Skip to content
Part 5 of 32 in the Series Hakabiyya by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

“In buɗe maka zuciyata?”
Kyakkyawar santaleliyar budurwar ta furta daga bakin ƙofa.

Da kallo ya bita har ta maida ƙofar office ɗin ta rufe ta taho ta ja kujerar kusa da shi ta zauna tana kafe shi da mayatattun idanuwanta.

“Ina neman tsari…”
Ya furta yana ci-gaba da duba tarin takardun gabansa, ganin ta yi shiru ya saka shi ɗagowa yana daɗa tamke fuska.

“…Ki tashi ki tafi, kin fi kowa sanin abinda shigowarki nan ke haifarwa…”

“Na shirya hakan, dan hakan ma na shigo, ina so inta maimaita shekarar idan har kana tare da ni anan.”

“Ba ki da hankali,  ki fita daga nan na ce ba maganar banza ba, bansan nuna ɓacin raina gareki na gaji da miki tsawa da hantara, na gaji da ganin mummunar fuskarki ta fitsara a gabana, ke ko kunya baki ji kaf makarantar nan sun san kina bibiyata, to ba wannan wasan da na yi nan ba kenan…”

“Kullum sai ka faɗa mini haka, amma ana cewa watarana sai labari. Ni tambayarka na zo yi.”

“Game da me fa?”
Ya furta yana tattare hankalinsa kanta fuskarsa a cunkushe.

“Ɗazu na ganka kana satar kallona me ke nan? Sannan ka ƙi faɗa mini dalilinka na faɗar da ni a jarrabawa, shin dan na ƙara maimaita shekarar ne ka ci gaba da ganina ko?”

Dafe kansa ya yi cike da nadamar zamansa a office din har ta same shi, shi kam koyarwar nan ƙoƙari take ta zame masa Annoba,  yarinyar ta gama shiga rayuwarsa ta gama tsaya masa a duk inda bai zata ba a tun ranar da ya fara lecturing a makarantar. Ya rasa waye ubanta a garin na Kano da aka kasa ɗaukar matakin abinda take masa ko da ya faɗawa manyansa na jami’ar, shi ba gwanin wulaqanci ba amma da ƙarfin tuwo sai da ta koya masa yake yarfa mata shi a cikin mutane sai dai fa babu alamar yana damunta. Lokaci ya yi da ya kamata shi ya ɗauki mataki da kansa, dan haka ya ɗago yana dubanta a ƙuntace.

“Ina ne gidanku?  Ya kamata na ga Babanki.”

Ta washe masa jerarrun fararen haƙoranta.
“Ƙara ta za ka kai gunsa ko? To gashi…”

Ta furta tana zira hannu cikin jakarta ta fiddo da wani kati mai kyau da aka ƙawata shi da ruwan zaiba ta aje masa gabansa.

“…Amma dan Allah ka faɗi kome banda zuwa office ɗinka da nake yi…”

Ta furta a marairaice, sai kuma ta ɗan duƙo gabansa tamkar mai tsoron wani ya ji abinda za ta faɗa, ƙamshin fitinan nan turarenta ya surare zuwa cikin hancinsa har sai da ya lumshe ido ya buɗe cikin nata da suke wani irin maiƙo dan kyau.

“…Idan Mami ta ji wannan labarin wallahi sai ta kusa karyani. Kai kanka kasan ba wahalar karyewa zan yi ba dan kuwa ka sha yi mini ba’ar ƙafafuwana kamar na Barewa…”
“Oh! Ni kuwa wai ina ka taɓa ganin Barewar da kake mini ba a da ita…?”
Ta furta tana mai cije laɓɓanta na kasa a hankali, sai kuma ta ƙara wara idanuwanta tana daɗa duƙowa gabansa tamkar mai son haɗa hanci da shi.
“…To dan haka ka rufa mini asiri yadda na saba rufa maka…”

“Ni kike rufawa asiri dan baki da kunya?”
Ya furta da zallar mamaki yana saka hannu ya harba katin ya yi nasa guri.

“To so nawa wai? Ko ɗazun da na ganka kana satar kallona ai ban faɗawa wani ba, haka rannan da na ganka kana kallon tafiyata ban faɗawa wani ba. To ko rannan da ka turo mini goodnight ta number da ban sani ba ai ko Hanifa ban faɗawa ba duk kuma ina haka ne dan kar na zubar maka da ajin da kake ta riritawa.”

Ta ƙarasa tana langaɓe kai.

Aji? ya furta a ƙasan ransa yana jin dariya-dariya na kama shi, sai dai da sauri ya gintse tuna wacece a gabansa.

“Haƙabiyya sunanki ko…?”

“Kullum sai ka manta sunana, wayyo duniya, Ya Allah na roƙe ƙa da girman zatinka ka zare soyayyar wannan bawa naka daga zuciyata ka sanya finta a cikin zuciyarsa.”

