Ba na jin akwai azabar da za ta wanzu a rayuwata da zan ji tashin hankali ya same ni ko fargaba in dai har ina tare da kai. Ina nan akan bakana Huzaif ka zo mu gudu, ka kalli goshinka fa na tabbata sune suka ji maka ciwo.
Tamkar busar sarewa haka ya ji zantukan na wucewa cikin kunnensa, ya lumshe idanuwansa yana jan bargo ya lulluɓe jikinsa jin sanyin A.C na ratsa ɓargonsa, ya tuna fuskarta da murmushinta da tarin soyayyar da take masa sai ya ji kamar shi kaɗai asara ta tabbata cikin. . .