Skip to content
Part 1 of 3 in the Series Halimatus Sa'adiya by Ameenat Auntyn Khalil

Haƙiƙa Allah Ta’ala shi ya fi cancanta da mu miƙa lamuranmu Gare shi, domin shi ne Majiɓincin lamari, Mamallakin mulki, Wanda idan ya ce kasance take abu zai ci gaba da kasancewa.

Daga cikin irin Ni’imominsa ne ya hore min haɗuwa da wasu mutane guda huɗu da suka taka muhimmiyar rawa cikin rayuwata, idan na ce wasu mutane ina nufin su ɗin ba iyaye na ne da suka haife ni ba, amma sun min gatan da ko iyaye na sai haka, duk dai haɗuwar tawa da su ta zo da yanayi a kaikaice, tunda ɗaya daga ciki ya zame min dafi ko kuma in ce guba mai kassara jini da tsoka, wadda ƙarfin ta ya kai har ta lalata min ƙashi da ɓargo.

Ta farko ita ce Aunty Lami ƙanwar maihaifina ce, na biyu kam sai ɗan uwanta Abba Ibrahim shi ma ƙanin Abbanmu ne, ta uku kuwa ƙawata ce Sa’adiya wadda ta kasance ba ni da wata ƙawa kamarta, muna zumunci, muna ƙaunar junanmu, hakan ya sa muka fayyace sirrinmu ga juna, na huɗunsu shi kam mahaɗin rayuwata ne, shi ɗin wani bangare ne a cikin gangar jikina, idan na ce wani ɓangare ina nufin bangon sukari na ne shi.

Ranar juma’ar da ta zame mana masomin komai, duk wani abu da zai faru cikin wannan rana ya fara afkuwa, to da yake masu iya magana suka ce mutum tara yake bai cika goma ba, sai na ƙara gaskata maganarsu.

Iska ce mai cike da sanyi ke kaɗawa, sannu a hankali sanyin da ake yi mai ratsa jiki ya soma kore jama’a daga titi, mazauna lokuna ma suka fara janye jikinsu, kamar yadda na ji wasu mutane da suka shigo gidanmu da rana suna faɗe ga dukkan alamu Jaura ce za ta wuce yau.

Ni kaina sanyin nake ji, wannan ya sa na fara shirya kayan yara wanda na wuni a kansa ina yi cikin jakar da nake adanawa, komai na amfani na ajiye shi wurin da ya kamata, kana na share tsakar ɗakin da babu komai a cikinsa sai ledar tsakar ɗaki, sai yar katifa da na naɗe ta da zanin gado ruwan sararin samaniya da filo guda ɗaya a kai, gefen sa kuma jakar kaya na ce sai takalma na biyu maras tudu biyu masu dan tudu, dayan kuma sau ciki ne (Toms), idan an hada su sun zama ƙafa biyar kenan, daga gefen jakar nake ajiye su, sai kuma waccan jaka da nake ajiyar kayan ɗinki a cikinta.

Juyawa na yi na kalli ɗakin komai yayi yadda nake so, tunda ni ba ma’abociyar tara shirgi ba ce, uwa uba kuma ba na son ƙazanta don haka nake shirya komai nawa tsaf, takwara na yawan yabon ɗakin, na kan ƙawata shi da ƙamshi lokaci zuwa lokaci don idan na yi turaren wuta yana daɗewa ɗakin bai daina ƙamshi ba.

Fitowa na yi tare da jawo ƙofar na kulle, sai dai take cikina ya ɗauki ƙugi, ko ba a faɗa ba na san yunwa ce. Sai sannan na tuna yau fa ban ci abinci ba tun bayan karin kumallon da na yi.

Har zan fita sai kuma na sake buɗe ɗakin, kai tsaye wurin da nake ajiyar biskit, madara da taliyar yara wato (Indomie) na duba wayam na gani babu ko ledar sukari. Take zuciyata ta kara yin zafi, rashin daɗin da nake ji a kan Abbanmu na yadda yake wofintar da mu ya ƙaru, na sani ba kyau jin haushin iyaye amma tabbas yadda Abba yake mana riƙon sakainar kashi ni da yaya Muttaƙa ina jin ba daɗi, don dai kawai mahaifina ne shi ba yadda zan yi.

Share hawayen da ya cika idanuna na yi, don alƙawari na ɗaukarwa kaina ba zan sake zubar da hawaye na akan matsalar mu ba, zan yi addu’a har zuwa lokacin da Allah zai amsa roƙo na.

Ficewa na yi daga ɗakin a karo na biyu na kulle shi da mukulli. Ba kowa a tsakar gidan duk kuwa da kasancewa gidanmu na mutane ne, har ma da waɗanda ba ƴan gidan ba shigo wa suke yi, saboda sabuwar sanar da mama ta ƙirƙiro da yi.

Cike da fargaba na fita daga cikin gidan, gabatowar magriba ce ta sa na ƙara ɗaga ƙafata don kada Abba ya dawo ya tad da na fita, don ba ya son fita da dare ko kaɗan, wannan ya sa ba ma kaiwa dare a waje, ko biki muka je dole mu dawo da wuri, idan kuwa na dare ne sai dai mu haƙura da shi, ko da kuwa bikin ya shafi wani nasa ne.

Sannu a hankali na isa shagon Ali, daga gefe na ja na tsaya, ganin maza sama da uku tsaye bakin shagon, su ma sayayya suke yi, warware kuɗin da ke cikin tafin hannuna na yi, sai kuma na maƙale su sanda wani tunani ya zo min.

