A can cikin wani ɗaki da aka gina a ƙarƙashin ƙasa a tsakiyar wani baƙin daji dake yamma da wata kushewa. Wata ƙwarya ce da ke cike da wani baƙin jini ta fara girgiza tana darewa, jinin cikinta ya fara toroƙo yana zaɓalɓala tamkar yana bisa garwashi, kafin kuma ta tarwatse gabaɗaya jinin ya fallatsa a ilahirin farin mayanin da aka kewaye ɗakin da shi, a sannan ne Ragon ya bayyana yana kuka, sai kuma ya yi tsit! Yana tsurawa mutumin da ke zaune acan kursuwar ɗakin kan wata baƙar kujera ido. . .