A karo na farko da wani tsoro ya tsirgata ta ƙanƙame jikinta tana waige-waige. Zuciyarta da dukkan tunaninta sun gaza gasgata hakan a mafarki. Tabbas a jiya da ta fita ta haɗu da Huzaif har sun yi zantuka masu yawa, gasu nan kwance cikin kwakwalwarta tamkar yanzu aka zuba mata su, sai dai fa ta kasa tuna yadda suka rabu da yadda aka yi ta dawo gida. To ko dai mafarkin ta yi. Da sauri ta runtse idanuwanta tana son tuna ko da wanda ya gansu tare a lokacin? Sai dai ta gaza tunawar. . .