Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Halimatus Sa'adiya by Ameenat Auntyn Khalil

Abu mafi girma da kuma burgewa a tare da ni da gidan su takwara shi ne yadda ake min a gidan, ko iyaye na ne su iya sakin jikin da za su yi da ni kenan, ina ƙaunarsu tsakani da Allah.

Gidansu takwara na matukar ban sha’awa ta yadda suke gudanar da rayuwarsu cikin wadatar zuci don suna da rangwamen gata, sabanin mu da rayuwar take da afuwa a gare mu, don alhamdulillah abbanmu yana da rufin asiri amma duk da haka ban kasa zama koma baya a cikin gidan ba, gidan uba na amma wasu abubuwan sai dai a zura ido, a kullum ina sawa a raina zai wuce, wata rana sai labari, sai kawai na sa kai na ci gaba da harkar gabana.

Tafiya kaɗan na ƙaraso gidanmu, a ƙofar gida na tad da motar Abba ko ba a faɗa ba na san ya dawo amma ya fita masallaci, na fahimci haka ne bayan na shiga cikin gidan namu, Mama na tsakar gida na alwala a famfo.

Ba ta amsa sallamar da na yi ba, ni kuma ban yi mata magana ba, ɗakin na buɗe, na shiga na ajiye kayan da ke hannuna a ƙasa, kayan ɗinkin kuma na ɗora su bisa keken ɗinkina.

Fita na yi, na taro ruwa a buta na shiga toilet bayan na fito na yi alwala na koma ɗaki.

To ban kai ga idar da sallah ba Abba ya dawo daga masallaci, ina ji magana suke yi shi da Mama a tsakar gida, bayan na idar da sallah na fito tsakar gidan nima da niyyar gaishe da Abba.

Na zo gabansa na tsuguna yana zaune kan kujera na ce,

“Abba sannu da dawowa, ya aiki?”

Ban aune ba na ji saukar mari har guda biyu a fuska ta, na tuntsura na faɗi ƙasa take na fara ganin taurari na yawo bisa idanuna, dafe kuncina na yi, wasu hawaye suka shiga zarya kan fuskata. Ko a mafarki aka ce Abba zai duke ni ba zan yarda ba, saboda shi mutum ne mai son ya’yansa ba ya son laifinmu amma sam an canja masa tunani, yadda yake son mu a da yanzu duk babu.

Wani zagi ya yi mini marar daɗin ji abin da ban taɓa ji ba kenan daga bakinsa ga shi ba na ƙaunar a zagar min uwa ko kaɗan, kuma itan ya zaga, ya ƙara da tuhuma ta,

“Ina kika je?”

Cikin kukan da ya yi sanadiyyar dakushewar muryata na ce,

“Abba kayan ɗinki na sayo na je gidan su Sa’adiyya .”

Ƙafa ya sa ya hamɓare ni take na fara watangaririya a tsakar gidan, ban san sanda na dangane da bango ba, Ƙasss! Na ji kafata ta yi ƙara da alamu ma targaɗe na yi, gunjin kuka na ci gaba da yi, ina neman ɗauki gurin Mama, amma matar nan ko kallon inda nake ba ta yi ba bare ta kwace ni.

Ganin ba mai ceto na ya sa na fara Roƙon Abba.

“Abba don girman Allah ka yi haƙuri, ba zan sake fita ba ko da rana ne, don Allah ka yi haƙuri.”

Wayar igiyar da muke shanya kayan wanki ya fusgo daga jikin bango, daidai lokacin kuma Yaya Muttaka ya shigo cikin gidan, to ganin Abba na shirin lafta mini wannan igiyar ya shiga tsakani, ƙarshe dai a jikinsa wannan duk ya sauka, cikin fushi Abba ya ce,

“Wallahi idan ba ka bani wuri ba zan mayar da hukuncin kan ka.”

Yaya Muttaka bai matsa ba cikin ladabi ya ce da Abba,

“Don girman Allah ka yi haƙuri!”

Jefar da igiyar Abba ya yi, jin shigowar Abba Ibrahim ƙaninsa, wanda suke uba ɗaya da shi, da yake maƙota muke da shi, katangarmu ɗaya sai dai ƙofar gidanmu na titi su kuma ta baya ƙofarsu take don haka duk abin da ake a cikin gidanmu za su iya jiyo shi ta katanga.

Shigowa ya yi ciki, ganin ya Muttaƙa na jayayya da Abba ya sa shi cewa,

“Haba Jibril, me yaran nan suke maka ne kake yi musu haka? Ai ko me suka yi bai kamata ka ringa dukansu ba, ka duba fa waccen mace ce, ina kai ina dukanta.”

Haka dai Abba Ibrahim ya yi ta yi masa faɗa kamar shi ne babba, Mama ta taso da niyyar yin magana ya dakatar da ita da faɗin,

“Ke kinga da ɗan uwana nake magana, ban kasa da ke ba bare ki ce za ki ɗauka, duk ba ke kike haɗashi da yaran ba.”

