Riƙe kansa ya yi out of idea yana jin tahowar guntuwar kwallar da ta maƙale a gurbin idonsa. Hannu yasa ya ɗauke ta ya fara murzata a jikin yatsunsa yana hango girman abinda zai yiwa yarinyar da ta muzunta mutumin da yake matsayin mahaifinsa, ta zuba masa najasa saboda kawai ya nuna ƙaunarsa gareta. Abu ne mai girman da ba zai taɓa yafewa ba, sai ya muzanta Haƙabiyya yadda kare ma ba zai yi marmarin kusantar ta ba a bayan ya aje mata wasu sharuɗa ta sa kafa ta shure. Ƙara juyowa ya yi yana. . .