Skip to content
Part 31 of 32 in the Series Hakabiyya by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Riƙe kansa ya yi out of idea yana jin tahowar guntuwar kwallar da ta maƙale a gurbin idonsa. Hannu yasa ya ɗauke ta ya fara murzata a jikin yatsunsa yana hango girman abinda zai yiwa yarinyar da ta muzunta mutumin da yake matsayin mahaifinsa, ta zuba masa najasa saboda kawai ya nuna ƙaunarsa gareta. Abu ne mai girman da ba zai taɓa yafewa ba, sai ya muzanta Haƙabiyya yadda kare ma ba zai yi marmarin kusantar ta ba a bayan ya aje mata wasu sharuɗa ta sa kafa ta shure. Ƙara juyowa ya yi yana kallon layin da ya shiga. Tausayinsa ya daɗa kama shi, wani abu mai ɗaci ya tsaya masa a harshe ya gagara haɗiye shi. Tun yana shekara bakwai a wani dare da ya wuce ta gabansa goye da kakarsa har rana irin ta yau bai ƙara tozali da shi cikin farin ciki ba. Ya sha zaga duniya da shi ko zai dawo masa da walwalarsa sai dai ya gaza har sai a cikin shekarar nan adai wannan yammacin da ya hange shi tare da ita ya kira shi ya faɗa masa ita ce farin cikinsa, idan har da gaske yana son ganin walwalarsa to fa ya nema masa ita ya aura. Tunda yake da shi bai taɓa ganinsa da wata mace ba ko ya nuna masa yana son wata duk da kuwa ba wani ja shekarunsa suka yi ba, a ƙalla a yanzu yake Hamsin da biyu (52) sai ita. Sai dai ta ƙi lamarin saboda wani dalilinta marar tushe, saboda ita shi take ƙauna, duk da kuwa yasan iyayenta musamman uwarta burinta keman. Shin ta yaya shi ba zai yi koma menene ba gurin ganin mahaifinsa ya samu abinda yake so? Ta yaya zai zama ɗa marar cika burin ubansa? Ta yaya kuma zai duba farin cikin wani saɓanin na halittar da baya da madadinta? Da Allah ya yi rantsuwa sai ya aura masa ita ko da za ta haɗiyi garwashin wuta don ƙiyayya. Sai dai fa a yanzu sai ya shayarta mamakin da har abada ba za ta ƙara gigin ɓata musu rai ba. Da wannan tunanin ya juya kan motarsa zuwa gida dan ya samu rigar da zai ɗora kan best ɗin jikinsa.

Yana isa kallo ɗaya yawa gate ɗin yasan da mutum a cikin, bai yi mamaki ba ya san hakan za ta iya yiwuwa dama idan har tasan abinda ta yi, da sauri ya ƙarasa cikin gidan. Wacce ya za ta ɗin ita ce zaune a tsakiyar falon. Ganinsa ya sakata miƙewa tana tattare jikinta guri ɗaya.

“Babana kika zubawa najasa Haƙabiyya, Baba nane fa daya maidani mutumin da har kika iya yabawa kike son. A bayan haka kuma saboda ba ki da mutunci da tarbiyya kika tako gare ni har cikin gidan da na hanaki zuwa, ashe har kina da kunyar da za ki iya tsayawa a gabana? Anya da hankali a jikinki?”

A hankali ya faɗa a hankali kuma kalmomin suka shige can cikin kunnuwanta da wani irin shiru da ke shirin daskarar da jininta. Idanuwanta ta lulluɓe ta gagara sanin irin hujjar da za ta bashi kan haka. Ba ta gudun zafafan kalamansa sai dai fa tana gudun ta ƙara nanata masa tsanar da tawa uban nasa ta kai matsayin da za ta iya aikata komen da zai sakata nadama a yanzu. Sanin ba tada wata hujja bayan wannan ya sakata zamewa a hankali ta durƙushe a gabansa a kan gwuwowinta tana haɗe tafukan hannayenta.

“Ka yi hakuri… Don Allah ka yi hakuri…”

Tana kula da sa’adda ya cije laɓɓansa ya juya mata baya. Tafi ƙarfin minti goma a haka kafin ta miƙe a hankali ta kewayo gabansa.

