Skip to content
Part 6 of 32 in the Series Hakabiyya by Fulani Bingel

A can cikin wani ɗaki da aka gina a ƙarƙashin ƙasa a tsakiyar wani baƙin daji dake yamma da wata kushewa. Wata ƙwarya ce da ke cike da wani baƙin jini ta fara girgiza tana darewa, jinin cikinta ya fara toroƙo yana zaɓalɓala tamkar yana bisa garwashi, kafin kuma ta tarwatse gabaɗaya jinin ya fallatsa a ilahirin farin mayanin da aka kewaye ɗakin da shi, a sannan ne Ragon ya bayyana yana kuka, sai kuma ya yi tsit! Yana tsurawa mutumin da ke zaune acan kursuwar ɗakin kan wata baƙar kujera ido, a hankali kuma ya durƙushe a gurin yana kafa ƙahonsa a ƙasa tamkar wanda ya yi tozali da manyan dawa.

Mutumin da yake dattijo baƙi, mummuna na haƙiƙa ya miƙe tsaye hannunsa dafe da wata baƙar sanda da aka sassaƙa mariƙinta da siffar kan mujiya. Ya taka a hankali zuwa gaban ragon ya ja ya tsaya idanuwansa a rufe. Ya buɗe baki ya fara furta wasu irin kalmomi yana kiran wani suna, ba daɗewa wanda yake kiran ya bayyana a gabansa ta cikin wani duhu, a sannan ne ya yi shiru ya buɗe idanuwansa yana kallonsa.
“Abinda muke aikinsa sama da shekaru ne ka turo mana Rago a madadinsa?”

“Ayi haƙuri kuskure ne…”

“Ba ma aiki da kuskure…!”

Ya furta da tsawa har sai da mutumin ya ja baya.

“…Da wannan kuskuren naka za ka rasa abinda ka fi so a duka rayuwarka, kar ka manta numfashinta tamkar kwan jimina yake a hannuna, a kowane lokacin da na tunzura zan iya sakinsa ya tarwatse a gaban idanuwanka. Na baka mako guda da ka kawo mini wannan yarinyar tunda har ta riga da ta taɓa wannan ƙyallen, idan ka kuskure hakan ka fi kowa sanin irin jinyar da zan iya saukar mata da sunanka!”

“Zan kawo ta ko gobe ka ce, amma a ɗan daɗa ba ni lokaci na ƙarshe, a kuma duba wannan alfarmar da na nema, a duba darajar addinina tunda an umarci na nemi wani ‘yancin… Zan kawo ta cikin biyayya da dukkan abinda kake so.”

Dattijon ya juya ba tare da ya ce masa uffan ba ya koma kujerarsa ya zauna ya rufe idanuwansa. Sai can ya ɗaga masa hannu alamun ya tafi ya gama magana da shi.

*****

Tun sa’adda ragon ya ci laya, hankalin tsiraran mutanen unguwar ya ƙi kwanciya har sai da aka tattaro malaman unguwar suka dinga karatun Qur’ani kusurwa-kusurwa. Sai dai fa har ƙarfe bakwai na dare Hamdiyya ba ta dawo hayyacinta ba, sai dai Hadiyya da ta fara nutsuwa tana ta basu labarin abinda ya faru da daɗewar da Hamdiyya ta yi da Huzaif ba tare da tasan wane ne shi ba.

Sai wuraren ƙarfe tara na dare ta buɗe idanuwanta suka sauka kan matar Kawu da ke gyangyaɗi, ai sai ta miƙe firgigit ta rungumeta tana sakin kuka.

“Yanzu da ni ce na yi amfani da yankin da shi kenan ni zan ɓace ko. Wayyo Huzaif! Na tabbata yaudararsa suka…”

“Ki ka ƙara kira mini wannan sunan sai na tattakaki a wurin nan wawiyar yarinya kawai.”

Kawu da ke gefe a tsaye ya faɗa a fusace yana zare takalmin ƙafarsa ya yi gunta. Da sauri matar ta sha gabansa tana girgiza masa kai.

“Kinsan Allah Hanne banda dare ya yi da a yanzun za ta bar garin nan, ta tafi can Kaduna gurin Iya ta zauna kafin lokacin aurensu da Haruna.”

“A dai yi haƙuri zuwa safiyar, har da yarinta fa Maigida.”

“Ba wani yarinta sai wannan shegiyar bokon da na bar ta ta yi, ai duk  Haruna ya jawo na sanyata, sai yanzu nake nadamar dama tun tana 12 na kulleta a ɗakin mijinta, za ki bar kallona ko sai na fauɗeki shashasha wacce aka yi rabon kunya da mutunci babu ita.”

