Skip to content
Part 29 of 32 in the Series Hakabiyya by Fulani Bingel

Suna nan suna zolayar juna har ɗan aiken ya dawo, nan ya faɗa musu ta shigo makarantar amma har ta fita, sai dai ya tambayi wasu sunce masa sun ganta da wani Malami Huzaif, sun fita tare a motarsa.

Nan Alhaji Bilya ya yi ta tsokanarsa da cewar sai ya je gida ya kwanta ya jira gobe kuma, daga nan tare suka fito kowa a motarsa kafin su rabu a babban titi.

Kai tsaye gida yayo yana ta tunanin inda Huzaif ya tafi da Amaryar tasa, can kuma ya tuna ai ƙofar gidan yaron ya fara ganinta ta yiwu yanzun ma tana can, sai kawai ya bawa direbansa umarnin idan ya shiga unguwar tasu ya yi gidan Huzaif ɗin kai tsaye.

*****

Tunda ta lallaɓa ta fice ba tare da sanin Mami ba, sai ta yi wucewarta Makarantar ta samu lecture dake gare ta lokacin. Anan ta bawa Hanifa labarin mijin da aka mata da kasancewarsa Baba ga Sir Huzaif sai bata faɗa mata ƙudurin Mami na son auren ba. Hanifar ta yi ta jujjuya lamarin kafin ta hau bata shawarar kada ta sake ta yadda, ta yi duk yadda za ta yi ta karkato hankalin Huzaif kanta ya ji zai iya saɓawa baban nasa saboda ita. Haƙabiyyar ta zaro ido jin shawarar tata, ta ce “ baki da hankali, kin manta daɗewar da na yi kafin shi din ya fara kulani, wannan ba shawara ba ce kawo wata.”

“To ki gwada yiwa abokin Baba kora da hali mana.”

“Ba zai gane ba, na faɗa miki har dubansa na yi na ce ba na sonsa ya tsaya yana mini murmushi mai kamar an shaƙe fatalwa.”

“Ke dillah ba haka ba, yanzu yawa ne duban saurayi ka ce baka so saboda rashin sanin inda rana za ta faɗi, kora da hali zaki yi ta yi masa har ya gane ya tafi dan kansa, kinsan ma ta yaya? Ki dage da zuwa gidan ɗan nasa shi kuma yana ganinku tare, ke kiyi ƙoƙari ma ki sato mukullin gidansa yadda kai tsaye za ki dinga afka masa gida.”

“Kai Hanifa ina tsoro, kar ya min kallon yar iska.”

“Ba zai miki ba, ai ya riga ya sanki ciki da bai.”

“Cikin dai banda bai ɗin, tunda dai ba taɓa kwaɓewa na yi gabansa ba.”

Suka yi dariya a tare, irin dariyar da ta kwan biyu bata yi ta ba.

“To yanzu ya za a yi?”

“Yauwa, yanzu kije ofice ɗinsu sir Huzaif, kina shiga sai ki yi kamar kin faɗi, ki fara kuka sosai har ya kula ki, daga nan sai kisan ƙaryar da za ki masa har ya yadda ki bishi gidan, kar ki sake ki baro gidan sai Babansa ya ganki a can ɗin.”

Daɗi ya cikata tana jin idea ta mata %, sai ta shafa kunnenta tana cije gefen bakinta, sai Kuma ta miƙe da sauri tana zarar jakarta, bari to na je, kalli na yi kyau sosai ko?”

Hanifar ta ɗaga mata kai kawai tana dariya.

Tana tafe tana addu’ar Allah Yasa shi kaɗai ne office din, tana bude ƙofar ta kuwa yi sa’ar shi kaɗai dinne, yana zaune yana aikin harhaɗa wasu takardu, sau ta yi tsai tana duban yadda ya yi wani fresh, babu wata alamar damuwa tatare da shi.

“Sir…”

Ta furta a hankali, ya ɗago ya kalleta, sai ya fadada fara’ar fuskarsa.

“Matar Baba ya aka yi ne?”

Ta tsuke fuska tana shigowa cikin office din sosai, “Sir rannan na yada ɗankunnena a ƙofar gidanka,”

“Ya akai kika san acan ya faɗi?”

Ya furta yana canja yanayin fuskarsa.

“Saboda har na je ƙofar gidan yana kunnena, ɗan kunnen mai daraja ne ka taimaka kai ni can na duba ko zan ganshi,”

Sai kuma ta yi kamar ta gurɗe, ta kuwa idasa kifewa gabaɗaya ƙasan gurin tana furta wash Allah.”

“Aa hankali mana, ya kike faɗuwa ne?”

