Skip to content
Part 26 of 32 in the Series Hakabiyya by Fulani Bingel

Ba na jin akwai azabar da za ta wanzu a rayuwata da zan ji tashin hankali ya same ni ko fargaba in dai har ina tare da kai. Ina nan akan bakana Huzaif ka zo mu gudu, ka kalli goshinka fa na tabbata sune suka ji maka ciwo.

Tamkar busar sarewa haka ya ji zantukan na wucewa cikin kunnensa, ya lumshe idanuwansa yana jan bargo ya lulluɓe jikinsa jin sanyin A.C na ratsa ɓargonsa, ya tuna fuskarta da murmushinta da tarin soyayyar da take masa sai ya ji kamar shi kaɗai asara ta tabbata cikin rayuwarsa. Kwana bakwai kenan da mutuwarta yana jin zantukanta na ratsa kunnuwansa, bai mantata ba ko na sakanni, to ya ma za ai ya manta alhalin ko’ina ka shiga cikin Nijeriya takarar Alhaji Hashim kawai ake magana, wanda da jinin Haƙabiyya ya same shi. Ya nisa a bayan ya roka musu tsinuwar Allah, sai kuma ya jawo Huzaif da ke kwance gefensa ya rungume cikin ƙirjinsa, ya yi tsai yana kallon kyakkyawar fuskar yaron yana rasa abinda ke hana shi jindaɗi a yanzu da ba shi da damuwar kowa, ga Innarsa cikin ƙoshin lafiya, ga Huzaifunsa ga kuma tarin dukiyar da Alhaji Hashim ya ba shi a cikin zinarin Bawa, to me ya sa yake jin zuciyarsa cikin ƙunci a duk ranakun nan? Ɗan ƙaramin tsaki yaja yana miƙa hannunsa ya kashe bedlamp ɗin gefensa.

Washegari da wuri ya tashi ya shiga kitchen ya tsiyaya fresh milk a ‘yar butar silver, ya jefa mata kanunfari ya juye a glass cup ya yi ɗakin Innarsa da madarar, so yake ya mata maganar tafiyarsa italy da sabon Abokinsa da ya yi Alhaji Bilya mai harkar fata daga Italy zuwa Libya zuwa Naija. A yanzun zai je ne ya fara ganin yadda harkar take shi ma ya tsunduma ciki. 

Da sassafar yake takun ƙafafuwansa na lumewa cikin ƙayataccen kilishin da ke falon, har ya isa ƙofar ɗakin ya yi sallama, jin bata amsa ba yasa ya buɗe ƙofar ya shiga, idanuwansa ne suka fara ƙara girma kafin cup ɗin hannunsa ya suɓuce ya faɗo a dandaryar tayil din wurin ya tarwatse, takan gwalaben ya taka a guje ya yi kan Innarsa da ke malale a ƙofar toilet ɗin ɗakin hannunta dafe a saitin zuciyarta, ɗago kanta ya yi zuwa cinyarsa yana kiran sunanta yana jin tashin hankulsn duniya na kusanto hancinsa, a sannan ta buɗe idanuwanta da ƙyar ta masa murmushi, sai kuma ta maida idon suka rufe ruf! Rufewa ta har abada! Akan idonsa ta yi mutuwar da bai isa ya hana ba, ba Hamdiyya da ɗan cikinsa zai bayar ba, ko kansa zai bayar da Huzaifu da Babansa da Yayansa basu isa su hanata amsa kiran mahaliccinta ba!

BAYA KAƊAN…

    Washegari ta tashi a kasalance ga gabanta da ke yawan faɗuwa akai-akai,  haka nan ta yi dukkan abinda za ta yi ta gama zuwa ƙarfe 10:00 za ta raka su Zawwa asibiti a yiwa tsoho Bawa general test, sun gama shiri tsaf sun fito harabar gidan suna jiran Baba Direba ya gyara paking, maigadi har ya wangale gate, hannunta na cikin na tsoho Bawa da ke zaune saman kujerarsa ta guragu, a lokacin da ta fara tura keken ne dan su ƙarasa jikin motar hancin wata baƙar mota ya sanyo kai cikin gidan, gabaɗaya suka bi motar da kallo a yayin da cikin Haƙabiyya ya bada wani irin sauti a sa’ilin da taga Huzaif ya fito daga motar Babansa ya biyo shi daga baya. Ta zabura za ta saki hannun Babanta ta ji ya riƙe ta ƙam, tabi  hannun da kallo da kallo taga hannunsa na kakkarwa haka bakinsa na rawa yana nuna Abban Huzaif. Ta kai kallonta ga Zawwa da ta kula ta ƙame ƙam bakinta a buɗe, ita maida kan Abban Huzaif da shi ma ya yi tsaye yana kallonsu idanuwansa na fidda kwallar da bata san dalili ba. A sannan ne kunnuwanta suka zuƙo mata muryar Baba na Kiran sunan Hameedu, ta waiwaiya a zabure taga wanda aka kira da Hameedun ya taho da sauri ya ture ta ya duƙa ya ƙanƙame Babanta yana hawaye.