Da sauri ta sauke idanuwanta ƙasa tana daɗa ɓoyewa  a bayan Haule.

Shiru suka yi gabaɗaya har ya gama ɓaɓatunsa ya fice.

Sai dai fa da sassafe ya ce ta haɗa kayanta su tafi. Haka ta haɗa tana ta kuka, ita ba abinda ya fi ɗaga mata irin ta samu damar ganin Huzaif kafin su tafi. Ta sani har a ƙasan zuciyarta da ace Huzaif yasan Manager yaudararsa ya yi ba zai taɓa ma karɓar ƙyallen ba. Ita tsoronta ɗaya ma kar su gaji su zuƙe jininsa ba tare da ya sani ba. Tuna hakan ya sakata ƙara rushewa da kuka tana ɗora hannu aka. Kawu ya ja tsaki mai ƙarfi yasa hannu ya zuba mata wani ranƙwashi a tsakiyar kai. Da sauri ta haɗiye kukanta sai ajiyar zuciya har suka isa Kadunan.

Ko da ya danƙata a hannun Iyan da ita kaɗai ta rage musu babba a zuri’ar, ƙanwar Uba take gare su. Ya daɗe yana roƙonta da ko shago kar ta sake ta tura ta, ta barta anan gida ta sakar mata dukkan aikace-aikacenta. Anan suka yi sallama ya juya ba tare da ƙara duban shiyyar da Hamdiyyar take ba. Ganin haka ya saka jikinta sanyi ta miƙe da gudu tasha gabansa tana sanya gwowowinta a ƙasa cikin hawayen da ta kasa hana zubarsu.

“Kawu dan Allah kar ka tafi, Allah ji nake kana tafiya zan mutu, Kawu ka yafe mini domin Allah ka ji ƙaina ka rabani da nan.”

Zuciyarsa ta tsinke, jikinsa ya yi sanyi gabaɗaya, sai ya yi tsai! Yana duban kyakkyawar fuskarta a kaikaice.

“Hamdiyya, me kika nema kika rasa a gurina da ba za ki iya yi mini abinda nake so ba?”

“Babu Kawu, ka yi hakuri na daina, zan yi duk abinda kake so, amma ka maida ni gunka, ba na son hutun nan.”

“Dainawa ɗaya ce ita ce ki haƙura da wannan yaron ki bar tuna sa, wallahi kinga da girmana na rantse miki ba alheri ba ne gareki. Yanzu idan kika ce mini kin haƙura da shi ba zan barki anan ba tare za mu koma. Za ki iya haƙura?”

Shiru ta yi sai wasu zafafan hawaye da ke sintiri a saman fuskarta.

“Magana nake miki, za ki iya haƙura da shi?”

“Kawu na tabbata shi ma yaudararsa aka yi, bai san…”

Ganin fuskarsa ta canja ya sakata haɗiye kalamanta ta miƙe ta juya kawai zuwa cikin gidan.

Ya daɗe tsaye yana ƙissima yanayin yarinyar, yana ji kamar zai yi wani kuskure, kamar ya bata dama ya yi magana da yaron ko zai gane wani abin. Sai dai kuma da ya tuna wasiyyar mahaifinta sai kawai yasa kai ya fita daga zauren yana mamakin abinda ya sanya jikinsa rawa tako’ina.

Ya daɗe zaune daga can nesa yana hango gidan kafin ya tashi ya tafi a hankali tamkar mai jiran tsammanin wani zai iya kiransa, sai dai har yasha kwanar layin hakan ba ta faru ba, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana jin wani yanayi marar daɗi na ratsa shi, kafin kuma ya ɗaga ƙafa zuwa tashar da za ta sada shi da garinsu.

Wani abu da bai sani ba shi ne, ya kawo ta inda ba zai ƙara tozali da ita ba har abada! Ta yiwu da ya yi haƙuri ya barta a gabansa da ƙaddararta ba ta yi musu yankan ƙauna ba!


