Skip to content
Part 24 of 32 in the Series Hakabiyya by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

“Na rage maka aikin, na bita a ɗazun har gidansu, sunanta Hamdiyya, gidansu na ƙofar Na’isa, mahaifiyarta ta rasu tun bayan gama primary dinta, tana tare da Babanta da wata tsohuwa da ban gane wace ba a zuri’arsu. Tana zuwa makarantar kwana, saura shekara ɗaya ta gama, yanzu Babanta ba shi da lafiya suna ta jele da shi wannan asibitin da ka je na Nassarawa. Sai me kake buƙata?”

Ya sauke hannunsa daga saitin zuciyarsa da ya dafe a tun lokacin da ya ce mamarta ta rasu, Ya sani ta tabbata marainiya kenan ba ma tada wanda zai mata kuka a yayin da ya miƙa ta gasu Tunjim, sai ya ji abin kamar almara, ya daɗa tsinkewa da lamarin tabbas dole ya daɗa taka tsan-tsan da su, ga babban abin mamakin ma yadda aka yi shi Maɗacin y ya bishi Asibitin ba tare da ya kula da shi ba. Ya ƙuta yana kallonsa a kaikaice.

“Wai ni C.I.D na aka ce ka yi ko kula da Ni, su duk ganin nawa bai musu ba sai sun haɗa da kai?”

“Duka.”

Ya bashi amsa yana miƙewa.

“Duk sa’adda ka nemi ganin budurwar taka ka neme ni na rakaka taɗin.”

Yaja ƙaramin tsaki yana miƙewa shi ma.

“Yanzu da ka bibiye ni har can ai ba ni na neme ka ba, dan haka ban nema.”

Ya kwashe da dariya yana sa tafkeken hannunsa ya mari hancinsa da yake ji na masa ƙaiƙayi.

“Allah ya huci zuciyar Farfesa,ni kam bari na wuce.”

To shi ma murmushin ya yi jin sunan da ya kira shi da shi, tabbas da a ce zai samu kwanciyar hankali karatun zai yi har ya zama Farfesan, yanzu yasan dadin ilimi da tarin ma’anarsa cikin rayuwar bawa. Yana jin takaicin rashin ilimin da ya hana su sarrafa dukiyar da suka tsinta har ya sadaukarwa macuta, ji dai cikin watanni da basu fice bakwai ba ya samu wani irin buɗewar kwakwalwa da wayewar da baya tunanin za a sake masa wayo ko wani abu ya ruɗar shi. Da ace yanzu ne a guje za su fara amfani da ita, ya yi kuka na gaske a ranar da ya fahimci ashe sarƙa guda da ke cikin akwatin za ta warkar masa da Innarsa har ta yi rara, ya tsinewa su Alhaji Hashim ya kuma barsu da mahalliccin sammai-da ƙassai.

Tun daga ranar daga shi har Maɗacin suke bibiye da ita ba tare da itan ta sani ba, sai da ya gama fahimtar abubuwa da yawa na rayuwarta ciki harda burin auren kyakkyawan miji da suke fata Ita ƙawarta. 

A haka watarana ya bi ta cikin asibiti a lokacin an sake kwantar da Babanta ita ke cinjiyarsa. Shi da kansa ya tsaya a inda za ta ganshi da zarar ta fito har ta fito ta iso gabansa zuciyarsa ba ta bar bugawa ba. Shi ya yi saurin fara yi mata magana, nan fa suka fara hira yana ta cusa mata kansa, tun tana kunya har ta sake ita ma ta fara cusa masa nata kan, basu rabu ba ranar sai da kowa ya tabbatar da ya zauna cikin zuciyar ɗan uwansa. A washegarin ranar babanta ya ce ga garinku nan!

