Kallon ta yake yadda take shayar da jaririyar cikin farin ciki. Ya dubi jikinsa wanda awanni goma sha biyu da suka gabata yake a kalmashe. Ai sai ya ja guntulalliyar ƙafarsa ya yi sujjada ga Ubangiji Mai Girma a karo na uku. Ya ɗago ya ƙara kallon Zawwa da ke ta ƙoƙarin ganin jaririyarta na zuƙo ruwan nonon da ƙarfinta, sai abin ma ya ba shi dariya.
“Kai Zawwa! Allah shaidata ina matuƙar ƙaunarki.”Ta ɗago ta masa farr! Da Ido.
“Ka faɗa sau goma kenan daga buɗewar bakinka zuwa yanzu… ba wani nan ma. . .