Sai da duk mazan nan suka fita daga cikin shagon sannan na shiga ni ma, kuɗin na miƙa masa, karɓa ya yi ya ce,

“Hali dubu me zan ba ki? Sauri nake lokacin sallah ya gabato.”

Da hanzari na ce masa,

“Baƙin Zip za ka ban guda biyu, sai waccen tutar baƙaƙe guda uku, sai zare shi ma baƙi dan naira arba’in.”

Juyawa ya yi ya fara haɗa min abubuwan da na ambata, sai da ya ciro komai ya saka a leda sannan ya miƙo min na karɓa, na ce “Na gode.”

Ya ce “Ba komai, ai ni ne da godiya.”

Fitowa nake ƙoƙarin yi daga shagon, fuskata ba yabo ba fallasa, daidai lokacin kuma Khalid yana shigowa shagon yana tambayar Ali pure water zai yi alwala, ya juyo gare ni don da farko ma ina ga bai yi zaton Ni ba ce.

Da yake sauri nake yi a daddafe muka gaisa, ya tambaye ni ina Hasanar tawa na shaida masa tana gida don daga nan wurinta na nufa, sannan na wuce yana ba ni sallahu akan na gaishe masa da ita.

Duk wanda ya ga irin yanayin tafiyar da nake yi zai iya zaton yanga nake, nan kuwa ni kaɗai nasan irin carbin da nake karɓewa, cikina sai faman kiran ciroma yake yi, ga sanyi da nake matuƙar ji, hantar cikina har wani kaɗawa take yi, jikina na matuƙar karɓar yanayin sanyi.

Ban damu ba don idan da sabo na saba, dama can ƴan unguwarmu suna jifana da kalmar girman kai, hakan ba ya damu na don na san kaina, na kuma san ba haka nake ba, dama can ni maganar mutane ba ta damu na don zaman da na yi da mama da kuma kakata Hanne ya sa na saba da irin wannan.

Tafiya na ci gaba da yi, saboda yunwa ji nake kamar zan siƙe, jifa-jifa ƙwalla ke cika idanuna, amma sai na dake na ci gaba da tafiya, a fili nake furta “Kukan ya isa haka don ba ya magani.” Cikin ƙanƙanin lokaci na isa ƙofar gidansu takawara, aminiya abokiyar kukana, ba kowa a wajen dama layinsu haka yake bai cika tara mutane ba sosai, sai dai idan ana biki ko suna ko kuma matasan unguwar sun fito hira da yamma zuwa dare haka.

Da sallama na shiga a bakina Umma na tsakiyar tsakar gida tana casa masara tana mitar ta kai surfe inji amma ba su surfa ta fita da kyau ba, sun mayar mata da hannun agogo baya ga sanyi ana yi doke sai ta kuma casa masarar.

“Wa alaikisalamu da Halimatus Sa’adiyya.”

Wuri na samu kan buhun gero a tsakar gidan na zauna daɓas, tare da cewa,

“Wash!!! Umma sannu da aiki, ina wuni.”

Ta ce “Lafiya lau, daga ina kike haka?”

Ledar hannuna na ajiye gefe tare da dafe goshinada yake sara min na ce,

“Wallahi Umma daga shagon Ali nake, na je sayan kayan ɗinki na ce ba zan tafi ba sai na ƙaraso na ga takwara.”

Casar da ta dakata da yi tun shigowata ta ci gaba da yi tana cewa

“Ta je gidan Sa’ida karɓo wa yayanta saƙo.”

Ban ji daɗi ba don haka rai ɓace na ce,

“Shi ne ba ta kirawo ni mun je tare ba?”

Umma ta ce,

“Wannan kuma i taku kun fi kusa, Auyo da Hadeja.” Ci gaba da surfenta ta yi.

Can na ce, “Umma wallahi yunwa nake ji, ko da abinci a gidan nan?”

Ta ce, “Shiga ɗakinku akwai abinci cikin fulas, ni dama na ga duk kin firirce, na ɗauka gajiya ce shi ya sa ban yi miki tayin abinci ba, daɗin daɗawa kuma ba komai kike iya ci ba.”

Ɗakin na shige ina faɗin, “In dai ba kifi ai ci zan yi Umma.”

Na shige ciki ai kuwa dafadukan shinkafa na tad da shaƙe cikin kula, sai ƙamshin attaruhu take, ga wani turiri yana tashi, zubawa na yi a faranti, har na fara ci can sai na hango farin ɗan ƙaramin bokiti cike da soyayyar awara,

Na ce, “Umma awarar waye wannan? Na ɗauka?”

Umma ba ta ban amsa ba, ta kwashe da dariya jin muryar Aminu da ke banɗaki yana faɗin.

“Kada ki soma taɓa mini awarata, Allah kika ɗauka sai kin biya.”

Ban kuma cewa komai ba don na ji me ya faɗa. “Mutum yana banɗaki yana magana.” Leda na ɗauka na zuba awarar manya guda uku tare da ɗakko ƙaramin fulas a cikin kwando na juye abincin da na fara ci, na rufe na fito tsakar gida, hannuna rike da awarar, ƙasa-ƙasa na ce,

“Umma na tafi, idan takwara ta dawo ki ce ta zo ina gida.”

Da hanzari na fice daga gidan, ina dariyar mugunta, saboda na san ɓarnar da na tafkawa mara mutuncin yayanmu Aminu. Shi haka yake ga kwadayi ga rowar tsiya, ko ɗanmalele muka yi ko wainar fulawa da shi ake ci a sha, amma nasa ba mai ci, gida na yi raina fes.

Masu iya magana na cewa rashin sani ya fi dare duhu, kuma ƙaddara ta riga fata, hakan ce ta faru da ni bayan na isa gida.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Halimatus Sa’adiya 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×