Daga sannan ta koma gurin Kawunta mai shegen tsauri, ya ci gaba da bibiyarta suka fara gabatar da wata zazzafar soyayya har tana zuwar masa a ɓoye, har ta koma makaranta ya ci gaba da ziyartar ta. Duk da ta faɗa masa wanda ake ƙoƙarin bata hakan bai sa ta fidda ran samunsa ba. Yana mata kyauta sosai musamman ta kuɗi sai dai ta ɓoye. Haka suka ci gaba da gabatar da soyayyarsu har tsayin shekara guda su Tunjim ba su ce masa ko tak! Ba kan lamarin. To fa zuwa sannan Hamdiyya ta zauna cikin rayuwarsa ta yadda ko a cikin barcinsa rabinsa da ita yake yi. Abubuwa da yawa ta masa da suka karyar da zuciyarsa kanta, sau ɗaya ta taɓa tambayarsa abinda yake yi a Kano ya ce mata aikin Banki ba ta sake tambaya, Haka garinsu tunda ta tambaye ya ce mata da nisa ba ta sake ba, to haka Innarsa tunda ya ce mata ba ta da lafiya kusan kullum sai ta ce ya kai ta ta ganta, ta kuma tambaye shi yadda take, har akwai sanda ta kwaso atamfofi guda biyu masu Fanteka ta bashi ya kaiwa Innarsa duk sa’adda za shi. Wani iri so take masa mai tsafta, son da ya tabbata ko dutse ake yiwa shi sai ya girgiza. Ya ji fa gabaɗaya shi ba zai iya sayar da ranta ga su Tunjim ba dole a nemi wata mafitar wacce babu fidda rai. 

A ɗan tsakannin da yake jin wannan damuwar kiran Tunjim ya iso masa. Ya je ya bashi ƙyallen da zai bata ta yi ƙunzugu da shi ta zo nan ba tare da tasan shi Huzaif dinne ya kawo ta ba. To anan fa ya daure ya fara neman alfarmar da ta fusata Tunjim ya aje masa garwashi gabansa ya gasa fuskarsa da azabar wannan garwashin.

Hakan bai sa ya haƙura da maganar sai da ya sake maimai tata cikin azabar da yake ji ya ce masa.

“Ka duba dai alfarmar dan Allah ku duba, yadda kuka ce na yiwa Innata sai na yiwa ita Hamdiyyar ta yi tafiyarta Ni ma na kama gabana, ba dai lefi kuke so na yi ba, na yarda na aikata zina akan kisan rai.”

“Duk ɗaya ai, wai mamaci ya karye.”

Alhaji Hashim da shigowarsa kenan ya furta yana fashe masa da dariya.

Bai ko dube shi ba ya ci gaba da zuba masa magiya suka yi biris da shi, har dai can Tunjim ya ɗaga masa hannu alamun ya tashi ya tafi.

Haka ya dawo gida zuwa yammacin ranar ya je suka haɗu da Hamdiyyar inda suke yawan haɗuwa, sai dai har ya rakata layinsu ta shige gida ya gaza bata ƙyallen da ke cikin aljihunsa. A ranar ne kuma Kawunta ya gane tana kula shi ya fusata ya tsaida aurenta da Yayanta. Har zuwa sa’adda ta zo nemansa cikin unguwarsu ya kuma ganta tun a farkon shigowarta layin. Yana sane da yadda kowa ke ce mata basu san wani baƙo Huzaif ba kasancewar ya kusa shekaru biyu unguwar haka da Hameedu suka san shi, daga Maɗaci sai malaminsa ke kiransa Huzaif, har ya gama zama cikin gidan tana bulayi cikin unguwar tana nemansa, zuwa sannan ya fara shakkar neman ba na lafiya ba ne, a sannan  ya fito tamkar yana shirin fita ta hango shi ta taho.

A rannan ya bata ƙyallen bayan ya zuga mata ƙaryar da ya san za ta tsoratata ta kasa amfani da shi ta kore shi daga rayuwarta gabaɗaya. Sai dai abu guda cikin abubuwan da ta yi kansa wanda baya taɓa mantawa shi ne karɓar ƙyallen da ta yi ta tafi duk kuwa girman tsoron da ya gani cikin idanuwanta. A rannan ya tsinke da lamarinta musamman da ya tuna wai zuwa ta yi ta bashi shawarar ya gudu da ita kar ta auri ɗan uwanta da yana da tabbacin ya fishi daraja da tsarki har gurin Allah. Haka ya kwana yana addu’ar kar ta yi amfani da ƙyallen, yana roƙan Allah ya bata hikimar da za ta fahimci sharrin da ke tattare da shi.

Tsawon kwana shida ya yi cikin wani irin tashin hankali da tsoron da baya fatar maimaituwarsa har ƙarshen rayuwarsa. A ranar ne ya ji kiran Tunjim ya je ya tadda rago maimakon Hamdiyya. Ya saurari faɗan Tunjim ya kuma sake roƙarsa kan alfarmar da ya nema da daɗadan kalamansa sai dai ya ƙi saurararsa.

