Skip to content
Part 8 of 32 in the Series Hakabiyya by Fulani Bingel

A karo na farko da wani tsoro ya tsirgata ta ƙanƙame jikinta tana waige-waige. Zuciyarta da dukkan tunaninta sun gaza gasgata hakan a mafarki. Tabbas a jiya da ta fita ta haɗu da Huzaif har sun yi zantuka masu yawa, gasu nan kwance cikin kwakwalwarta tamkar yanzu aka zuba mata su, sai dai fa ta kasa tuna yadda suka rabu da yadda aka yi ta dawo gida. To ko dai mafarkin ta yi. Da sauri ta runtse idanuwanta  tana son tuna ko da wanda ya gansu tare a lokacin? Sai dai ta gaza tunawar. Kallon jikinta ta yi na ɗan lokaci kafin wani tunani ya tsirga mata ta yi ɗaki da gudu ta jawo hijabinta da ke saƙale a ƙofa ta fara shinshinawa, ta kuwa zuƙo daddaɗan ƙamshin turarensa da bai taɓa gushewa cikin tunaninta ba ko na habba. Da sauri ta zabura za ta kaiwa Iya ta ji ƙamshin ko ta gasgata, sai kuma ta yi turus! Tana tuna abinda za ta ce mata idan ta tambayeta yadda aka yi hijabinta ke ƙamshinsa. Sai ta ce mata me? Rungume juna suka yi?. Ko kuwa matashi ya yi da kafaɗarta?.

Aje hijabin ta yi tana sauke ajiyar zuciya jin kanta zai fashe da tunani. Wani Almajiri daya kwaɗa bara da ƙarfi ya sa ta miƙe ta saka takalmanta ta yi ƙofa da gudu bayan ta cewa Iya “Zan dawo yanzu.”

Hanyar kasuwa ta yi daidai inda ta haɗu da shi jiyan ta ja ta tsaya. Daga nan inda take tsaye tana iya hango lungun da ya tura ta. Hankalinta ta ji ya fara kwanciya ta doshi lungun a daidai inda ya tsaya ita ma ta tsaya tana shafa gun da wani guntun murmushi a fuskarta. Fitowa ta yi tuna tabbas za ta iya gane gidan nan mai kyau da suka je jiya. Ta kan titi suka miƙe suka yi tafiya kaɗan kafin su sha wani layi guda ɗaya sai ga gidan. Da sauri ta ɗaga ƙafa ta doshi titin ta miƙe shi samɓal! Tafiya ta dinga yi tun tana tunanin za ta ga kwanar har ta fara sarewa. Tun ba daɗewa ta isa ga wata ƙatuwar tanka da ta kula da ita a jiyan a bakin layin da suka shiga sai dai a yau babu wani layi kusa da Tanker. Haka ta dinga tafiya tana mamakin yadda layin ya ɓaci mata tun tana ganin tsilli-tsillin gidaje har ta fara shiga gonaki. Har azahar tana bulayi a cikin Kaduna sai dai ta kasa ganin ko me kama da gidan. Jin da ta yi a kowane irin lokaci za ta iya zubewa saboda yunwa da gajiya yasa ta samu wata gindin bishiya ta zauna tana sauke numfarfashi. Ƙafafuwanta masu kyau ta kalla ganin yadda suka yi futu-futu, ta bi jikinta da kallo duk ta fita a hayyacinta ga warin gumi da take yi. Ta tuna shekaru biyu baya sa’adda take yar ƙwalisarta kaf!

Makarantarsu babu mai kyawunta da iya gayu amma wai ita ce yanzu take yawo tamkar mahaukaciya a gari tana neman wanin da bai fi uban da ya haifeta ba. A hankali wasu siraran kwalla suka taho mata ta sa hannunta ta ɗauke a zuciyarta tana fatar ta ƙara haɗuwa da shi ko da kuwa ace ita ce haɗuwar ƙarshe da za su yi, ko da kuwa ace a cikin mafarkin ne ita dai tana son ta tambaye shi hanyar da za ta bi ta raba kanta da tunaninsa da dukkan soyayyarsa. Wasu kalamansa da suka mata  daɗi ajiyan suka yi sururu zuwa cikin kunnuwanta tamkar yanzu yake raɗa mata su. Ba zan iya jure kukan ki ba, ki daina ko ba domina ba….