Ta faɗa tana saka hannu bibbiyu ta riƙe kumatukanta.

Ya buɗe bakinsa sosai yana dubanta, ya daɗe yana saƙa yarinyar ba lafiya take ba bai taɓa jaddada zatonsa ba sai yau. Ga mamakinsa sai ya ji hannunsa a ƙirjinsa yana shafa saitin zuciyarsa.

“Allah ya tsare ni da wannan mugun fatan naki, ki tashi ki tafi daga nan kina haddasa mini ciwon kai da wannan turaren naki mai warin tafarnuwa! Sannan rashin muhimmancinki gare ni yasa ba na iya ko riƙe sunanki, ya kamata ki gane ni ba Malamin da zan tsaya soyayya da dalibata yarinya ƙarama marar kunya kamarki ba ne. Wai shin a ina kike koyan wannan fitsarar? A ina kamarki tasan ta dubi tsabar idon namiji duk girmansa ta furta tana sonsa…?”

“Sir a dubu biyu da sha takwas (2018)  muke ba a dubu ɗaya da ɗari tara da casa’in da takwas (1998) ba, sannan boarding school na yi fa inda ake gudanar da rayuwa fiye da kala ɗari, to ko kafin na gama aji uku na ƙaramar sakandiren malamai biyar suka ce suna so na nasa ƙafa na ture saboda Allah ya riga da ya ƙaddara ni taka ce. Sa’annan ni ba yarinya ba ce ba za ka gane ba ne, to ko in miƙe ka ga tsayina? Shekaru ashirin fa saboda Allah haba Sir ya kake kallo nane a idonka?”

Ya ƙanƙance ido yana kallonta kansa na daɗa tamkewa da mamakin da take bashi a duk buɗe bakin da za ta yi.

Tabbas ba yarinya ba ce a gurin kowane ingarman namiji irinsa, sai dai fa ta yi yarinya ace kamarta ta iya bibiyar namiji da wani shirmen soyayya.
“Ka damu na tafi ko…?”

Ta furta a sanyaye tana miƙewa tsaye.

“… Zan tafi amma idan ka faɗa mini wannan kalmar.”

“Wacce fa?”

“Wacce nake faɗa maka kullum.”

“Bansanta ba.”

Ya furta yana buɗe wani ƙaton text book da ke gabansa.

“Sir Please… Ko sau ɗaya ne…”

“Ba sunana Sir ba, ki kirani Huzaif ɗina kawai, Sir ai ba a kawo masa wargin ana sonsa.”

“Dan ALLAH, ka ji…?”

“Ya Rabbi!”

Ya furta yana bubbuga biron hannunsa a goshinsa. Sai kuma ya tsura mata ido ganin yadda ta wani narke kamar mai shirin kuka.
“Idan na faɗa za ki kyaleni ko na wata guda ne?”

Murmushi ta yi da ya tsinka zuciyarsa, ya kai hannunsa kamar zai taɓa nata da ke aje gefensa sai kuma ya share.

“Idan har ka faɗa ne daga zuciyarka zan kyaleka iya yadda kake so.

“To Haƙabiyya kina burgeni. Shi kenan?”

“Shi kenan kam, na tafi to. Amma kar fa ka manta ina ƙaunarka sosan gaske, ba kuma za ka taɓa samun iri na ba. Haka ba zan taɓa manta ka ce ina burge ka ba”

Daga haka ta juya akan takunta mai cike da kwarkwasa. Ya bi bayanta da kallo har ta buɗe ƙofar ta fita, sai dai fa kafin ya sauke wani kwakkwaran numfashin ƙofar ta sake buɗewa sai gata ta leƙo tana haske shi da murmushin da ke tsaya masa arai ya hana shi sukuni har cikin barcinsa.

“Sir faɗa mini gaskiya, da na juya bin bayana ka yi da kallo ko..?”

Da ƙarfi ya daki teburin gabansa yana miƙewa tsaye.

Ba shiri ta rufe ƙofar tana dariya. Ya koma daɓass ya zauna yana riƙe kansa, sai yanzu kalamanta suka dawo cikin kunnuwansa, murmushin gefen baki ya ƙuɓce masa, wai ba zai taɓa samun kamarta ba. Ko waya faɗa mata akwai mace a gabansa? Shi baya buƙatar a so shi baya kuma buƙatar ya so wani. Shi fa kwata-kwata bai ma kawo zama da mace a lamarinsa idan har ba wani mutum guda da ke cikin rayuwarsa ya ga ya zama irin abinda yake so ba, ya ga ya samu macen da za ta kula da shi har ƙarshen zamansu. A sannan ne yake jin zai iya duba me zai yiwa kansa idan lokacin bai ƙure masa ba kenan.