*****

A cikin wata biyun da ta kwashe gaban Iya ba ƙaramar gwagwarmaya aka sha ba. Sai dai a hankali ta fara manta wasu abubuwan da yawa, yayin da ta wani ɓangaren take gasgata zancen iya da kullum ke jaddada mata Huzaif yaudararta ya yi zai maida kanta kuɗi, shi ɗin ɗan mafiya ne matsafi, da ace ba shi ba ne da tuni ya neme ta ko da kuwa a birnin sin take ɓoye. Iya har alƙawari ta mata idan har Huzaifu ya bayyana kansa a gidanta kafin cikarta mako huɗu ita da kanta za ta sanya a ɗaura musu aure. Sai dai har watan ya ƙare babu shi babu alamarsa. Wannan abin ya ɗaga mata hankali ta yadda ba ta iya kwanciya saman filo ba tare da ta jiƙe shi da ruwan hawaye ba, tana tuna kalamansa, tana tuna sanyayyar muryarsa a yayin da yake jaddada mata irin soyayyar da yake mata, tana tuna kome na halittarsa. Kai tasha ta zo cin abinci ta ganshi tsaye a gabanta sai ta miƙa hannu za ta taɓa shi ta ji ta cafki iska.

Ita fa babban burinta shi ne ta yi tozali da shi ta tambaye shi dalilinta na zaɓarta a matsayin abar wasansa, ta kuma tabbatar masa da har ya mutu ba zai taɓa samun wacce za ta ƙauna ce shi domin Allah irin ta ba, wani irin zafinsa ta fara ji da jin haushinsa, a karo na farko tun haɗuwarsu sama da shekara gudu da ta ji haushinsa cikin ranta.

*****
A hankali take takawa zuwa ‘yar kasuwar da Iya ta aiketa siyo bushasshen kifi, ranta a cunkushe yake sai harare-harare take ita kaɗai tana zoɓara baki sama. Cike take da jin haushin yadda har wata biyu Kawu bai zo ya ganta ba bare ta ji inda maganar aurenta da Yaya take. Ji take ita ma idan za ta shekara anan ba za ta taɓa nemansu ba suje can su ƙarata. Can kuma wata zuciyar ta zungureta da dama iyayenta suna nan…Tuna hakan yasa ta ja ta tsaya a gefen hanya a cikin idanuwanta take hasko yadda suke ƙaunarta, tana jin da ace suna nan da ba za su taɓa hana ta abinda take so ba, ba za su iya mantawa da ita har tsayin wata biyu ba. Hawaye suka fara ɗiga a gaban hijabinta, ta yi sauri ta ja gefen hijabin tana sharewa. A sannan ne ta ji an finciketa ta baya an jata da ƙarfi zuwa wani lungu da baya ɓullewa, ta buɗe baki za ta kwala ihu ta ji anyi wuf! An toshe mata bakin an haɗata da garu. Runtse idanuwanta ta yi da ƙarfi tana jin yadda zazzafan hucin mutumin ke sauka a fuskarta. Jin shiru ba a ce kome ba sai toshe mata baki da aka yi yasa ta buɗe idon ta sauke su a cikin nasa da suka canja kala sosai da wani irin yanayi da ta kasa wassafa shi.

“Huzaif!” Ta furta can a ƙasan maƙoshi, a yayin da shi ma ya zame hannunsa yana dubanta a sanyaye.

“Bazan iya jurewa ba, me yasa kike kuka, cikin satin nan kaf ina bibiye da ke kullum sai kin yi kuka, ni ne ko?”

Kasa magana ta yi jin ya ma raina mata hankali. Da ƙyar ta danne zuciyarta tana jin ba za ta ƙara zubar da hawaye a gabansa ba.
“Ki yi hakuri…Ban sani ba, ban san kina nan ba, ban san me ya faru ba. Allah shaida na wahala gun nemenki Hamdiyya..”

Ya furta yana ɗora hannunsa a kafaɗunta.

Cije bakinta ta yi tana jin wani zafin rai na mamayarta, da ƙarfi tasa hannuwanta ta ture nasa tana dubansa a zafafe, sai dai fa ta kasa ɗauke idonta kansa, haka ta gagara buɗe baki ta ce wani abu, gani take tana furta ko menene zai ga logonto, dan haka ta yi gefe za ta fice daga lungun ya yi saurin saka hannayensa ya dafe bangon ta zama a tsakiyarsa har suna jin zazzafan hucin junansa.

“Ba za ki yarda ba ko…? Ba za ki sake yarda da ni ba ko…? Me zan miki ne…?”

Ya yi shiru yana tura laɓɓansa na ƙasa cikin bakinsa.

A idonta sai taga ya mata wani irin kyau mai sanyin kallo, zuciyarta ta fara nutsuwa, sai kawai ta kauda kanta gefe tana jin ta faru ta ƙare…
“…In rantse miki Hamdiyya…?”