Ya yi shiru yana kallon yadda take ƙoƙarin miƙewa. Ya kaɗa kai ya ce,

“Da gaske kike kin yada ɗan kunnenki a can?”

Ta marairaice fuska ta ce, “Allah da gaske nake, na rantse a ƙofar gidanka ya faɗi, kuma ɗan kunnen na gado ne, Maman Mami ta bata, ita kuma ta ba ni shi, na rantse idan Mami ta gane baya nan ba abinda zai hanata karairaya ƙasusuwan jikina.”

Sai ta hau sharar kwalla.

“Ya furzar da iskar bakinsa yana nazarinta a kaikaice, sai kuma ya zari mukullin motarsa ya miƙe, “muje ƙofar gidan na gani, idan kuma na tarar ƙarya kike ba abinda zai hanani kakkaryaki na zubar gurin.”

“Kai ka isa ka karya matar da kake kira ta Babanka?”

Ta furta da gunguni.

“Me kika ce?”

“Ni fa bance kome ba Allah”.

Ya kaɗa kai ya yi gaba. Ita kuma ta hau cije baki tana dafe baki da yarfe hannu.

Ya yi kamar ya riƙe ta sai kuma ya basar ya wuce ta da sauri.

Ita kuma ta hau ɗingishi har ta isa ga motar ta buɗe ta shiga, ya tada ya fice daga makaranta.

Sun ɗan yi tafiya mai yawa kafin ya waiwaiya ya kalleta ganin yadda ta yi rashe-rashe cikin motar kamar ba ita yanzu ke kukan ciwo ba, sai ya girgiza kai kawai ya maida hankalinsa kan tuƙinsa. Ita ma juya Idanuwanta ta yi tana godewa shawarar Hanifa cikin ranta. Tasan badan ita ba da yanzu ba ta tare da shi cikin mota guda. Tana ta ‘yan tunane-tunanenta ta ji ya yi parking, ta kalli wajen taga a ƙofar gidan nasa suke, sai kawai ta hau murmushi.

Ya tamke fuska yana harararta ya ce, “to munzo, maza fito ki dudduba ɗan kunnen naki, naga yadda za a yi ki ga abinda ya faɗi kwana da kwanaki anan.” Ta fito ta hau dube-dube a ilahirin wajen kamar me neman abu, sai ya tsurawa ƙafarta ido yaga yanzu babu ɗingishin, ya kalli fuskarta yaga sai murmushi-murmushi take, sai kawai ya fisgota yana wara idanuwansa a kanta.

“Ƙarya ko?”

Ta kwakkwaɓe fuskarta, ta buɗe baki kamar za ta yi magana sai ta cije bakin tana runtse ido ta ce, “wayyo Allah cikina, wayyo sir marata, washhhh! 

Ya Allah!”

Sai ya yi baya a dan firgice yana ganin yadda take hawaye.

“Lafiya wai, me ya samu cikin ne, ko muje asibiti ne?”

Ta daɗa cije baki tana ƙaƙalo hawayenta da ke neman kafewa.

“No sir toilet nake so, ina tunanin romon da na sha ɗazu ya hargitsa mini cikin.” 

Ta furta tana cije baki tana yarfe hannu.

Ya narke fuska cike da tausayi ya riƙo hannunta, “sannu, muje ciki akwai toilet sai ki shiga, za ki iya tafiya?”

Ta gyaɗa kai tana matse hannunsa da ya riƙe ta gudun kar ya cika ta. Da haka ya buɗe gate din suka yi cikin gidan.

Suna shiga ya kaita har bakin toilet ya juyo, ita kuma ta shige ciki ta tsaya a gaban mudubin saman sink tana kallon kanta, ta kunna famfo ta fashe da dariya harda riƙe ciki, sai da ta yi mai isarta ta hau gyaggyara kanta, harda fesa wani turare da ta gani gurin ta lumshe ido tana jin kome nata ya kama ƙamshin Huzaif, sai ta fito ta tsaya a ƙofar toilet ɗin tana ƙare masa kallo, ta kuwa buga wani uban tsalla tana tafi,”wow! Wow! Sir ka gama kashe ni, amma dai idan muka yi aure anan za mu zauna ko? Kasan ba kalar fentin da nake so a rayuwata irin wannan fari da ratsin blue black ɗin. Wai ya akai kasan haka zaɓina yake?”

Ta furta tana ƙarasawa kujerar da yake zaune.

Ya ɓalla mata harara bayan ya miƙe tsaye.

“Ina duk ciwukan da kika ce kina ji, dama ƙarya kike ko?”

