Haƙiƙa Allah Ta'ala shi ya fi cancanta da mu miƙa lamuranmu Gare shi, domin shi ne Majiɓincin lamari, Mamallakin mulki, Wanda idan ya ce kasance take abu zai ci gaba da kasancewa.
Daga cikin irin Ni'imominsa ne ya hore min haɗuwa da wasu mutane guda huɗu da suka taka muhimmiyar rawa cikin rayuwata, idan na ce wasu mutane ina nufin su ɗin ba iyaye na ne da suka haife ni ba, amma sun min gatan da ko iyaye na sai haka, duk dai haɗuwar tawa da su ta zo da yanayi. . .