*****

Kai tsaye gurin ƙawarta Hanifa ta yi da ke tsaye bakin gate tana ta jiranta. Da gudu ta ƙarasa ta ruƙunƙumeta tana tsungulinta.
“Keee! Kinsan Allah plan ɗinki ya mugun yi, ke kinga yadda ya rikice ya gigice yana rawar mazari tamkar Michel a club?”

Hanifa ta tureta tana harararta cikin wasa.

“To sau nawa dama na faɗa miki kika ƙi ji? Ai fa ki daina bari yana treating ɗinki kamar wata yar 14, ki nuna masa kin isa macen da ke buƙatar irinsa cikin rayuwarki ba shi ba ma ke ko da sa’an Babansa za ki iya gog…”

Ta yi sauri ta rufe mata baki tana janta gefe.

“Ban fa san ɗanyar balagarki, ni ki faɗa mini mene tsarin goben?Allah har yanzu ji nake kamar na koma, ke har fa miƙo hannu ya yi kamar zai taɓa ni ya fasa, ya rabbi! I’ll never forget this moment…!”

Ta dakata tana lumshe idanuwana.

“…Ko ya zan ji hannunsa? Ina feeling kamar ya kai taushin na Gebriel na cikin novel din (The boss takes his wife).”

“Ko kamar bayan kada ne haka zai taɓa ki da shi.”

“Eh na ji ina sonsa a hakan ma. Ni ki faɗa mini tsarin goben na ƙagu ɗan mitsitisin bakinsa ya furta yana so na.”

“Lokaci ne fa zai zo, ko a yanzu akwai wacce ta isa ta yi daɗewar da kike yi a gunsa idan?”

“Kai kai Hanifa kina gigita Ni fa, ke kaɗai ke ba ni tabbacin wataran Huzaif nawa ne.”

Yauwa to bari kiji tsarin, ta lalubi kunnanta ta raɗa mata. Ta daɗe shiru, sai kuma can ta mata murmushi adaidai lokacin da direbanta ya ƙara so.
“Shi kenan to mu haɗe goben.” Daga haka ta shige motar suka yi gida.

Tun a falon ƙasa take kwala mata kira, ganin ba ta ganta ba ya saka ta hawa sama zuwa cikin ɗakinta nan ma bata nan. Ɓangaren Abbansu ta yi sai dai fa tunda ta doshi hanyar da za ta kaita bedroom ɗinsa take Jin hayaniya. Dan haka ta ƙarasa saɗaf-saɗaf ta tsaya a bakin ƙofa tana saurararsu.

“Ni ba hanaki neman Hamidu na yi ba, mummunan ƙudurinki kansa nake so ki cire. Zawwa! Ba fa da wannan alƙawarin muka baro ƙauye ba, kar ki zama cikin mutanen da Allah ke la’anta saboda rashin cika alƙawarinsu. Shin wai ba cewa kika yi har abada ba ki sake ambato mini sunansa ba? To menene ya yi zafi da tun farkon shigarmu shekarar nan har yau da muke ƙarshenta  kika tsiri tada mini hankali kan lamarinsa?”

“Ni fa har abada ɗin da na ce na nufin har Hamidu ya nemo mu domin yafiya. Ban za ci yana da zuciyar da zai kwashi shekaru ashirin ba tare da ya neme ka kan haƙƙin ka ba ban za ta ba wallahi. Haka a yanzu ne yarinyar ta yi girman da za ta iya kama mini zuciyar namiji kome shekarunsa, dan haka Bawa sai dai ka yi haƙuri ba zan iya yafewa Hamidu ba har abada, alƙawari na ɗauka sai na nemo shi na dasa masa ciwon da ni kaɗai ke da maganinsa. Sai na dasa masa dafin ƙaunar yarinyar nan na barshi ya same ta a ƙarƙashin inuwarsa na tsahon kwana uku kacal!A bayan ya mallaka mana dukkan abinda ya mallaka ta dalilinmu a sannan kuma zan saka kakkaifar adda na datse alaƙar da na haɗa ɗin na maida shi ɗan kwikwoyin da zai na bibiyata kullum safiya yana tanɗar tafin ƙafata har ƙarshen rayuwarsa…”

“Kin yarda ki maida diyarki bazawara saboda son zuciyarki Zawwa ki kashe rayuwar yarinya ƙarama?”

Ya furta da zallar mamaki, a karo na farko da ya ji tsoron ƙiyayya irin tata na damunsa.

Sakar masa wani murmushi ta yi da iyakarsa fatar baki a bayan ta saka siraran yatsunta ta ɗauke kwallar idonta. A sannu ta miƙe daga inda take ta isa gabansa tana sanya hannu ta  janye rigarsa da ta rufe dungulmin ƙafarsa, ta tsura mata ido na ‘yan mintuna tana kallo kafin kuma ta ɗora hannunta a kanta, ta runtse ido ta buɗe su cikin na Tsoho Bawa da ke dubanta a tsumaye.

