Ga mamakinsa sai ya ji ya gaza tuna wani abu mai muhimmanci da ya gabata, haka ya rasa tunanin daya dace ya yi.

A sannu ya ja kujera ya zauna yana kafe tagar ɗakin da ido.

A sannan kuma ya fara ƙanƙame jikinsa sa’ilin da ya ji wata sassanyar iska na ratsa duk wani tsiron gashi na halittarsa! Idanuwansa suka fara lumshewa a hankali, sannu a hankali ya tafi wani barci mai nisan da ya gigita rayuwarsa.

*****

Cikin duhu wani irin duhu mai tsananin da baya iya ganin ko rabewar yatsunsa ya samu kansa a ciki, jikinsa ya yi nauyi yana jin tamkar an danne shi da buhun Alkama, ya fara jan jikin nasa da yake jin kamar yana saman ruwa, zuciyarsa cunkushe take da wani abu da bai san menene ba shi dai yasan ba tunani yake yi ba ba kuma bacci yake yi ba. Ya buɗe baki zai kira Innarsa ya ji kamar an saka gam an liƙe masa bakin. Ya sake numfasawa yana ƙoƙarin dagewa ya tashi zaune a sannan ne ya ji wani abu tamkar gizo-gizo na tafiya saman kansa, ya miƙa hannunsa da yake jinsa cikin ruwan da bai san menene ba ya shafo kan da yasan cike yake da cukurkuɗaɗɗiyar sumarsa irin ta fulanin daji, ga mamakinsa jin kan ya yi tamkar bayan kwarya an tanɗe an suɗe gashin tas! Tamkar wani abu bai taɓa tsirowa saman kansa ba, ya yi wata irin zabura ya tashi zaune yana jin yadda ƙafafunsa suka yi facal cikin ruwa, ya ƙara shafa kan yana zarcewa da hannun saman idanuwansa ya dirza idon ya mutsittsika a tsammaninsa na farkawa daga barci a tsamaninsa na tashi daga mummunan mafarkin da yake yi, sai dai hakan bai faru ba a sa’ilin da ya buɗe idanuwan ya ƙara ganinsa cikin duhun da baya iya ganin gabansa. Ya sake zabura yana rarrafawa zuciyarsa cike da tsoro mai girman da ke ƙoƙarin dakatar da fitar numfashinsa ya manta koda wata aya guda da zai iya ambata domin kariya, a lokacin ne wani haske mai tsananin da ya dakatar da ganinsa na sakanni ya gauraye gurin, yana-yanar da ta lulluɓe idanuwansa ta yaye ya tsinci kansa a tsakiyar wani tafki cike da jinin da ya zo masa har ƙirji. Ya kwada razananne ihu yana facal-facal ɗin ƙoƙarin fitowa daga wurin, a sannan ya fara jiyo takun tafiya ya ɗan saurara kaɗan takun na daɗa kusantowa gare shi fuskar mutanen na washe masa har suka bayyana su biyu tal! Baƙi mummunan Dattijo hannunsa ɗauke da sanda, sai mutumin da ya kira masa kansa da Alhaji Hashim tsaye kusa da dattijon ya ɗaura wani jan yanki a cikinsa da goshinsa.

