Skip to content
Part 9 of 32 in the Series Hakabiyya by Fulani Bingel

Cikin watanni biyu sun daɗa wata irin shaƙuwa, dan hatta Iya ta shaƙu da Huzaif ta yadda har kwanon abinci ta masa a gidanta. Ya zama yaronta ta kowane ɓangare dan daidai da aiken kasuwa shi take bawa. Wankinta da duk wani abu na wahala shi yake zuwa da kansa ya zage ƙarfinsa ya yi mata.

A yanzu ba tada buri irin taga anyi aurensa da Hamdiyya, sai dai fa wani abu da ke da ɗaure kai shi ne, a duk lokacin da ta yi niyyar zuwa Kano gurin Kawu ko yi masa aike game da batun sai ta kama wata zazzafar jinya ko kuma wata nannauyar mantuwa ta sameta. Ga shi dai duk mako biyu Kawun ke yi musu aiki na kayan masarufi sai dai fa ta gagara faɗawa dan aiken Kawun ko da ta yi niyya, haka ta gagara ko da aikawa ne a turo mata shi, shi kansa ta rasa dalilinsa na kawo mata yarinya ba tare da ya ƙara bi ta kanta ba sai tarin aiki.

A yanzu da take zaune saman ‘yar kujerarta ta tsugunne abinda ke ta zungulinta kenan, so take ko gobe ne ta tafi can sai dai jin da ta yi zazzaɓi ya fara rufeta ya sakata zama nan gurin tana saƙar zuci. Haba watanni kusan shida kenan fa da zuwanta har sun shiga sabuwar shekara sunci wata guda cikinta ba wata magana da aka tsayar. Haka ɓangaren Harunan da ake cewa an bawa mata, tsawon lokacin nan bai tako gidansu ko sau ɗaya ba dan ganin matar da aka bashin. Taja tsaki ita kaɗai.

Sallamarsu ta ji ta ɗago tana kallonsu suka haɗa ido da Huzaif haka nan ta ji faɗuwar gaba. Yaran sun yi wani irin kyawu sun murmure musamman Hamdiyya da ta yi wata irin cika fatarta na sheƙi. Wani tunani ya ɗarsu cikin ranta ita kaɗai ta kama jijjiga kai, sai kuma ta saka hannu ta yafitosu suka taho nan gabanta suka zauna. Ta dubi Huzaif. “Kana ji ko? Kawunku nake son gani bansan me ke sakani mantawa da lamarin naku ba. Dan haka gobe ka rakata can Kanon ta je ta sanar masa ina son ganinsa. Amma kar ka fito gabansa har sai na yi magana da shi, ka rakata kawai saboda ba na son tafiyarta ita kaɗai bata ma taɓa zuwa nan da kanta ba.”
Hamdiyya ta kama jijjiga ƙafa tsabar daɗi.

Iya ta harareta.

“Sai ki je kina masa rawar jiki ya ƙi dawowa da ke, kinsan dai halinsa sarai.”

Ta kwashe da dariya.

“Ah haba Iya kome fa ya ƙare.”

Tabbas kome ya ƙare.

Huzaif ya furta a hankali yana sosa ƙeyarsa.

“To shi kenan Iya Allah ya kaimu goben. Ke ki shirya da wuri ba na son tafiyar rana.”

Ta zoɓari baki gefe ganin yana mata magana yawa wani Baba.

Washegari da duku-duku ya zo suka tafi tasha, motar farko da suke su huɗu kacal ita ta fara tashi. Ta ringa zare ido ganin ita kaɗaice mace a motar. Huzaif da ke can gefe ya murmusa ganin yanayinta ya dawo gefenta da zama. Sai sannan hankalinta ya kwanta ta ɗan kishingiɗa tana kallon taga kunnuwanta na zuƙo mata wata hira mai daɗi da ke wakana tsakanin maza biyun da ke kujerar bayanta. Gudan babban burinsa ya je gida ya ga abinda matarsa za ta haifa, asalima sai ya je zai bada abin amfani, ya ci burin haihuwar nan ta yadda har adashin Shanu ya shiga dan ya yiwa matarsa kyauta da Saniya idan ta haifa masa ɗiya mace. Ɗayan kuwa burinsa guda ya je yaga mahaifiyarsa da ba tada lafiya ana ta masa aiken shi kaɗai take da burin gani.
Ta murmusa tana jin daɗin hirar tasu har tsakar kanta, ta ja green ɗin gyalenta ta lulluɓe fuskarta da haka barci ya ɗauketa ta ɓingire nan jikin tagar.