Ai sai ta cigaba da hawayen tana waige-waige wai ko zai ji a jikinsa ya fito gareta yadda taga anyi hakan a wani Film Karan Arjun da ya fita kasuwa a shekarar da suke. Sai dai wayam hakan ba ta faru ba har hawayen suka ƙafe ta miƙe da ƙyar tana jin wani zafi a jikinta da har yanzu ta kasa gane daga inda yake ta doshi hanyar da za ta maidata gida.

Tana jin Iya na mata bambani ta yi shegewarta banɗaki. Wanka ta yo ta zo ta tuttura abincin da Iya ta sakata a gaba sai ta ci, ta gama ta yi ɗakinta ta lalubi hijabin nan da yake ƙamshin Huzaif ta maida shi jikinta tana sunsunarsa tamkar marainiyar karya.

A lokacin da ta ɗora ƙugunta bisa katifarta dan ta kishingiɗa, a sannan ne wani Almajiri mai kaifin sauti ya kwarara sallama.

“Wai ana sallama da Hamdiyya. Ya ce ace mata Huzaif ne.”

Kafin ɗan aiken ya fita ta riga shi isa ƙofar gidan. Sai da ta hange shi tsaye gefe ya ci uban ado yana ta walwali cikin wani jan yadi, da dai ta tabbatar shi ne sai ta ji kunya ta kamata kamar ta nutse gurin ganin ko takalmi babu a ƙafarta. Ta juya za ta koma ciki ta ɗauko ya yi hanzarin tare ta yana mai riƙo bakin hijabinta.

Zare nasa takalman ya yi ya aje gabanta, shi kuma ya koma can gefe saman dandamalin ƙofar gidan ya zauna.

Kallon takalman ta yi, kafin kuma ta ɗaga ƙafarta a hankali ta zura ciki. Tana gama zurawar ta ji gabanta ya yanke ya faɗi har sai da ta runtse idanuwanta ta buɗe su a hankali suka haɗa ido da shi ya sakar mata tattausan murmushi. Ga mamakinta sai ta ji kashi casa’in cikin ɗari na damuwarta ta gushe, haka da yawa-yawan tambayoyin da ta ƙunsu cikin bakinta sun lume a can wani guri da bata san ina ne ba, babu kome a gabanta da rayuwarta sai son sa da ƙaunarsa, babu kuma kome cikin kwakwalwarta sai son su rayu a haka tare har ƙarshen rayuwarsu. A sannu cikin rangwaɗa ita ma ta taka ta zauna acan ƙarshen dandamalin tana kallonsa. Ta buɗe baki za ta yi magana ta jiyo fitowar Iya nata bambamin faɗa.

“Bari na zo naga shi Huzaifun da ya tare mana ko’ina ya hanamu rawar gaban hantsi. Ke yanzu dan iya shege saurayi ya aika ki fito sai kuma ki riga shi ɗan aiken fita? Hamdiyya wannan wace irin asara ce? Shi namijin kike wa rawar ƙafa haka?” Sai kuma ta yi turus tana riƙe haɓa a bayan ta haɗa ido da Huzaif. Ta ƙara kallonsa sheƙeƙe tana taɓe bakinta da goro ya ɓata.

“Kai ne akewa kallon ɗan mafiyan?”

Ya sunkwi da kansa ita kuma ta ƙara taɓe baki.

“To banga kama ba sam wallahi…”

Ta waiga ɓangaren da Hamdiyya ke zaune suka haɗa ido ta zoɓara mata baki gefe.