“Amma fa Huzaif ya kamata ka duba gaskiyata, saboda Allah idan ba mutuwar zuciya ba ya za ai kamarsa ya ce ni yake so da aure shi ko kunyar Baba ma baya ji, ko kunyar abinda ya musu bai ji, ko kunyar ƙananun shekaruna bai ji ba, na tabbata zai ba ni shekaru fiye da talatin wallahi. Haka Ya fa san kai nake so, kai nake ƙauna, da kai nake da muradin gina rayuwar aure na, to me zai sa sai a yanzu da yasan ka gama isa gurin da ba za ka taɓa gogewa a zuciyata ba shi kuma ya zo da batun da har kunyar furtawa nake, ɗazu fa su Mami suka sanya rana sati biyu, yanzu Huzaif ba ka jin kome kaina? Ka yarda ka binne ƙaunar da kake mini saboda uba irin naka da bai taɓa tsayawa ya tambayeka abin…?

“Tau!” Ta ji ya ɗauke ta da wani zazzafan mari, kafin ta dawo hayyacinta ya ƙara ɗauketa da wani da bayan hannunsa. Ta fara yin baya da baya yana biyota har sai da ta kusa isa ƙarshen ɗakin.

“Na rantse da Allah ba zan taɓa sonki ba idan ma saboda ni kike aikata hakan, a yaushe shi Abba ya san kina so na…!?”

Ya furta yana idasa cike tazarar da ke tsakaninsu. Tana jin yadda hucin zazzafan numfashinsa ke ratsa duk wani tsiron gashi na fuskarta, akan idanunta jijiyoyin goshinsa ke wani irin kumbura da ɓacin ran da ba ta taɓa tunanin yana da shi ba.

Hannunta ta kai ta shafa in da ya mare tan, ta ji ciwon abin har a cikin dunduniyarta, sai dai fa da Allah ta yi rantsuwa ba za ta taɓa bari Huzaif ya zama ba rabonta ba, dan haka ta kafe shi da jajayen idanuwanta da suka rine da ɓacin rai, babu ko alamar hawaye cikinsu ta ce “ni ma na rantse da girman Allah ba zan taɓa daina son ka ba, zan rayu da kai koda kuwa da gawarka ce. Babanka kuma ba zan aure shi ba ko zai mutu alƙawari ne wann..!” Bata kai ga idasawa ba ya sa hannayensa biyu ya hankaɗata jikin bangon kanta ya ƙumu da garun ta yi gefe za ta zube a gun ya fincikota zuwa gabansa ya sanya hannayensa biyu ya danƙi kafaɗunta.

“Ban san da wani kalar yare kike so na maimaita girman tsanata gareki ba Haƙabiyya. Amma abu biyu nake umartarki shi ne ki ringa kallona a matsayin Ajalinki idan har ba za ki yi biyayya ga abinda mahaifina yake so ba. Ke wai idan ba dabba ba mai tosasshiyar basira ta yaya kina ikirarin kina so na kina kuma cin mutuncin mutumin da yake uba a gare ni? Shin da ace wata alaƙa za ta shiga tsakaninmu me yake zame miki a yaren Hausawa? Da wani idon za ki dube shi, da wacce ƙafar za ki taka gare shi domin kai gaisuwa gare shi a yayin da ƙaddarar da ba na fatar sauyawarta ta sauya?Wai shin… Ke ɗin, wacece ma a cikin mata da har za ki guji mutum me tarin alheri irinsa? Da me aka yi ki da har za ki dubi tsabar idona ki ce kin tsani ubana. Bari ki ji… A yau ko da ba shi ba tunda har kika iya ɗaukar najasa ki ka zuba ta ga ɗan Adam mai tarin daraja wallahi summa tallahi kinji na rantse ni Huzaif *BA ZAN IYA AUREN IRIN KI BA…!”*

Maƙogwaronta ta ji ya bushe, ruwan hawaye ya fara sauka har saman laɓɓanta, kakkarwa take yi tana jin yadda haƙoranta ke datsewa, magana take sonyi ta kasa, idanuwanta ta tsaida a kan shi, tana ganin girman ƙiyayyar da ke barazanar tsinke numfashinta, tana ganin yadda gaskiyar zantukan da ya faɗa ke bayyana ɓaro-ɓaro saman fuskarsa. 

“…Sannan abu na biyu da zan faɗa miki shi ne kar ki kuskura ko da wasa ki yi dalilin da Abba zai san na taɓa wata alaƙa da ke ko kuwa kin taɓa buɗe bakin ki mai warin masai kin ce kina so na. Kar ki kuskura wannan batun ya je kunnuwansa ina daɗa maimaita miki kar ki kuskura! Akan wannan zan iya kome dan ganin na wargaza rayuwarki na ɗaiɗaitata yadda ba za ki ƙara moruwa ba. Ki ji tsoron rayuwa, ki ji kuma tsoron duk wata halitta da ta fito a jinsin Namiji..!”