Ta yi nisa cikin barcin ta fara jin wani irin nishi haka kamar ana taɓa ta. Ta farka a tsorace ta ga Huzaif nata nuƙurƙusu ya haɗa zufa sharkaf. Ta waiga agigice ga mutane biyun nan ta ga suma barcin suke. Hankali tashe ta tallofoshi jikinta tana tambayarsa lafiya har hawaye sun fara zarya a kuncinta.

Ya ƙara riƙe cikinsa idanuwansa sun kaɗa jajur, da ƙyar ya iya buɗe baki ya ce mata, “ki cewa Direban ya tsaya na sauka cikina ke murɗawa sosai ina son yin amai.” A ruɗe ta waiga ga direban ta faɗa masa nan da nan ya tsaya. Ita ta tallafe shi suka fito daga motar suka yi can gefe nan ya sunkuya yana yunƙurin amai tana ta kwarara masa sannu cikin hawaye da majina. Da ƙyar ya samu ya yi wani irin baƙin amai ya ɗago a wahalce Yana dafe cikinsa. Ta bashi ruwan da direba ya bata ya kuskure bakinsa ta riƙo hannunsa za su koma motar, ɗaga ƙafar da za su yi suka jiyo ihun direban nata ƙoƙarin fitowa daga motar, wuta ce ke ci ganga-ganga wata irin wuta mai zafin da suke juyo hucinta har nan inda suke tsaye. Hamdiyya ta kwalla ƙara tana shigewa jikin Huzaif ganin yadda motar gabaɗaya ta kama da wuta tana ƙonewa har ta ƙone ƙurmuss ita da direban da mutanen nan guda biyu! Gaba ɗaya ta fita hayyacinta haka take ta bubbuga ƙirjinsa tana ihun kuka. Tunda ta zo duniya bata taɓa ganin tashin hankali muraran irin wannan ba. Ta ƙara ƙanƙame shi jikinta na kakkarwa ta ko’ina.

Sun daɗe tsaye a wannan halin yana dan bubbuga bayanta kaɗan kafin ta ɗago ta ƙara kallon ƙonanniyar _motar_ ta fashe da kuka.

“Shi kenan ko Huzaif sun mutu, a gabanmu sun ƙone, kai innalillahi wa inna ilahhir raji’un, Allah ka karemu daga sharrin ƙarfe, Allah ka raba mu da mutuwar azaba, Huzaif ƙonewa suka yi fa” ta sake fashewa da kuka. “Gudan kana ji matarsa ce za ta haihu ya ke maza ya je ya kai musu abinda za su yi amfani, gudan kana ji Mamarsa ce ba lafiya yake maza ya je ya dubo jikinta, shi kenan duka sun tafi ba tare da sun cika hadafinsu ba, kai innalillahi wa inna ilahhir raji’un.”

“Ki daina damuwa, duk wanda ya mutu anan ya cancanci ya mutun ne haka ni ne sila. Ba za a taɓa gane ba mu mutu a cikinsu ba, ba kuma za a taɓa rarrabe gawarsu ba. Sun ƙone kurmus Hamdiyya…”

Ta kalle shi da mamaki ganin ya yi maganar a sa’ilin da murmushi ke bayyana fuskarsa, tamkar ba shi ke halin ciwo yanzu ba.

“Ke ma yanzu za mu tafi inda ya dace ki mutu…”
Ta yi baya da ƙarfi ba tare da kwakwalwarta ta lissafi kome ba.

Ya ɗaga takunsa zuwa gabanta ya danƙo hannunta na hagu.

“Wannan shi ne sakamakon duk wata mace irinki mai maitar son kyawawan maza da rashin jin maganar na gaba da ita…” Ya furta yana zare zoben hannunsa ya zira a nata. A take jikinta ya saki gabaɗaya.

