“In buɗe maka zuciyata?”Kyakkyawar santaleliyar budurwar ta furta daga bakin ƙofa.
Da kallo ya bita har ta maida ƙofar office ɗin ta rufe ta taho ta ja kujerar kusa da shi ta zauna tana kafe shi da mayatattun idanuwanta.
“Ina neman tsari…”Ya furta yana ci-gaba da duba tarin takardun gabansa, ganin ta yi shiru ya saka shi ɗagowa yana daɗa tamke fuska.
“…Ki tashi ki tafi, kin fi kowa sanin abinda shigowarki nan ke haifarwa…”
“Na shirya hakan, dan hakan ma na shigo, ina so inta maimaita shekarar idan har kana tare da ni anan. . .