“Ke yanzu dama wannan ɗan yalolon abin kike wa kuka dare da rana? To ai ko tsohon mijina Hamza da na bari saboda gajartarsa ya fi shi kyan gani da fasali, hala farar fatar da dogon hancin yawa nunannan karas da kwalakwalan idanuwan ke burgeki?Tirr! Da halinki ke kam, Ni wallahi na sha zan zo na ga jibgegin mutum da zan gagara tsayawa gabansa. Shi Kawun naki yanzu ko kunya bai ji ba ya ɗauko ki gari ya gari ya kawo ki nan saboda ɗan wannan yalolon bafillacen? Kai kuma…”
Ta waigo saitinsa.

“…Ta ce mini jiya kun haɗu, da gaske kun haɗun? Ya akai bata san ta dawo gida ba? Kai tsaya ma, faɗa mini gaskiyar abinda ya haɗaka da ƙyallen da aka ce ka bata ya ɓace da rago.

Ta ƙarasa tana jijjiga ƙafa.

Hamdiyya ta dube ta da mamaki tana ƙarasawa kusa da ita da sauri.

“Haba Iya baƙo ne fa?”

“Dillah rufe mini baki shashasha, baƙon gidanku…”
“Kai yaro kai fa nake sauraro, gwara ma ka faɗa mini gaskiya idan da gaske aurenta ka zo yi ni kaɗaice zan iya tsaya maka kan lamarin, dama can kai ne ka yi shiririta da baka je ka fara nemanta gurin manyan ta ba.”

Ya yi shiru har yanzu kansa a ƙasa.

“Auho na fahimta, ba za ka iya magana anan ba ko? To taso muje tsakar gida a saka maka tabarma ni ba baƙuwar zahi ba ce ai.”

Ya ɗago ya kalleta da fuskar mamaki, sai kuma fuskarsa ta faɗaɗa da murmushi.

“Wai Iya baki gane ni ba ne?”

Ta bishi da kallo sororo, Hamdiyya ma haka.

“Ni ne fa wanda jiya da kika fito nan ƙofa neman yaro sulɓi ya kwasheki za ki zame na tallafe ki? Kin tuna har kika ce Avoniki kika fito ki samu yaro ya siyo miki, na ce miki kar ki siya na yanzu sun ɓata shi har bugarwa yake, kika ce ke dai in siyo miki shi a haka, kin tuna har na kawo miki na tafi?Ina ga shi yasa duk daɗewar da Hamdiyya ta yi gurina jiya baki tuna ba, sai dai ita ce ban san meyasa ta manta ni da kaina na rakota gida ba. Sai maganar kifi shi ma kin manta a gabana naga wani yaro ya kawo miki kifin.”

Kai! Yaushe Iya ta yi maganar kifi ga Huzaif?
Hamdiyya ta furta ba tare da ta san sa’adda kalaman suka haɗa kansu ba. Daga yanayin furucin za ka gane itama  cikin zuciyarta take tambayar.

Iya ta yi azamar ɗago kanta tana zuba masa ido. Shi kansa ɗauke kai ya yi gefe yana sanya bayan hannunsa ya shafo sumursa. A sannu kuma sai ya juyo da fuskarsa cikin rashin walwala.

“Haba Iya ai nasan shi ma batun kifin za ki iya cewa kin manta, saboda ki tunani yasa na ambato miki har kifin da a gabana yaro ya danƙa miki shi a hannu, anan kam ai baki ambaci kifi ba.”

“A’a kai yaro kul! Ka yi mini ƙarya, ji da ganina ras suke bar ganina dattijuwa. Wanda na aika jiya ya za ai na manta fuskarsa, mutum ne mai ɗan girma da cikar kyawu. Kai fa jibeka yawa sandar rake, banda fala-falan kunnuwanka babu wani abu mai kauri a jikinka. To to gwara ma muryar taka na ji kamar na taɓa saninta.”