“Wannan kuma shi ne sakamakon nuna ƙaunarki gare ni.”

Ya ƙarasa yana aje mata ƙwandala a tsakiyar tafin hannunta. A take suka ɓace ɓat!

Ta fi ƙarfin minti goma tana sake karanta saƙon tamkar karatun Mauludi, sai take ganin kamar ba da hannunsa ya rubuta ba ko kuma ba ita zai turowa ba, sai dai fa daga Sururun Qalbyn naki da ya saka ta tabbata shi ne, haka saƙo nata ne ita kaɗai babu wata ma a zuciyarsa sai ita kaɗai ɗin! Wata dariyar farin ciki ta kwace mata ta rungume wayar tana tuna daɗewar da ta yi cikin soyayyarsa.

A tun ranar da ya fara shigowa cikin ajinsu ya gabatar da kansa ba ta ƙara samun nutsuwa cikin zuciyarta ba.
A da, kafin lokacin ta tsani karatun, asalima sai da ta shafe shekara guda a gida kafin ta yarda a sama ma mata Admission, sai da Zawwa ta mata jan ido tukunna, haka koda aka sama mata admission ta fara zuwa ba ta je da niyyar karatun ba, ta je ne da niyyar rage zaman gida kawai da hana kunnuwanta sauraron faɗan Mami da take yawan jaddada mata cikin burikan da ta ci na haihuwarta samun iliminta shi ne na farko, so take ta zama babbar likita irin yayanta  Haadiru da a sannan kaf! Kano babu kwararren likitan fiɗa irinsa, so take ta zama likitar zuciya wadda za ta iya tsaga ƙirji ta fiddo mata zuciyar mutum guda ta duba ta gani ko da ƙashi aka yi ta? A lokacin ƙunƙuni take tai ta mita Mami ta faye ƙullata da matsaya ɗan Adam.

Da ire-iren wannan burin ta shiga jami’ar, ita da ake fatar mata likita ta ɓige da Business Admin, nan ma Mamin murmushi ta yi ta ce duk ɗaya, nan gaba kaɗan akwai dukiyar da ita kaɗai take da burin ta tattala musu ita. To dai ta shiga da burin idan an gaji aka ga ba abinda take sai ɗaukar wanka ta shiga cikin aji Zero kwanya za a fiddata. Sai dai fa dukkan wannan tunanin nata kafin ta haɗu da shi ne, a bayan idanuwanta sun yi tozali da shi kome kuma na ƙudurinta ya canja take jin bata ƙi ta ƙarar da adadin da ya rage mata na rayuwarta cikin makarantar ba idan har shi yana cikinta, za ta iya rantsewa da Allah tafi kowa sammakon shiga jami’ar a yayin da ta san yana da lecture ɗin safe ko da kuwa a maƙotan ajinsu ne. Da ta kula yana da son mutum mai ƙoƙari da hazaƙa nan da nan ta fara nacin karatun dan kawai idan ya shigo musu ta fara rattafo masa tambayoyi. Da wannan ta fara cin kansa har take iya bibiyarsa a duk inda yake cikin makaranta yana yarfata da tsinkata cikin mutanenta ba tare da itan ta damu ba, ta san kome zai ƙare da zarar ta cafki zuciyarsa ta zama ita ce kaɗai ke jagorantar farin cikinsa, haka ma ƙawarta Hanipa ke yawan faɗa mata. To yau dai gashi da kansa yake nemanta da su hadu guri mai muhimmanci. Ta miƙe fuskarta fal murna ta shige toilet a ranta ji take suna haɗuwa ya furta mata yana sonta za ta ce masa ya turo gida kawai a saka musu lokacin aure. Da wannan tunanin ta gama uzurinta ta dawo ta kwanta tana jan blanket ta ƙudundune cikinta.

Washegari ta dinga yin  abu salalo-salalo a tsammaninta na ƙin zuwa makaranta da wuri, so take ya gaji ya kira ta dan kansa shiyasa ko reply ɗin saƙonsa taƙi yi tana jira sai ya kira ta. Tana sane ta tsallake lakcar da take da ita ta safe dan kawai ta ja masa rai da ajinta da ya daɗe da tafiya sai jiya take jin ya dawo.