Bakinsa buɗe idanuwansa tamkar za su faɗo haka ya tsaya yana kallon saitin Alhaji Hashim yana ƙaryata zuciyarsa da kwakwalwarsa da ke gaya masa mafarki yake yi, yanzu ya gane da miyagu ya haɗu ya gane yana inda idan aka azo ba a taɓa fita da rai, ya gane yana irin gurin nan da su Garbati ke ta basu labari idan sunje birni, irin gurin nan da yake ji a labari ana cire kan mutane a maida shi kuɗi, to amma ina Innarsa? Ya zabura yana waiwaigawa da nufin nemanta, ya sa bayan hannunsa da ke cike da ruwan jini ya goge hawayensa, ya buɗe bakinsa da ƙyar da yake jin tamkar an saka zare da allura an ɗinke ya ce yana kallon Alhaji Hashim “ina Innata, tana asibiti, Ni kaɗai anan ko? Ina take?”
Yana kallon yadda laɓɓansu suka wadatu da murmushi, yana kallo baƙin Dattijon ya yi wasu surutai yana ɗaga sandarsa ya nuna saitinsa, nan take wannan ruwan jinin da yake cikinsa ya ɓace ɓat! Ya ganshi a saman wani faffaɗan jan yanki, cikinsa ya yamutsa nan ya duƙe yana kelaya wani irin baƙin amai na guda-gudan ɗanwaken da ya ci a safiyar ranar, a galabaice ya durƙushe yana sakin numfarfashin wahala.

Alhajin ya matso saitinsa ya duƙa ya riƙo haɓarsa ya taso shi zaune yana mai kafa masa ido sai kuma ya kece da dariya yana juyawa ya kalli baƙin Dattijon.

“Oga Tunjim ka ga dakakken namiji yana kuka tun kafin ya ga kan wasu na zama Dala? Ka taɓa ganin inda idanuwan farin namiji suka koma ja jajur?”

Oga Tunjim ya sheƙe da dariya kafin kuma ya haɗe rai yana kallon Alhaji Hashim.

“Na taɓa ganin na Babansa ma, ko Ka manta kai ma da kuka ka shigo mana nan kana neman duniya?”

Alhaji Hashim ya turɓene fuska yana maida kansa saitin Hameedu da ke ta sharar hawaye ya zabga masa harara.

“Bari kuka yaro ba yanzu ya kamace ka da shi ba, kasan wanene Ni?”

Bai jira amsarsa ya ɗora.

“Ni wani mutum ne da na fito daga wani ƙauye da ke can yankin yarbawa na shigo duniya na tsunduma kaina a ƙungiyar asiri saboda neman ita duniyar, kasan mai nake so a duniyar? Ka ringa girgiza mini kai idan na tambayeka ko yanzu na datse kunnenka ɗaya ya zama sule…”

Hameedu ya girgiza kai a razane yana dafe kunnensa ɗaya da ƙarfi yana shessheƙa.

Oga Tunjim da ke gefe ya sheƙe da wata irin dariyar mugunta.

“Yauwa….Mulki nake so yaro, mulkin da zan mulki duka Nijeriyar taku, mulkin nan dai da za a bayar a shekarar alif ɗari tara da casa’in da bakwai (1997) nake so yaro, ka ga shekarun da saura ko?…”

Ya furta yana wani irin jijjiga.

“To tun muna 80s nake jiran wannan ranar, saboda ranar na kawo kaina nan gurinsu Oga Tunjim suka yi alƙawarin za su bani mulkin koda kuwa wahalarsa daidai take da matar jaki(jaka) ta haifi zomo ko kuma raƙumi ya fita ta ƙofar allura za su ba ni. Kasan sai yaushe yadda zan samu mulkin ba tare da siyasa mai tsanani ba, a kuma bani shi ta dolen dole idan ma da wani kan mulkin za a wayi gari ya mutu ya bayyana gare mu? Sai a wannan shekarar yaro, a tun ranar kuma nake neman abinda zai zama tsanin samun mulkina, a saboda shi ka ganni a yankinku ka ganni na fito daga wannan surƙuƙin da mutane basu shiga har na kaɗe ka na kawo ku asibiti da ke Kai ɗan ƙauyene kanka ya cika da tuwon tsari da kunun ɗorawa sai baka taɓa tunanin abinda naje yi nan ba, baka ma taɓa tunanin ko ni macuci ne ba, a’a zan tafi ma roƙona kake na taimake ka, baka san cewa a ranar naga abinda nake so a gurinku amma nake ta ƙoƙarin kauda kwaɗayina saboda tun farko ba ni da niyyar cutarku. Gashi nake so mai gazar-gazar wanda yake baƙi siɗik da ratsin furfurar da bata fi uku ba a tsaitsaye tamkar an ƙona shi da soda, naga irinsa kuma akan Innarka a yayin da wata Nas ta zame ɗankwalinta a gabana. A saboda da gaske nake ban san cutarku  na so kauda kaina duk da kuwa wahalar da nasha wajen neman irinsa, Ni wanda nake jin zan iya cuta ma to mai kuɗi ne, ba talaka tiƙiss ɗan karkara irin ka ba, wai kasan ma me tsafinmu yake buƙata?kasan me ake so na kawo…?”

