Gidan Asabe mai gyaran targaɗe muka je ba tare da mun faɗawa kowa ba, dama Mama ce Yakamata mu faɗawa tunda Abba ya kuma fita a daren, to ita kuma ta ɗauki fushi kan abin da Abba Ibrahim ya yi mata, ko ba haka ba ma dama ita ba mace ce mai sakewa da kowa ba idan ba ƴaƴanta ba, su kaɗai suka san kan mahaifiyarsu, ni kuma ba ta ta tawa tun ina ƙarama bare yanzu.
Asabe dattijuwa ce ta daɗe tana gyaran targaɗe shi 𝒚𝒂 sa muka je gidanta, tana taɓa. . .
Masha Allah labari yayi dadi Antyn Kalil
Allah ba da nasara
Amin ya Allah, na gode Yasmin.