“Ba zan tozarta rayuwarta ba duk da ya tozarta tawa ya maidani matar nakasasshe. Idan ana neman haihuwa domin barin baya, barin wanda zai maka addu’a, barin wanda za a kira a ce jininka ne, ka sani a yau zan faɗa maka wani abu da baka sani ba, ni na  shafe shekaru biyu cif ina neman haihuwa irin ta ɗiya mace domin kawai ta ɗaukar mini fansa kan abinda Amininka ya mana. Bawa ko ina da niyyar yafewa Hamidu wallahi da Allah na yi rantsuwa ba zan yafe masa tunda har aka shafe shekaru ashirin bai waiwayemu. Dan haka kabar mana mugun tun…”

“Kenan ba ki tsoron reshe ya juye da Mujiya?…”

Ya tari numfashinta yana haki.

“…Ba ki kuma tsoron ƙaddarar da za ta haɗa abinda ke ko ni ba za mu iya hanawa ba balle rabawa. Ba ki tsoron jarabtar da za ta saka ita ɗiyar taki ta dubi tsabar idon ki ta ce miki bata rabuwa da Hamidu ba kuma ta mallaka miki dukiyar Hamidu? Zawwa na tabbata a ranar fashewa za ki yi namanki ya yi ɗaiɗai a dandaryar ƙasa saboda baƙar ƙiyayyar da ke lulluɓe a ruhinki, ni kam ba ni da ƙafar da zan tashi na tattara namanki domin kai ki makwancinki ina dai da bakin da zan buɗe domin yi miki dariya. Kar ki fara wannan wasan, kar ki fara abinda baki san ƙarshen sa ba idan har na isa mi…”

“Ka isa! Amma ka sani idan har ta rayu a ɗumina tsahon shekaru ashirin, ta tsotsi hallittar nan biyu da ke tsakanin ƙirjina ba za ta taɓa ture abinda nake so ba, ba kuma za ta zambace ni ba irin yadda Aminin ka ya yi. To balle ma na buɗe bakina na faɗa mata shi ne sanadin rasa ƙafarka guda ɗaya. Shin wata ɗiya ce ta halak da za ta ji wannan ta kasa ɗaukar fansa?”

Murmushi ya sakar mata mai ciwo yana daɗa auna shekarunta cikin hankalinsa.

“Shi kenan Zawwa je ki nemi Hamidu ki aura masa Haƙabiyya bisa ƙudurinki. Ni Bawa ba zan sake tunasar da ke ko ƙoƙarin hanawa ba. Zan dai dawwama yi miki addu’ar samun nasara. Allah Ya baki sa’a.”

Haƙabiyya da ke laɓe bakin ƙofar ta dafe ƙirjinta tana ambaton sunan Huzaif cikin zuciyarta. Sai kuma ta zare ido tana girgiza kai, inaa! Dole nema ta turo shi gidansu ya nemi aurenta kafin Mami ta gano mutumin da take nema ta aura mata. Ta ƙara jingina kanta sosai jikin ƙofar ko za ta jiyo suna wani ƙusƙus ɗin, ba ta san ta taso za ta fito ba sai da ta buɗe ƙofar ta kuwa ta fi luuu za ta faɗa ta tare ta a jikinta tana kallonta cike da zargi. Da sauri ta ƙaƙalo murmushi tana yatsina fuska sai kuma ta riƙe saitin goshinta.

“Mami Allah goshina ciwo yake, wayyo zai rabe.”

Ta furta a marairaice tana yarfe hannu.

“Ciwon kan ne sai kin biyo ni har nan? Ina magungunan ɗakinki?”

“Babu fa, ni dama faɗa miki zan yi gobe kar a tura mini driver zan dawo da kaina. Kakarsu Hanifa ce ta faɗo daga gujerarta ta gurɗe ƙafa, to za mu je dubo ta.”

Ta ƙara kallonta tana nazarinta kamar me son ganin wani abu.

“To ba za ki je ba…”

“Mami… Dan Allah mana…Washh.. kaina!”

“Ya ki Autata, ƙyaleta zo ki zauna nan ina da maganin ciwon kai a drawer.”

Tsoho Bawa ya furta yana yafitota.

Da sauri ta tafi gunsa ta zauna tana tankwashe ƙafa.

Zawwa ta bisu da ido sai kuma ta taɓe baki ta fice daga ɗakin.

“A ina ne shi gidan Kakar tasu yake.?”

 “Nassarawa G.R.A.”

“To shi kenan Allah ya kaimu sai kuje, amma kar ki yi maghriba.”

yesss!  Ta furta cikin ranta tana jin daga gobe burinta zai ida cika.     

<< Hakabiyya 4Hakabiyya 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×