“Wallahi summa tallahi bansan kina garin nan ba sai a cikin satin nan. A tun ranar da muka rabu ban ƙara samun lafiya ba sai a…”
Kayya! Zo muje dai…”

Sai kawai ya jawo hannunta suka fito daga langun ta kuwa biyo shi kamar jela, ganin suna dosar titi ya sa ta fara ƙoƙarin tirjewa.

“Ko da ace ni abinda kike za ta ne ba zan taɓa sai da jininki ba. Ko da ace Baba nane shugaban masu tsafi na duka duniya ba zan taɓa bari wani ya taɓa ki ba balle ni kaina. Ko da kuwa ace a dalilinki ni zan rasa tawa rayuwar ba zan iya ba Hamdiyya ba, ba zan taɓa iya cutar da ke har haka ba. Ki yarda da Ni!”

A cikin sautinsa ta gama gasgata dukkan abinda ya faɗa ya fito ne tun daga lungun zuciyarsa. Jikinta ya yi sanyi gabaɗaya, a karo na farko da ta ji ta munafunce shi da har ta iya zaton zai iya yaudararta. Sadda kanta kawai ta yi ƙasa ta ci gaba da maida sahunta a duk inda ya ɗauke nasa.

Basu wani daɗe suna tafiya ba suka zo inda ya sauka. Gidan ya ƙeru sosai har sai da ta ɗago da mamaki tana kallonsa, ya mata wani murmushi mai kama da yaƙe ya buɗe gidan suka shiga. Tsayawa ta yi tana ƙarewa tsararren falon kallo, shi kuma ya tafi ga fridge ya ɗauko ruwa ya zauna yana sha.

“Bari ki ga na fita na kira yaro a gabanki zan aike shi ya samo miki ruwan sha, na san ba lalle ki sha na gidan nan ba.”

Yi ta yi kamar ba ta ji shi ba ta miƙe ta isa ga fridge ɗin ta buɗe ta ɗauko ruwan mai sanyi ta fara sha. A hankali ta lumshe idanuwanta  jin yadda sanyin ruwan ke tafiya da duk wata damuwarta. A daidai nan ta ji tsayuwarsa kusa da ita, sai kuma ya sunkuya a gabanta hannunsa ɗauke da Alƙur’ani mai girma.

Da mamaki take dubansa ganin ya dafe ƙur’anin yana dubanta.

“Na rasa me zan yi ki dawo da kallonki gareni irin na baya… Na rasa me zance ki gasgata dukkan abinda zan furta. A cikin idanuwanki nake hango rashin yardar ki gareni, dan haka zan miki rantsuwa da abinda ba a taɓa wasa da shi a kowacce irin saɗara… Ya Allah ina roƙonka da girman littafinka mai tsarki, idan har nasan abinda ya faru da wannan baiwa taka ya Allah ka…”

“Wai menene haka! Kasan me kake yi kuwa…?”

Ta furta da tsawa tana sanya hannu ta ƙarɓe ƙur’anin ta ajiye shi a gefe.

“Saboda ni sai ka rantse da Alƙur’ani kasan girman hakan kuwa?”

“To wai ya kike so na yi? Kinsan yadda nake ji a duk lokacin da na dubi cikin idanuwanki na ga tarin shakku da zargi?”

Ya furta a marairaice yana yatsine fuska kamar mace.

Jikinta ta ji ya mutu gabaɗaya da wannan salon nasa, ba shiri ta lalubi kujera ta zauna tana doka masa harara.

Ganin haka ya sa shi ma ya miƙe ya zauna kusa da ita, ta matsa ya matso ta ƙara matsawa ya ƙara matsowa har sai da suka kai ƙarshen kujerar da take haɗe ga bango. Ta yi wuf! Za ta miƙe yasa hannuwansa biyu ya jawota ta faɗo gefensa.

“Wai me ye haka ne? Kar ka ƙara taɓani Ni ba halalinka ba ce, wai ma baka san an ɗauran aure ba ne?”

Ta furta a tsiwace.

Bai ce kome ba sai tagumi da ya rafka hannu bibbiyu yana dubanta.

Share shi ta yi ganin haka yasa ya sauke tagumin ya numfasa.

“Ki yi hakuri… domin Allah ki yi yafe mini.”

Sauke ajiyar zuciya ta yi tana ƙare masa kallo, sai yanzu ta kula da ramar da ya yi sosai. Jikinta ya daɗa sanyi tana jin kamar duk ita ce silar damuwarsa.

“Ka daina ba ni haƙuri dan Allah, na fahimta fa, nasan kome, koma ince na fika sanin ba za ka taɓa iya aikata haka gareni ba, rai nane ya ɓaci da naga har wata biyu baka neme Ni ba Huzaif, ta yaya zan nutsu? Ta yaya ba zan yarda da saka hannunka ba?”

