Suna nan suna zolayar juna har ɗan aiken ya dawo, nan ya faɗa musu ta shigo makarantar amma har ta fita, sai dai ya tambayi wasu sunce masa sun ganta da wani Malami Huzaif, sun fita tare a motarsa.
Nan Alhaji Bilya ya yi ta tsokanarsa da cewar sai ya je gida ya kwanta ya jira gobe kuma, daga nan tare suka fito kowa a motarsa kafin su rabu a babban titi.
Kai tsaye gida yayo yana ta tunanin inda Huzaif ya tafi da Amaryar tasa, can kuma ya tuna ai ƙofar gidan yaron ya fara ganinta ta yiwu. . .