Mararta ta tamke tam! Cikin firgici ta ɗaga ƙafarta da azama za ta bar gurin Zawwa ta yi caraf t riƙe mata hannu tana girgiza mata kai.

“Abokin Babanki ne Hameedu Siddiqu, maza buɗe musu sitting room ɗin Babanki, ki nutsu kuma!”

Ta furta mata tana mai juyawa ta dubi Hameedun da ke durƙushe gaban mijinta da ya nakasta. Wata sabuwar wutar tsanarsa ta sake ninkuwa a cikin zuciyarta. Ta kalli motar da ya shigo da ita ta kalli suturar da yake sanye da ita. Ai kawai sai ta ɗaga ƙafa  a kan takunta mai ƙarfi bayan ta saki siririn tsaki ta bar musu gurin.

Huzaif da ke gefe yana la’akari da ita ya bita da kallo yana jinjina inda Haƙabiyya ta gado tsiwa. Sai kuma ya matsa zuwa inda mahaifinsa yake yana saurararsu.

“Ka bar kukan nan haka Hamidu, zuciyata bata taɓa ƙullatarka ba, Allah shaidata ni zan bada labarin nagartarka, na bar kome a ƙaddararmu, na bar kome a bai faru ba, kawai dai na ji ciwon da ba ka sake nema na ba. Haba Hameedu idan na yi fushi da kai a kan dukiya ai ban cika mutum ba, abu ne fa da dukkanmu nan za mu tafi mu barta.”

Haƙabiyya ta tafi da sauri ta buɗe sittin room din ta dawo ta fara tura keken Babanta zuwa cikin ɗakin, ganin haka Huzaif ma ya riƙo babansa  suka yi cikin ɗakin.

Yana shiga ya zare hannunsa yana ƙara zurfin kukansa, ya duƙa sosai gaban Bawa yana mai haɗe tafukan hannayensa.

“Ka yafe mini Bawa, domin mahallicinmu ka yafe mini, tabbas naso zuciyata, na so kaina a lokacin da bai kamace ni ba, na ha’inceka irin ha’aintar da ban taɓa yafewa kaina ba. Duk wata walwalar rayuwa ina yi ne kawai ba tare da nasan daɗin hakan ba, banda sukuni Ko misqala zarratin tsawon shekarun nan Bawa ban huta ba gurin nemanka, ko wannan yaron shaida ne a saboda ban same ku ba duka farin cikin rayuwata ya tsaya cak! Ka ga yarinyar da ta yi silar zuwana nan ba tare da na san kai ne mahaifinta ba.”

Ya furta yana nuna saitin da Haƙabiyya ke tsaye tana kwalala ido, shi da Bawan suka nisa suna hango mafarin kome cikin idanuwansu.

*** ***

DAWOWA CIKIN LABARI.

Tsoho Bawa nisa yana sauke ajiyar zuciya, ya dubi Alhaji Hameed da har yanzu ke duƙe gabansa tafukan hannayensa a haɗe, a hankali ya miƙa hannunsa ya riƙo nasa, “ka tashi Hameedu ban cancanci ka duƙa mini har haka ba, menene ka mini da har za ka tafiyar da rayuwarka cikin ƙunci? Kar ka manta kowane bawa fa da irin kuskurensa, ni wallahi tun a lokacin na yafe maka, ban riƙe da kome ba sai jin ciwon rashin ganinka cikin rayuwarmu, ina Inna?”

Sautin kukansa ya daɗa ƙarfi, ya yi zaman dirshan yana ƙara ƙanƙame hannun Bawan cikin nasa hannun. Ya buɗe baki zai yi magana ya ji wani abu ya riƙe masa ƙirji, sai kawai ya ɗora kansa kan hannunsu da ke haɗe, a cikin idanuwansa da ke rintse ya tuno ranar da aka fidda gawarta waje, jama’ar unguwar suka mata sallah, daga sannan bai sake sanin inda kansa yake ba sai bayan kwana biyu da ya farfaɗo ya ganshi a gadon asibiti ana masa ƙarin ruwa da na jini. Daga nan ya tsani Nijeriyar da abinda ke cikinta gabaɗaya, saboda hakan ya ɗau Huzaif ya bi bayan sabon Abokinsa Alhaji Bilya zuwa Italy bayan ya saida gidansa na Abuja, a can ya sai fatu masu yawan gaske da dukiyar da Ale Hashimu ya ba shi, ya cika container goma sha biyar ya danƙa ma Alhaji Bilya amana, shi kuma ya share guri ya zauna a matsayin gwauro wanda duk haɗuwar mace bata daɗawa da ƙasa ko kaɗan, wani abokin Alhaji Bilya ɗan ƙasa ya masa cuku-cukun shiga wata makaranta ya saka Huzaif ma, ya samu wata tsohuwa ya aje ta gidan da ya kama tana rage masa ɗawainiya duk da sau tari shi ke kula da Huzaifun har kuwa wankansa, nan ya ci gaba da harkokinsa ta hanyar Bilya cikin ikon Allah bai samu matsala ko ta kwabo da shi ba. Bayan shekaru biyu ne ya dawo 9ja inda ya nemi Maɗaci ya kashe wasu lamura da su ya koma italin, daga nan bai sake dawowa ba sai bayan gama secondryn Huzaif, anan ya gina musu gida guda biyu a unguwa guda, ya danƙa ma yaron nasa shi ma ya zauna a nasa, daga nan suka ci gaba da zamansu yana ci gaba da bunƙasa kasuwancinsa.