Haka ya dawo zuciyarsa da gangar jikinsa na bashi shawarar ya je yaga Hamdiyya sai dai wani tsoro mai girma na hana shi. Har zuwa bayan kwana biyu sa’adda ya sake jin kira ya tashi ya tafi gare shi.

BIYU BABU! IDAN AJALI YA YI KIRA…

“Za a sake yi maka alfarma ba tare da neman wani abu mai girma daga gareka ba, sai dai ka sani idan har kuskure ya ratsa wannan kai za ka ɗauki responsiblity ɗinsa.”

Ya yi shiru yana tasowa daga kujerar da yake zaune ya zo ya tsaya gaban Huzaif da ke zugunne a ƙasa.

“A yanzu haka yarinyar bata Kano, Kawunta ya ɗauketa zuwa kaduna don ya nesanta tsakaninku. Ka jira zuwa wani ɗan lokaci sai ka bi bayanta can ɗin, ka sake hilatarta na sani ba abu ne da zai baka wahala ba, ka ɗauke ta akwai wani gida za zan baka mukullinsa, ka yi amfani da ita a cikin gidan ka ɗibar mana abinda muke so jikinta har na tsawon wata uku. Ina nufin a kowane wata sau ɗaya za ka take ta har cikar watanni ukun, daga nan za ka kawo mini ita nan zan ɗebi jininta da bai gaza ƙaramin sirinji uku ba.  akwai kwayar da zan baka ka dinga bata domin ta gusar mata da hankali ta yadda ba za ta taɓa fahimtar ka take ta ba ko da kuwa a cikin  jikinta ne. Haka ga duk mutanen da za su kawo maka matsala a rayuwarku ta can kar ka damu da su ni zan yi maganin abin daga nan.”

Hameedu ya sauke ajiyar zuciya yana jin relief cikin ransa, sai ya ji kamar har anyi an gama shi ya kama gabansa ita ma ta kama nata. Ya ɗago da zummar yi masa godiya sai yaga yana wani irin murmushi suna haɗa ido ya tuntsire masa da dariya yana duƙo da fuskarsa daidai saitin Hameed, wani wari da ƙarni da ya buge shi, shi ya saka shi haɗiye wani mugun yawu ba tare da ya shirya ba, ya sani idan ba mugunta ba babu  abinda ke sa Tunjim kyakyata dariya irin haka.

“Kasan menene ladan wannan sassaucin dana maka…?”

Bai jira amsar sa ba ya ɗora.

“Kwayoyin haihuwarka da zan yi amfani da su na ƙarawa kaina ƙarfi da lafiya, da kuma irin ciwona da zan zuba cikin jikinka wanda hatta a gumi ana iya ɗaukarsa. Yanzu ka zaɓi ka dawwama ba haihuwa akan ka bamu ita mu kashe?”

Ya dube shi ido cikin ido yana jin murnarsa na komawa can cikin cikin shi, sai kuma ya tuna Huzaif , ya tuna idan shi ba zai haihu ba yayansa ai ya haifa masa shi, haka idan da yawan rai shi kan shi Huzaif ɗin zai kawo masa ‘ya’ya.

“Kar ka yi wani dogon tunani kawai e ko a’a? Kodayake da kasan matsalar da nake gudar maka da baka tsaya tunani ba, bana so rabo ya ratsa tsakaninku duk da ban ga kome ba sai dai babu alheri a ciki, zai iya zame maka bala’in da ni kaina bansan ƙarshensa ba. Ka sani kuskure ɗaya da za ka yi a tafiyar nan zai iya tarwatsaka ya tarwatsa dukkan lamuranmu. Dan haka ka kiyaye, ka kuma gode mini da zan raba ka da abinda zai sa rabo ya ratsa. Tashi ka tafi.”

Ya miƙe akan duga-dugansa da yake ji tamkar an sa guduma an bubbuge su, sai dai taku uku ya yi ya nuna shi da sandar hannunsa, yaji ya tsaya ƙyam tamkar sassaƙaƙƙen gunki, kome na halittarsa ya daina motsi har ya tako gabansa ya tsaya ya jefa masa wani kyakkyawan zobe cikin aljihun gaban rigarsa.

<< Hakabiyya 23Hakabiyya 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.