Sai Mama ta yi laƙwas dama ba jituwa suke yi ba shi da ita, ya yiwa Abba faɗa sosai, ya kuma shaida masa ya bi a hankali, idan bai wasa ba za a kaishi a baro, kuma Allah zai tuhume shi kan yadda ya tafi da mu don ya tabbatar ba mu yi masa komai ba yake mana haka.

Cikin zuciyata na ce “Na yafe masa ma ni, don ina kaunar Abbana, kawai dai wani lokacin ba na jin dadin yadda yake mana yanzu, da ba haka yake ba sam.”

Na san ba laifinsa ba ne, dole zuga ce ko ma wataƙila an haɗa masa da kauce hanya, dole abin ya yi yawa ko ma ya fi haka.

Juyawa ya yi kan yaya Muttaka shi ma ya yi masa faɗa sosai, ya nuna mana muhimmancin yi wa iyaye biyayya, “Kada na ƙara ji kana yi wa mahaifinka musu, kai ma wata rana uba ne, idan aka yi maka haka za ka ji daɗi?”

Yaya Muttaka ya ce “A’a.”

Abba Ibrahim ya ci gaba, “To kada ka sake ka ji ko.”

Yaya ya ce “To Abba.” Tsugunawa ya yi ya ba Abbanmu haƙuri. Abba ya nuna ba komai. Fita suka yi tare da Abba Ibrahim da Abbanmu.

Ni kuma na yunƙura da niyyar tashi amma na kasa da taimakon yaya Muttaka na koma ɗakina, jikina duk ya kukkurje musamman guiwar hannuna.

Kuka nake iyakar ƙarfina, saboda ba wani abu da zan iya yi bayansa.

Yaya Muttaka ya ce “Ki bar kukan nan haka, in dai ina gidan nan ba zan bari ya sake taɓa ki ba.”

Ɗif! Aka ɗauke wuta, kendir ɗin da ke maƙale saman keken ɗinkina ya Muttaka ya kunna, a lokacin na yi shiru amma hawaye bai daina sauka kan farar fatar fuskata da ta yi jajir ba, wanda bai sanni ba zai iya cewa wani abin mayen na sha duba da yadda manyan idanuwana suka rine suka yi ja, sun ƙanƙance a lokaci guda, hancina kuwa ya fi ko ina yin jawur saman fuskata.

“Yaya duk abin da Abba yake yi ba laifinsa ba ne, wallahi Mama ce take zuga shi, ka duba fa yau ban fita ba sai bayan biyar da wani abu, kuma kayan ɗinki na je sayowa, daga nan na biya gidansu Sa’adiyya, ka ga abincin can.”

Na nuna masa ƙaramin flask ɗin abinci da na taho da shi daga gidan su takwara,

“Umman Sa’adiyya ce ta ba ni tun bayan abincin safe da aka ba ni shi ma ganin idon Abban ne ya sa aka bani, wallahi ba su kuma ba ni komai ba.”

Kuka ya sake kwace mini, Ina mamakin halayen matan uba a wannan zamanin, Allah ya so dai ɗa na kowa ne, abin daɗin kuma dukiya da ɗa Allah ne kaɗai ya san mai morar su.

Yaya ya gyara tsayuwar sa a jikin bangon ɗakin ya ce,

“Ki yi haƙuri, ni duk ban san haka na faruwa ba, kin ga idan na fita tun safe sai dare, wani lokacin ma kin yi bacci nake dawowa.”

Na share hawayen da yake ta bin kumatuna na ce,

“Na sani Yaya, ni ba ni da matsala da kowa na gidan nan, sannan duk abin da ke faruwa ma ba na kai shi zuci, kawai dai dukan nan da Abba ya yi min yanzu ya ɓata min rai Allah ya sani ya dame ni ya kuma daga min hankali, ina tsoron kada ya koma duka na yanzu.”

Hannayensa duka cikin aljihu yana nazarin magana ta ya ce,

“Ki ƙyale su, shi ma Abban zan je na ba shi haƙuri, amma gaskiya ba zai yiwu ya shigo da duka ba, me kika yi masa ma ai ga su Ummee nan da Haneefa wa yake duka a cikinsu, duk abin da suke yi wa mutane wa ya taɓa yin magana, ko don su suna da uwa a gidan.”

Motsa ƙafata nake son yi, abin mamaki sai na kasa zaune na tashi a hankali, kumbura na ga saman ƙaramin yatsana ya yi, “Subhanallahi! Yaya ka ga ƙafata yadda ta yi.”

Cikin razani na yi maganar, ya matso da hanzari ya iso yana haska ƙafar da touch din hannunsa,

“Innalillahi!.. Targaɗe ne wannan.”

Take na sake fashewa da kuka, Allah da ya yi ni ba na kaunar ciwo a jikina, ko kurji bisa larura yake fito min, idan kuwa na yi arba da shi to fa sai ya mutu tabonsa ya goge nake jin daɗi, yanzu kuma ga targaɗe, na san targaɗe duk da ban taɓa yinsa ba amma na san yadda ake faɗar zafinsa idan an je gyarawa, ba ni da abin yi sama da kuka tare da jero addu’o’in neman sauƙi daga Allah.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Halimatus Sa’adiya 1

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×