Ta sake zoɓarar baki a karo na kusan ashirin a sa’ilin da ta ƙara kallon wayarta babu alamun kiransa zai shigo kai tun safe ma sai ka ce wacce tsiya ta ƙarewa babu wanda ya kirata har shegiyar ƙawarta Hanifa ba ta kirata ta ji yadda aka yi jiyan ba.

Miƙewa ta yi ta fara shirin tafiyar sai ga Mami ta shigo ta umarce da ta je masallacin ƙofar gida ta kira mata Baba Habu Maigadi. Har ta yi ƙofa sai kuma ta dawo ta ɗauki wayarta tana ma Mamin murmushi ganin ta bita da kallo tana taɓe baki, tasan halin Mamin yanzu za ta ce ta ajiye ita ko gani take yi tana matsawa daga kusa da wayar zai iya kira.

A sannu ta sauka zuwa ƙasan ta ƙarasa ga gate ɗin ta buɗe, wata ni’imtacciyar iska ta daki fatar fuskarta har sai da lumshe ido tana shaƙarta. Ga mamakinta sai ta ji ƙamshi-ƙamshi irin na turaren Huzaif, irin dai ƙamshin turaren nan da ta ji a yayin da ta tsaya ƙofar gidansa. Ta fara waige-waige idanuwanta suka yi tozali  da wata hamshaƙiyar baƙar mota tana ta walwali cikin hasken rana, sai dai gilasanta baƙaƙe ne ba ka iya ganin wanda ke cikinta. A jikinta ta ji ƙamshin nan daga motar nan yake. Haka nan sai ta ji tana son zuwa taga ko Huzaif ne ke mata wasa, dan haka ta ɗaga ƙafa da azama za ta ƙarasa gun sai kuma wayarta ta yi ƙara, jikinta na rawa ta ɗaga wayar tana ambaton sunansa a zahiri.

“Ba shi ba ne…”

Wata murya mai cike da karsashi da ɗaɗin sauraro ta furta cikin kunnuwanta. Ta ɗaga wayar da sauri daga kunnenta ta kalli number taga wata shegiyar special number ce ai sai ta maida kunnenta da azama tana ƙifta idanuwa.

“Ya Rabbi! You have a golden eyes like her, ki bar juya idanuwan nan dan Allah…

“Meee?”

Ta furta tana jin yadda ƙafafunta ke rawa, har yanzu kanta bai tsaya ba tsabar waiwaye, sai kuma ta tsaida idanuwanta kan baƙar motar nan tana jin kamar kowaye yana ciki.

“Uwa ma bada mama, uwar yarona marigayiya uwar kowa na nake nufi…”

Ya furta akwai alamun kiɗima cikin muryarsa.
“Wrong number…”

“A’a Please… Ba Baby Haƙabiyya ba ce? Ke ce dai, ke nake nema tun jiya da yamma.”

“An mini Miji wallahi…”

Tana jin yadda ya kwashe da wata matashiyar dariya.
“Hankali dai, ai bance kome ba, kin ji na ce aurenki zan yi ne? Ko da dai na gode da har kika gane dalilina na kiranki.”

“Wai waye ne?”

Ta furta tana jingina da ƙofar gate ɗin jin jinin jikinta na shirin daskarewa, in dai zai buɗe baki ya yi magana sai ta ji sautin bugun zuciyarta ya canja.

“Alherinki ne! Ance mini jami’a kike zuwa ko? Dan Allah alfarma… Kar ki ƙara saka wannan ficicin gyalen naku, haka kar ki yi kwalliya irin ta jiya ki ce za ki tafi makaranta raina ba zai mini daɗi ba, bari na je ki kula mini da kan ki. Am.. Kar fa ki manta ina bibiye da duk abinda nake so, wa billahil azim Baby Sarauniya ba da wasa na samo ki ba.”

Daga haka aka kashe wayar.