“Ahaf iya wallahi Ni ne! Kin tuna ina sanye da burgujejen wandon jinsi da ƙatuwar riga ina ga shi ya sa na cika miki ido. Yanzu kuma kin ga ɗan yalolon yadin dake jikina.” Ya ƙarasa yana nuna jikinsa.

“Ikon Allah! Aikuwa haka ne, oh ni Halimatu Ta Annabi da ɗimaucewa, kasan Allah sam ban gane ka ba. Ke maza shiga ki shimfiɗa masa tabarma a tsakar gida.

Wannan mutum ne mai girma gurina. Jiya da ba dan shi ba da tuni ina nan kwance gurɗe da ƙafa.

Huzaif ya yi murmushi sosai har wushiyarsa ta bayyana.

“Iya ai ba lefinki ba ne, wannan dai Avonikin ne da na hanaki saye. Ai yanzu kayan bugarwa suke sawa sosai ciki. Da ka shafa sai kan ka ya juya har sai ka yi barci za ka samu sa’ida.”

“Ai bari fa yaro, yanzu ina shiga zan ɗau shege na jefa cikin masai.”

Suka shige gidan gabaɗaya. Iya ta ƙarasa ga randarta ta kwarfo ruwa ta aje gabansa. Kana ta ɗauko kujerarta ‘yar tsugonne ta zauna kanta ta fara ɓarar gyaɗarta tana kallonsa bakinta nata motsi tsabar murna.

Hamdiyya ma can gefen tabarmar zauna tana ta satar kallonsa.

“To ina saurararka yaro, faɗa mini dukkan gaskiyar abinda ke faruwa.”

Ta furta a bayan ta hambuɗa ɗanyar gyaɗa biyar cikin bakinta.

Nan ya tankwashe ƙafa ya kwashe kaf! Labarin da ya bawa Hamdiyya ya bata. Tun iya na gyaɗa kai can sai gata tana sharce hawaye da facar hanci.

“Amma su Manajan nan naka anyi tsinannu. Haba shi ya sa na ganka a bushe ashe ciwo kasha har ka yi rama irin haka. Sannu ka ji, da sannu Allah zai maka sakayya. Kai dai kar ka sake ka ƙara kusantar ko garin da suke, ka yi zamanka nan ga itatuwa nan zan haɗo maka ka dinga hayaƙi kana wanka da su, ka yi ta addu’a sai ka ga Allah ya kare ka daga sharrin magauta. Hamdiyya kuma in sha Allahu rabonka ce, ni da kaina zan yiwa shi Kawun nata  magana, dama duk rashin zama a tattauna da kaine. Sai ku ci gaba da kula Allah ya tsare ku daga dukkan abin ƙi.”

Ta ƙarasa tana miƙewa ta faɗa rumfarta.

Suka dubi juna a tare a yayin da wani shauƙi ya ɗebe su ya yasar gefe. Matsowa ya yi kusa da ita zai mata magana ta yi azamar miƙewa tana dosar ɗakinta. “Bari na ɗauko maka darduma ka yi sallah, maghriba ta yi tun ɗazu.” Dariya ya mata ya miƙe shi ma ya ƙarasa inda buta take.

Yana idar da sallar ita ma ta fito suka yi tsaye a cikin duhun maghribar suna kallon juna cike da zallar ƙauna. Ya matso kusa da ita ta yi saurin kewaye shi tana yin hanyar ƙofa. Da hanzari ya biyo bayanta shi ma.

“To me ye na wani fitowa, can ya fi daɗin hira ai.”

Ta harare shi kamar idonta zai faɗo cikin duhu.

“Na gode Allah da nake da sauran kunya, Iya fa za ta iya jinmu.”

“To wani abu aka ce miki zance?”

“Ni da na san hali.”

Ya matso kusa da ita ta yi azabar zaunawa bisa tudun bayanta.

“Ke wai lafiya?”

Ta yi shiru tana ɗaga kanta sama ta kalli manyan taurarin da suka ƙawata sararin samaniyar, a sannu ta ƙanƙame jikinta sa’ilin da wata sassanyar iska ta fara ratsa ɓargonta.