Ya nisa yana ɗagowa ya kalli idanuwan Bawa da ke ta kallonsa, “Inna ta mutu, ta mutu tunda daɗewa Bawa.”

Bawan ya yi shiru yana jin bugun da lamarin ya masa, duk da dama yasan hakan za ta faru, sai dai fa ita mutuwa a kullum haka take ga bawa, ba ka taɓa sabawa da jinta.

“Allah ya ji ƙanta ya mata rahma, ya ƙarama juriyar rashinta.”

“Amin na gode, amma Bawa ba za ka tambaye ni ba?”

“Me fa Hameedu?”

Ya yi shiru yana jin nauyin maganar na sarƙe masa harshe.

“Abinda ya sa na ɗauke dukiyarka da abinda yasa ka rasa ƙaf…”

“A’a dan Allah kar ka ƙara sa, ba na saka rasa ƙafata a dalilinka, ka sani banda Allah babu mai wannan ikon, na kuma yi godiya gare shi tunda gani cikin aminci da lafiyata.”

“Ni ne fa sila, wallahi ni ne!”

“Na ji fa, ai ka bar saƙo kan hakan, abu ɗaya na sani ba za ka taɓa aikata hakan gare ni da nufin mugunta ba sai dai da wata sigar wacce ba na buƙatar ji, na fahimce ka har cikin raina Hameedu, ina roƙonka da Allah ka manta dukkan abinda yawuce.”

Hameedun kawai sai ya saki baki yana kallonsa da wani irin mamaki, bai taɓa zaton har haka kyawun zuciyar Bawa take ba, sai ya ji yana daɗa Allah wadai da nasa halin, har ransa ya sani da ace Bawa ne a madadinsa, da babu abinda zai sa nasa sunan ya fito cikin lamarin.

Sai ya nisa kawai yana rasa me zai ce, har Haƙabiyya da ta daɗe da barin falon ta sake shigowa hannunta ɗauke da babban tire ta aje a gefensu, ya bita da kallo ta wutsiyar ido sai kumbura take kamar za ta fashe, ya yi murmushi cikin ransa yana rasa inda zai aje ƙaunarta da ke motsa masa a kowacce thaniya, bai san yarinyar za ta zame masa farin gani, farin alheri ba sai yanzu da ya ta yi silar sada shi da amininshi ya sauke babban nauyin da yake kansa, sai yake jin kansa tamkar saurayin da ya fara shiga farkon shekarar balagarsa, ya sauke ajiyar zuciya yana maida hankalinsa kan Bawa da ke ta kallonsa, suka haɗa ido Bawan ya masa murmushi, sai ya ji kuma kunya ta kama shi, ya dan kai hannu ya sosa goshinsa yana jin kamar ya buɗe ido ya ganshi kusa da ita suna hira, sai kuma ya tuna kuskurensa ya tuna zuciyar mata, ko Bawan ya yafe ba lalle it yarinyar ta iya yafe masa silar nakasta ubanta da ya yi ba.

Tiren gabansa ya jawo ya hau bubbuɗewa yana son kauda tunanin da yake yi.

“Na ji ka ce Haƙabiyya ta yi silar zuwanka nan? A ina kuka haɗu ne.”

Ya tsinca yi muryar Bawan cikin kunnuwansa. Sai ya tsaya da bubbuɗe kwanukan da yake yi yana jin daɗin tambayar na ratsa shi.

“A hanya, alheri ya haɗa mu shi ne na biyo ta har gida, ɗalibar yaronka Huzaif ce.”

Ya yi shiru yana jin wani nauyin Bawan na daɗa kama shi.

Bawan da ya fahimci lamarin sai kawai ya girgiza kai yana tuna maganar Zawwa game da Hameedun, bai so hakan ba, bai so tun ba aje ko’ina ba Hameedun ya fara nuna ƙaunarsa ga ɗiyar tata, sai yake ganin abin kamar almara, kamar tabbatuwar fatan Zawwa ke bayyana.

“To ina iyali?”

“Babu, ban taɓa yi ba, sai yanzu dai ake niyya…”

Ya furta da yanayin da yasa Bawan kame bakinsa daga maganar, duk da yaso ya ji abinda ya saka shi zama haka ba aure, sai dai daga yanayin Hameedun ya fahimci ba abune mai daɗi ba, dan haka ya shashantar da zancen ta hanyar yin dariya.

“Ka ji zance na ko? Dama na faɗa maka sai Zawwa ta haifi ɗiya har ta girma sannan ka auri ɗiyar, ai shi kenan, alƙawari na na biyan sadakinka da sisin gwal na nan fa. Ni Allah yasa shi Huzaif ɗin bai yi auren ya barka ba, ina kake ne Huzaifu matso mu gaisa mana…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Hakabiyya 25Hakabiyya 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×