Da ruwan hawayen da bata san ya za ta iya hana zubarsu ba ta tare shi…

“Huzaif duk ina burge kan da ka ce ina yi, shin shi ba so ba ne…Duk ina wannan abu mai muhimmancin da ka gayyace ni guri mai muhimmanci za ka faɗa mini shin ba kalmar so ba n…?”

“To hell with you and your gayyatar! A gidan ubanki na taɓa furta ina sonki?…”

Ya yi saurin tare ta yana daɗa zare mata manyan idanuwansa.

“Shin ke a cikin dabbobin da ake ƙyamata wanne iri ne ya lashe miki zuciya wai?Hala Alade? Ba ki ji na ce miki ba na ƙaunarki ba sai na ƙara nanata miki ba na ƙaunarki? Ba ki ji na ce miki ba zan taɓa auren irin ki ba sai na ƙara nanata miki ba zan taɓa aurenki ba ko za ki haɗiyi zuciya ki mutu gabana? Shin wai tare aka halicce mu ne da ba za ki iya barina ba ki fita daga rayuwata? Ko ƙanin ubanki nake zame miki ne wai? Ko kuwa kama kika ga ina yi da uban da ya haifi ubanki!!? Na ce ba na ƙaunarki! Idan kina son ganin dariyata gareki shi ne ki je ki auri mahaifina da kike kira mai matacciyar zuciya!!!”

Ba ta iya furta komai ba, amma tana jin yadda wani nauyi ke sake danne ƙirjinta, tana jin yadda kalamansa ke tsittsinka mata zuciya, suna zarcewa can cikin kwakwalwarta inda ba za su taɓa gogewa ba. A haka ta sanya hannuwanta da ɗan ƙarfin da ya rage mata ta fincike kafaɗarta da ya riƙe a hannunsa.

“…Sannan ko da wasa kada ki sake gigin shigo mini gida, wallahi kinji na rantse da ƙarfina zan tausheki anan na miki abinda za a ɗinke ki tamkar kwaryar da ta shekara goma a farfashe. Shigowa cikin gidana ya ƙare duka a tun ranar da halittar da ba ni da madadinta ta tsaida lokacin aurenki. Na roƙe ki da gobe idan Alhajina ya dawo ki dasa wuƙa a tsakanin tsokar da ke tsakiyar ƙirjinsa ƙarshen ƙiyayya, Abba ne dai ba zai fasa son ki ba, ba kuma zai fasa aurenki ba kin riga kin zame masa baƙar annoba, baƙar jaraba! Fita daga gidan nan!!”

Ya idasa da ƙaraji yana nuna mata hanyar ƙofa.

Wani kallo ta masa da ya girgiza shi, ta tattara dukkan ƙarfinta ta juya da gudu ta fice daga gidan.

Kai tsaye gida ta yi sai dai tana shiga ta ga Zawwa tsaye a tsakiyar falon hannayenta rungume a ƙirjinta.

“Daga ina kike!?”

Ba ta yi magana ba sai rugawa da ta yi da gudu ta shige jikinta tana fashewa da wani irin kuka mai karya zuciyar me sauraro. 

Sororo Zawwa ta yi ganin ta yi abinda ba ta taɓa yi ba shi ne ta zo cikin jikinta. Ƙoƙarin ɓanɓareta ta fara yi ta ƙara ƙanƙameta sai ta ji ta bata tausayi.

“Ki bar ni dan Allah! Da ciwo sosai… Da ciwo sosai a lokacin da ka gane mutumin da kake ƙauna bai taɓa sonka ba, da ciwo Mami, its hurt so much, I feel like I’ll die. What should I do?…”

“Mene?Kome haƙuri ake yi…”

Zawwa ta furta tana shafa bayanta duk da bata fahimci kome ba.

“Ba zan iya ba, ba zan iya ba Mami ina ƙaunarsa sosai…! Na miki lefi mai yawa da ban faɗa miki mutumin da kike so na aura da ɗansa muke tare ba, shi nake so da ƙauna, na sake miki lefi da na ɓoye miki munanan halin da nake gwadawa Abokin Baba. A yau da Hanif ya yi bayan gida na ɗauka na juye masa a kai dan ya tsaneni ya fasa aure na dan kansa, na watsa masa wannan najasar a idon ɗansa Mami, shi kenan ko? Na ɓata kome ko? Haka shi ma ya ce mini ba zai so ni ba ko da ba Babansa na aikatawa haka ba? Ba zai so ni ba ko da bai taɓa sanin mutumin da na aikatawa hakan ba. Me zan yi Mami?”