Ya yi shiru yana jijjiga kansa yana sakar masa murmushin ƙeta.

“…Da gaske nake da na ce zan taimakeka Innarka ta samu lafiya, da gaske kuma nake da nace kaima za ka taimakeni da abinda nake buƙata. Haka da gaske nake da na ce idan ka shiga ka shiga kenan fitarka daga nan tana cikin tafin hannuna sai kuma kayi mini abinda nake so tukunna. Ka riga da ka zama bawana dukkan ‘yancinka yana gare ni. Yanzu na karɓi abu guda ɗaya saura ɗayan, ɗayan kuma gashi can…”

Ya furta yana nuna masa wani farin mayani da aka yi kamar labule, a sannu labulen ya fara tattare kansa sai ga Innar Hameedu kwance samɓal saman wani gadon kara hancinta ɗauke da abin zuƙar numfashi, idan ba abin ka tsurawa ido ba kaga yana motsawa ba za ka taɓa zaton tana da sauran rai ba.

Hameedu ya yi wata irin zabura jikinsa ya fara kakkarwa tamkar zai tarwatse namansa ya yi sassa-sassa, ƙafafuwansa suka kasa ɗaukar nauyinsa haka ya tattaro sauran ƙarfinsa ya fara rarrafawa cikin rashin hayyaci dan ya isa ga Inna.

“…Yaro kasan aure ko? Nasan eh ne amsar dan na ganka zanƙalele a tashin ƙauyenku ma ƙila yaranka biyar ko? To kai idan ma baka san yadda ake bi a taki mace ba zan koya maka a yanzu yanzun  nan da nake so ka je ka haiƙewa Innarka ka gauraya mini mani ɗinka da nata zan ɗeba ayi mini aikin da idan na hau mulkin ƙasar nan sai na shekara takwas cur! Idan ma na nemi daɗi jiki na rawa waɗancan Dattijan za su ƙara mini shekarun, kana ji ko? To Maza kwaɓe wandonka ka haye samanta ka yi ta aikin da na saka ka, ta shirya tsaf ta yadda ba za ta taɓa sanin me ka yi ba, kaima an riga da angama shiryaka dan kuwa tuni an maka aski an wankeka tas! A tafkin jini. Kana gamawa ni kuma zan turaku Hindu ayi mata aikin da za ta samu lafiya, ba tare da na ƙara bayyana gare ku ba, ba kuma tare da hankulanku sun ƙara tashi ba, sai dai idan na hau mulki da kaina zan nemo ka na baka ministan noman rani, ai dai na yi, kasan shi ɗa nagari bashi taɓa manta alheri  bare ni da bansan baƙin mugun da ya yiwa tawa Innar cikina ta haifeni ba.

Da gaske ba zan taɓa mantaka ba Hameedu!”

Ya yi shiru yana duban saitin da Hameedu ya tsayar da rarrafan yana zuƙu numfashinsa da ƙyar yana fesarwa hannunsa dafe a saitin zuciyarsa.

Ya yi wani murmushin mugunta yana ƙarasawa gare shi ya ɗago shi sai dai yaraf ya sume masa a jiki.

<< Hakabiyya 16Hakabiyya 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×