“Huzaif!…”

“…Kana jin me nake ji?”

“Menene Hamdiyya?”

“Wani iri wallahi, ban sani ba, kalli jikina har rawa yake, ina jin kamar farin cikin da nake ciki ya fi ƙarfin hankali da tunanina, kamar ba zan ƙara rayuwa da kwatankwacin farin ciki irin wannan ba, shin wai wane irin so nake maka ne? Shin yaushe har ya shige ni ya ginu a cikin rayuwata haka a tsayin shekara guda kawai? Kasan girmar fargabar da nake ciki ɗazu? Ban taɓa yini mai nisa da tarin ƙunci ba irin na yau ba kuma na fatar sake maimaita irinsa. Huzaif kewaya gonaki da kwangaye da kududdufai na rinƙa yi ina neman kome sunanka ne tamkar mahaukaciyar da hauka ya shigeta a cikin daƙiƙa guda da ɗaura aurenta. Shin anya akwai adalci a irin wannan son da nake maka? Anya baka cikin ƙaddarar rayuwata da za ta girgiza ni? Na ji ance kowane bawa yana da irin tasa ƙaddarar da za ta taɓa shi kafin ya kai ga kushewarsa anya ba kai ne tawa ƙaddara ba…?Kana kuwa jin irin abinda nake ji a yayin da baka gaban idona? Kana kuwa jin irin ɗacin da nake ji a yayin da zuciyata ta kasa jin haushinka? Ko kasan har a cikin kwanon shan ruwana da fuskarka nake tozali ? Ko kasan a gabaɗaya barcina tare da kai nake yinsa cikin mafarkina? Kana kuwa jin…” Sai hawaye zurr! Ta kasa ƙarasawa, ta ja hanci tana kallon yadda ya yi nisa a wani nisantaccen yanayi.

“Huzaif ka nawa Allah ka faɗa mini yadda zan bar sonka, ka nawa Allah ka koya min yadda zan tsaneka.”

“Da na yi miki me Hamdiyya?”

“Da nake sonka fiye da kaina.

Da nake maka son da ba na iya jin zafinka, ba na iya tambayarka, Huzaif! Ga fa gaskiya ƙiri-ƙiri ina gani a cikin idanuwana na kasa furta ma ita. Ga wata daɗaɗɗiyar tambaya ina jinta tana kewaya cikin kwakwalwata da dukkan ɓargona na kasa furzar ma ita, shin wata irin ƙauna nake maka marar algus?.”
“To ni kuma ya kike so na yi da raina a yayin da kika tsaneni? Hamdiyya baki fa kika fini da hanzarin bayyana abu. Da kinsan abinda ke ƙasan ruhina game da ke da duk ba ki damu ba kina jin kamar ke kaɗai ke jin abinda kike ji. Shin wai me kike so na miki ki yarda ina miki ƙaunar da baki yi mini irinta?.”

“Ka turo iyayenka gobe, jibi a ɗaura mana aure.”

Sunkuyowa ya yi daidai saitinta yana kallon idanuwanta masu maiƙo da suka canja kala tsabar kuka.

“Ba zai yiwu ba, ba zan miki ƙarya ba ban zo rayuwarki da wasa ba, banda ma wannan damar, wallahi summa tallahi da ina da ita a yanzu ma zan iya aurenki!”

Wani danƙulallen abu ya tsaya mata a maƙoshi, ta gaza magana sai haɗiyar zuciya take.

“Hamdiyya wallahi fa na ce miki, ki mini magana mana.”

“Amma fa kamar watannin baya kai da kanka kake roƙona za ka turo gun Kawu?”

Ta furta kalmomin da ƙyar tana tsare shi da idanuwa.
“Hamdiyya rantse miki fa na yi ba ni da wannan damar yanzu, ki yarda mana!”

“To wai sai yaushe kake da damar?”