A hankali ta zare jikinta daga nata ta lalubi kujera ta zauna tana ambaton Allah a zuciyarta. Tabbas Bawa ya yi gaskiya da yake ce mata ba a tsaurara ƙiyayya za ta iya zo maka da salon da zai baka mamaki. Kallonta ta ƙara kaiwa kanta ganin ta durƙushe tana zubar da hawaye kan ɗan mutumin da ta tsana a duka duniyarta, shin ta yaya za ta yafe wannan? Wato har a yanzu Hameedu bai daina cutarta ba tunda gashi ya kawo musu abinda ya tada hankalin ɗiyarta kwalli ɗaya da ba tada tamkarta a duka rayuwarta, ya kanainayeta gabaɗaya ta yadda har ta gagara saita tunaninta kan abinda za ta yi. Shin burin zuciyarta za ta bi ko kuwa farin cikin ‘yarta kwalli ɗaya za ta duba? Anya tana da zuciyar da za ta iya haɗa jini da jininsa, anya tana da zuciyar da za ta iya yini gudu cur! Da jinin Hameedu? Idan kuma ta dage gurin daƙile farin cikin ‘yarta domin cikar nata burin anya za a samu halittar da za ta ƙara mata kallon uwa ta gari? Runtse idanuwanta ta yi da ƙarfi tana yamutsa halittar goshinta cikin rashin  sanin abinyi. Jin hannu a jikinta ya sanya ta buɗe idon ta ganta duƙe a gabanta cikin hawayen da take jin ciwon ganinsu a fuskarta har cikin ruhinta.

“Mami kin ji zafi na ko? Tabbas ban zama ‘yar halak ba da na zamto mai jawo miki zagi har a mini gorin rashin tarbiyya. Bansan me ya sa a duk lokacin da zan gan shi a sannan wutar ƙiyayyarsa ke mamaye dukkan ruhina. Bansan dalilin da yasa a tun ranar da na ganshi cikin gidan nan nake jin zuciyata na wani irin zugi da azabar raɗaɗi. Bansan me ya sa ko sunansa na ji an ambata a sa’adda nake guri sai na ji mummunan faɗuwar gaba ta same ni ban sani ba wallahi, shin wannan ƙiyayya ce ko kuwa akwai wani abu da nake tsoro tattare da shi? Mami na so kaina a lokacin da na dage gurin ganin na samu abinda nake so ta ko ƙaƙa duk da ku kun nuna mini abinda kuke burina da shi, sai dai a yanzu na dawo nutsuwata a sa’ilin da na gane bin ki da zan yi k7uan dukkan abinda kike so a matsayinki na uwa gare ni shi ne hanyar rabautata. Bansan dukkan dalilinki na son aure na da Abokin Baba ba na dai san kince shi ne silar da Baba ya rasa ƙafa ɗaya dan haka kika umarce ni da aurensa domin ɗaukar fansa, duk da kuwa shi Baba ya nuna mini Idan ma akwai wannan zance to ya yafe masa duniya da lahira, ya kuma umarce ni da idan zan aure shi to na aure shi domin Allah. Mami na yarda zan aure shi domin na ɗaukar miki fansar, zan aure shi domin shi ne abinda mutumin da nake ƙauna yake so, zan aure shi domin haramta abinda ke tsakanina da Huzaif! Na yarda a ɗaura ko nan da mako guda ne!!”

Daga haka ta miƙe da gudu ta haye sama.

Baki buɗe ta bita da kallo ganin kamar ba cikin hayyacinta ta faɗi maganganun ba. Sai dai ga mamakinta a hawa na biyar da ta taka ta juyo ta mata murmushi wanda ke nuna abinda ta faɗa ya fito ne  daga zuciyarta.

Wani yawu ta haɗiya mai ɗaci jikinta na ƙara sanyi a yayin da wani ɓari na zuciyarta ke sanyata tunanin ranar nadama. Ɗiyarta da ke cikin shekarunta na 22 ne ta hana kanta farin cikinta saboda ta cika mata nata burin! Ƙara cira kanta sama ta yi tana kallon matattalar da ta bi. A ranta take jin ko a wuta za ta ga Hameedu da dukkan ahalinsa idan ba ta ƙara izata ba, ba za ta taɓa gigin ciro shi ba balle ta kai ga yayyafa mata ruwa!!.

<< Hakabiyya 30Hakabiyya 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×