Ta narke fuska tana dubansa a marairaice.

“To mene dan masoyi ya yiwa masoyinsa ƙarya, ya kuma kake so na yi da sonka da ke sakani yin ƙaryar, kana fa sane ka fara toshe duk wata hanyar da kasan zan maka magana, ɗazun sau nawa na kira ka ka ƙi ɗagawa, ni bazan iya ba, da gaske bazan iya ba Huzaif, ka dinga tuna yadda shi mahaifin naka yake ji a kaina, ina jin fiye da hakan a kanka, wane irin son kai ne irin haka kake yiwu rayuwarmu wai?.”

Ta ƙarasa tana jin kwallar gaske na taruwa cikin idonta.

“Rayuwarki dai, ki kuma gaggauta barin gidan nan, ki bari dai zuwa dare zan kira ki.”

Ya furta a natse, sai kuma ya yi gaba zai buɗe mata ƙofar, ta yi azamar riƙo hannunsa, ta dube shi da murmushin ƙauna ta ce, “bazan tafi ba har sai ka…” Daidai nan ƙofar falon ta buɗe sai gashi ya faɗo ciki, idanuwansa suka sauka kan hannunsu dake haɗe, su ma suka bi hannun nasu da yake kallo da ido, Huzaif ya fara ƙoƙarin zare nasa ta kuwa daɗa ƙanƙame hannun tana turo baki gaba.

“A’a Baby Sarauniya ashe kina nan, dama tunda na ji zuciyata na raya mini haka nasan ba za ta yi ƙarya ba.”

Ya furta yana takowa da azama zuwa gare su, ba su yi aune ba sai ganinsa suka yi a tsakiyarsu ya saka hannunsa ya raba nasu da ke haɗe. Suka dubi juna a tare kafin su maida kallonsu kansa, ya wangale musu fararen haƙoransa har sannan yana riƙe da hannunsu sun saka shi a tsakiya. Haƙabiyya ta warce nata hannun tana sunkutar jakarta da ke bisa kujera ta yi gaba, sai shi ma ya cika hannun Huzaif ya rufa mata baya yana faɗin “Baby Sarauniya tsayani na mayarki gida, kai Huzaifu har kun gama karatun kenan?” Bai jira amsar sa ba ya fice daga falon.

Huzaif ɗin ya zauna a kujera yana riƙe kansa da yaji yana sara masa, sai kuma ya dubi hannunsa da Alhajinsa ya raba da na Haƙabiyya, ya ji ransa ba daɗi, a karon farko da ya ji haushin Babansa na tsungulinsa, sai kuma ya yi istigfari ya miƙe yana dukan goshinsa dan ya bar  tunani irin haka, ya buɗe ɗakinsa ya faɗa bisa gadonsa yana jin kamar ya aikata wani zubi babba.

“Ba zan bika ba, nasan hanyar gidanmu, ba na bukatar rakiyar.”

Abinda ta furta masa kenan bayan ya cimmata, sai ya tsaya yana kallonta galala kalar tsiwarta na kashe shi,

Ta yi ƙaramin tsoki tana tafiya, sai kuma ta dakata ta waigo tana kallonsa idanuwanta na cike da tsantsan tsana.

“Ka daina shisshige mini tunda na faɗa maka ba na ƙaunarka akwai wanda nake so, kar kasa wataran na maka abinda gaba zan zo ina nadama, kuma ka je ka yi tunanin abinda ya kawo ni gidan ɗanka yanzu.”

Sai ta yi gaba tana goge fuskarta tana rasa abinda za ta yi taji daɗin ranta, har ta samu mai taxi ta shiga.

Cikin haushi ta zaro wayarta ta dokawa Hanifa kira, tana ɗagawa ta ce” to kora da halin bai yi ba, na faɗa miki dama ɗamsul basiratu ne, sai ki canja wani tsarin. Amma ga mukullin a hannuna, ni duka na dauko sai dai ya yanko wani kuma” Kafin Hanifar ta yi magana ta kashe wayar ta jefa ta cikin jaka.

“Ka kalli gabanka, dan wallahi ka kashe ni bayan diyya sai ka yi zaman prison.”

Ta furtawa mai taxin bayan ta doka masa uwar harara kamar shi ya kar zomon.

“Wai laifi ne dan an mini kyauta na karɓa ko kuwa dan kyautar ta fito daga hannun da kika tsana? Zawwa, ina fa rabaki da wannan zazzafar ƙiyayyar marar dalili, wane irin abu ne haka za ki wani dangwarar da abu ba ko na gode ki yi tafiyarki, kika sa na ji kamar na nutse a gurin tsabar kunyarsa da na ji..”