“Nan da wata biyu, na miki alƙawari nan da wata biyu za mu yi aure.”

“Alƙawari fa yana da nauyi?”

“Na sani Diyya, shi yasa na ɗaukar miki abu mai nauyin dan ki yarda.”

Ta yi masa murmushi tana sanya hannu ta rufe fuskarta.

“Yi hakuri na takura maka ko?”

Ya yi murmushi mai sauti.

Ni zan dawwama baki haƙuri ai.

“Kasan har na fara tunanin sunan ɗan mu?”

Ya miƙe tsaye yana zare ido da mamaki.

“Ahh bari na tafi, ba za ki lalata ni ba tun yanzu. Yarinya ƙarama da ke kin iya jawo zantuka kala-kala, wai ina kike koyo?Na san dai ba wannan aka koya muku a makaranta ba.”

Ta miƙe ita ma tana dariya.

Tunda Kawu ya kawo wata ‘yar ƙaramar tv nake kallon india a wata tasha.

“Ah lalle ba mamaki, ni ma da can na taɓa zuwa wani gari naga ana kallo a majigi.”

“To me za mu sakawa Babynmu?”

Ta furta tana ƙunshe bakinta da dariya.

“Na baki wuƙa da nama, me kike so a saka?”

“To yanzu mu yi hasashen ga Babyn a hannunka, sai ka ɗaga yaron haka..”

Ta yi wani irin juyi tana cilla hannunta sama. “Sai idan macece a saka mata sunan Umma… Yauwa inji ma mene sunan Ummanka?”

“Hamdiyya.”

Ta kwalala ido da zallar mamaki.

“Dan ALLAH da gaske?”

Ta furta tana riƙe haɓa.

Shi ma ya riƙe haɓar irin yadda ta yi.

“Da gaske mana, sunanku ɗaya, yanayin kyawunku iri ɗaya, har tsayinku ma ɗaya, dan haka nake mugun ƙaunar kome naki.”

“Taɓ! Amma baka taɓa faɗa mini ba ko da wasa.”

“Amma ke ma baki taɓa tambaya ba ko da wasa.”

“Allah sarki Umma har na ji ina ƙaunarta.”

“Allah sarki ni har na ji ƙaunarki ta ninku a zuciyata.”

“Huzaif ka bari mana…”

Ta furta tana miƙa hannunta ta shafo wani zobe a hannunsa da ke ta walwali, sai dai kafin ta cire hannun ta ji kamar an kira sunansa da ƙarfi cikin kunnuwanta.
Ta wawwaiga.

“Wai baka ji an kira ka ba?”

Ya jujjuya kai alamun mamaki.

Ya buɗe baki zai yi magani ya ji ta riƙe shi tana zare ido. “Kai wallahi kiranka ake amma tunda baka san waye ba kar ka amsa, ance ba a amsawa Aljanu ke kira, wai cewa ake yi aniyar ku ta biku matsiyata.”

Ya mata murmushin ƙarfin hali a lokacin da ilahirin jikinsa ya girgiza yana masa wani irin ƙaiƙayi.

“Bari na je Hamdiyya sai gobe..”

Ya furta yana juyawa cikin hanzari, da sauri ta riƙo rigarsa tana kallonsa a marairaice.

“Huzaif dan Allah kar fa ka ɓace mini Ka ƙi dawowa.”
Ya janye rigarsa da ƙarfi idanuwansa har sun yi ja.

“Hamdiyya ki tafi na ce miki kullum zan ringa zuwa!!”
Daga haka ya falfala da gudu ya sha kwanar da za ta fidda shi bakin titi. Jikinsa na rawa ya tsaya jikin wani kango ya zura hannunsa a aljihu ya zaro kwandala ɗaya ya jefar nan gabansa, ya zuge tazugensa ya tsilala fitsari kanta, yana gamawa wani hayaƙi ya ratso daga jikin kwandalar ya lulluɓesa, a take suka ɓace bat!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Hakabiyya 7Hakabiyya 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×