A babban falon gidan muka zauna, daga bisani kuma Aunty ta sa aka ƙara shirya min ɗakin da zan zauna.
Wanka na fara yi bayan na shiga ɗakin, sannan na yi sallah aka kawo min abinci, sosai na zage na ci na ƙoshi sannan na sha magani, daga nan kuma sai bacci ya fara ɗauka ta, har na kwanta sai kuma na fara jiyo muryoyin yaran gidan da alamu baƙo aka yi. Sandan da nake dogarawa da shi sakamakon ciwon da ke ƙafata na kama na tashi a hankali, kafin na kai ƙofar fita ma an turo ƙofar an. . .