“Marar dalili? Marar dalili fa ka ce?”

Ta furta tana jin wani sabon baƙin ciki na taso mata. Ganin ya tsaya yana kallonta sai kawai ta miƙe ta fice daga ɗakin, ya bi bayanta da kallo a ransa yana mata fatar shiriya.

Kiciɓis ta yi da Haƙabiyya da ke ta sanɗa tana ƙoƙarin hayewa samanta. Jawo hannunta ta yi kafin kuma ta kama kunnenta ta jata zuwa saman,”ke dan baki jin magana shi ne na ce ki tsaya ku zanta da shi kika yi tafitarki ko?” Ta furta tana ƙara murɗe kunnen. “Auchh! Mami dan Allah yi haƙuri, gani na yi ya tafi gun Baba hira, kuma ma ba ƙaramar matsala zan fuskanta ba idan na rasa lakcar, shi yasa na tafi, ki tambaye shi  har makarantar yazo fa.”

Ta cika mata kunnen ta ce, “me ya ce miki da ya zo makarantar?”

“Bai ce kome ba.”

Ganin ta harareta ya sata canjawa.

“Cewa ya yi in tsaya ya dawo da ni gida.”

“Sai kika ce me?”

“Sai na ce a’a nasan hanyar gidanmu.”

“Dan ubanki haka na ce ki ringa yi masa? Ke wato so kike ki ɓatan rai ko?”

“A’a Mami bai fa ji haushi ba, kuma ma ba kince kar na sake na shiga motar wani ba idan ba ta gida ba.”

“Ba ta wani ba ce, wannan ta abokin babanki ce wanda za ki aura, dan haka karya ƙara yi miki tayi irin wannan ki ce a’a, wallahi kar ki kuskura ki yi masa abinda zai ɓata da ke ya fasa auren. Ki  nutsu sosai,  ki kuma maida hankalinki kansa, kan lamarin nan zan iya saɓa miki ta inda baki za ta ba. Wuce ga abincinki can, ki kuma tabbata kafin  maghriba kin kira shi kinji yadda ya isa gida, kin kuma yi masa hira.”

“Haba Mami tsabar zubar da aji.”

Ba tasan a fili ta furta ba sai da taji saukar ranƙwashi a tsakiyar kanta, “ajin ubanki! Wannan za ki jawa ajin? Matsa daga gabana shashasha kawai.”

Ta wuce sum-sum ta faɗa ɗakinta tana fidda kwallar azaba.

Ta daɗe tana tuna mai zubin ghost da yadda ya shigo tsakaninsu ya raba hannunta da Huzaif, abin ya mata ciwo sosai, ta yi Allah wadai da irin ƙwaƙwalwarsa ta rashin fahimta, a haka barci ya kwashe ta ba tare da ta yi sallar ba balle cin abincin.

Washegari ana gama lecture biyun da suke da, ta ja gefe suka yi ƙusƙus da Hanifa, ta tashi ta tafi gidan Huzaif, kasancewar unguwa ce ta attajirai kowa yana gidansa yasa ba wanda ya ankara da sanda ta buɗe gidan ta shiga. A falon ta zube ta yi ɗaiɗai abinta, sai can kuma ta miƙe ta hau bubbuɗe ƙofofin falon har ta yi sa’ar ganin kitchen ta shiga, ta tsaya tana mamakin yadda aka tsara shi tamkar da mace a gidan. Gun fridge ta yi ta buɗe ta shiga ƙarewa fruits din ciki kallo, har ta hango Inab ta ɗauko ta fito falo ta yi gurin tv ta kunna ta dawo ta zauna. ‘Uhmm sai ka ce gidan ubana.’ Ta furta cikin ranta bayan ta jefa inab ɗaya a baki. Sai kuma ta kalli tvn jin wata baturiya na faɗin za ta kashe kanta, taga Film ake ga wata budurwa tsaye nesa da wani guy tana hawaye ta ɗora wuƙa a saman hannunta tana jiran idan bai ce yana sonta ba ta tsarga jijiyar, sai abin ya burge ta ganin guy ɗin ya taho da gudu ya rungume budurwar yana faɗa mata yadda zuciyarsa ke cike da sonta. Ta yi zumbur ta miƙe kafin kuma ta kwasa da gudu ta yi kitchen ta hau laluben wuƙa har ta ganta ta fito falon tana murmushi, a sannan ta ji kici-kici za a buɗe ƙofar falon, ta yi sauri ta ɓoye a ɗan wani lungu har ya buɗe ya shigo.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Hakabiyya 28Hakabiyya 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×