“Na rage maka aikin, na bita a ɗazun har gidansu, sunanta Hamdiyya, gidansu na ƙofar Na’isa, mahaifiyarta ta rasu tun bayan gama primary dinta, tana tare da Babanta da wata tsohuwa da ban gane wace ba a zuri’arsu. Tana zuwa makarantar kwana, saura shekara ɗaya ta gama, yanzu Babanta ba shi da lafiya suna ta jele da shi wannan asibitin da ka je na Nassarawa. Sai me kake buƙata?”
Ya sauke hannunsa daga saitin zuciyarsa da ya dafe a tun lokacin da ya ce mamarta ta rasu, Ya sani ta tabbata marainiya kenan ba ma tada wanda. . .