“Ban san haka ta faru gare ki ba sai a satin nan biyu da suka gabata da na dinga zarya unguwarku ko zan ganki sai na haɗu da wannan ƙawartaki ta makaranta, daga yanayin yadda na ga tana dubana a tsorace nasan wani abu ya faru. Da ƙyar na samu ta saurareni ta ba ni labarin abinda ya faru. Kinsan a tun ranar da muka rabu ban ƙara yin lafiya ba sai bayan wata guda. Ni kaina ba abinda ke daɗa zafafa jinyata sai rashin ganinki tsawon wannan lokacin ba ki biyo sahuna ba kinga lafiya alhali duk sati muke haɗuwa. Babban tashin hankalina kar ya zamana anyi miki auren ne. Ban zaci zan tashi daga jinyar ba duk da bansan mafararta ba. Haka nan na wayi gari na ji bayana ya riƙe, jikina ya saki na gagara ko juyawa balle na iya tashi. Kwanana biyu a kwance cikin kashi da fitsari kafin Allah ya jeho wani maƙocina. Shi ya tsaya kai da fata wurin ganin na warke duk da  da ƙyar aka iyi samun maganin lalurar, a cewar masu maganin wai jifa na aka yi.”

Ya yi shiru ganin har ta fara sharce kwalla.

Suka yi zuruu na tsayin lokaci kafin ita ma ta bashi labarin duk abinda ya faru har haushinsa da ta ji.

“Hamdiyya ki yafe mini duk ni ne silar kome da na buɗe miki lararuta. Yanzu da wani abu ya same ki shin ta yaya zan iya yafewa kaina…?”

Ya numfasa idanuwansa sun kaɗa jajur.

Wani murmushin ƙarfin hali ta masa tana girgiza kai.

“Kar ka ƙara tuna hakan balle ka kalleni da shi. Idan har za mu yi zaman da za mu ɓoyewa junanmu damuwarmu babu gaskiya kenan. Na roƙe ka da ka ɗauki hakan a ƙaddarar soyayyarmu, mu kuma gode Allah da wani mummunan abu bai faru gare mu ba, gobe sai ka ga ya saka mana da abu mafi alherin wannan, kar dai ka ƙara taka inda manager take, dole kuma ka dage da addu’ar neman tsari ga ire-irensu. Sannan roƙona ɗaya gare ka, dan Allah Huzaif ka duba maraicina, ka dubi yadda Kawu ke ƙoƙarin raba ni da kai amma na ƙi hakan saboda ƙaunarka ta domin Allah da nake yi, ka dubi girman zatin Allah kar ka taɓa yaudarata, idan ma kana da niyyar hakan ka tafi tun yanzu, ka tafi wuri mai nisa can da ba zan ƙara ganinka ba, idan ka yaudare ni a bayan wannan yardar da na baka bansan ya zan yi da rayuwata ba, wani irin so nake maka da ba na fatar na aure ka ba tare da na rage fiye da rabinsa ba…”

Ta yi shiru tana kafe shi da idanuwa, tana kula da sa’adda wani abu mai nauyi ya gilma a cikin idanuwansa, sai dai fa kafin ta farga ta jita a tsakiyar ƙirjinsa ya ƙanƙameta. Mutsu-mutsu ta fara za ta kwace ya ƙara matseta tamkar zai karya ƙasusuwanta.

“Ki bar ni dan Allah, kin ji?”

Ya furta da wata irin murya da bata san shi da ita ba, sai taji kamar ba Huzaif ɗin da ta sani ba, kamar an mata musayansa da wata halittar irinsa mai tarin daraja gunsa.

Sassauta riƙon da ya mata ya yi yana shafa bayanta. A hankali ya buɗe tafin hannunsa wata ‘yar ƙaramar ƙwaya ruwan ɗorawa ta bayyana. Tsura mata ido ya yi yana ƙoƙarin maida kwallar idonsa da ya rasa dalilin tahowarta a daidai lokacin da dukkan burinsa ke gabda cika. A ransa yake jin tabbas da waccar dabarar gwara wannan tafi kusa da tafarkin tsira, tafi kusa kuma da samun nutsuwa a zuciyarsa. Zare jikinsa ya yi da ga nata ya ɗago yana kallon cikin idanuwanta har sai da ta ji kunya, a sannu ya buɗe baki ya hure mata idon. A tare suka dubi juna da wani tattausan murmushi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Hakabiyya 5Hakabiyya 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×