Ta bita da kallo tana riƙe gefen cikinta da ta ji ya tamke tsam, ta yi azamar ɗaga ƙafafunta da ke mazari ta faɗa cikin gidan tana doko ƙofar. Ta toshe bakinta da ƙarfi tana jin wani matsanancin tsoro na ratsa ko’ina na halittarta, wannan mutumin da suka yi waya shi ne dai wannan mai kyan da ta gani jiya a gidan Huzaif, shi ne dai wanda Huzaif ya ce mata ba Babansa ba ne, ƙila Aljanine cikin Aljanun da kwalliyar mata ke burge su. Ai sai ta rushe da kuka da ƙarfi tana cuccusa gashinta da ke waje cikin hula.

A sannan Baba Maigadi ya shigo ta bishi da kallo fuskar nan kafa-kaca, sai kuma wani tunani ya zo mata ta yi azamar matsawa kusa da shi tana kakkarwa.
“Baba ka ga wata baƙar mota a waje?”

Ya girgiza kai, sai kuma ya juya yana buɗe ƙofar ya leƙa.

“A’a babu mota a waje…, lafiya kike kuka?” Ya ƙarasa cikin walwala.

Ta kwalalo ido tana jin cikinta na rugugin aradu haka ta ja ƙafa ita ma ta leƙa ai sai ta dafe ƙirji.

Babu baƙar motar nan, kai ko ƙurarta ba ta hanga ba.
Ai da gudu ta juya zuwa sama cikin ɗakinta ta fara tattara abubuwan buƙatarta ta yi ɗakin Zawwa, ranar makarantar da bata je ba kenan, haka wayarta kashe ta ta yi ta jefa cikin drawer, duk faɗan Mami da mita a cikin ɗakinta ta kwana a bayanta a kuma tsakiyar gadonta.

Washegari sai da hantsi ya dubi ludayi ta iya lalubo wayarta ta kunna.

A take kiran Huzaif ya shigo ta ɗaga da azama tana sauke ajiyar zuciya.

“Wai menene haka kike yi? Kinsan sau nawa na kira ki? Kinsan awana nawa jiya a ƙofar gidanku na kasa bugawa?”

Ta kwalalo ido.

“Dama ka san gidanmu?”

“Ban sani ba!”

“Yi hakuri dan Allah.”

Ya sauke ajiyar ta can ɓangarensa yana jin duk zafin kansa na sanyaya. A rayuwarsa yana son mutum mai bada haƙuri. A jiya da bai jita ba shi kaɗai yasan yadda ya ji. Ɗauko mota ya yi takanas ya zo cikin unguwarsu ko zai ganta, gashi baya so tun yanzu da bai gama fahimtar ta ba mahaifinta ya gansa, ban da haka da kai tsaye zai kutsa cikin gidan nasu.

“Sururul Qalby baka haƙura ba ko?”

Sassanyar muryarta ta ƙara ratsa dodon kunnensa.
Ya ja iska ya fesar yana sanya hannu ya shafo tattausar sumarsa.

“Na haƙura mana, amma kar ki ƙara rufe waya kinji, kin ɗagan hankali sosai.”

“To ai ban san kana kiran wayata ba har haka.”

“Ban san wata magana fa, ina za mu haɗun?”

“Sitting room din Abbanmu.”

Ya harari wayar kamar tana gabansa.

“Ke ai na san da gidan naku na ce miki mu haɗu waje ko?”

Ta yi ƙasa da murya sosai.

“Ai na daina fita ne, na bar zuwa ko makaranta ance na killace kaina.”

“What? Wai ni sa’an wasanki kika maidani ko.”

“A’a, ka tsaya ka ji mana…”

Ta furta tana wawwaigawa, gani take kamar Aljaninta na cikin ɗakin.

“Me zan ji wai? Kina tunzura ni wallahi.”

“Kai Sir?…”

Sai kuma ta nisa.

“Bari dai zan rubuto maka gun a text.”

Ta ƙarasa tamkar mai raɗa, ta kashe wayar ta buɗe gurin rubuta saƙo ta rubuta masa ta tura. Sai kuma ta yi murmushi tasan dai duk maitar Aljan bai san abinda ke zuciyar bawa ba balle ma ya zo mata nan gurin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Hakabiyya 8Hakabiyya 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×