Cikin watanni biyu sun daɗa wata irin shaƙuwa, dan hatta Iya ta shaƙu da Huzaif ta yadda har kwanon abinci ta masa a gidanta. Ya zama yaronta ta kowane ɓangare dan daidai da aiken kasuwa shi take bawa. Wankinta da duk wani abu na wahala shi yake zuwa da kansa ya zage ƙarfinsa ya yi mata.
A yanzu ba tada buri irin taga anyi aurensa da Hamdiyya, sai dai fa wani abu da ke da ɗaure kai shi ne, a duk lokacin da ta yi niyyar zuwa Kano gurin Kawu ko yi masa aike game da batun. . .