Skip to content
Part 3 of 5 in the Series Halimatus Sa'adiya by Ameenat Auntyn Khalil

Gidan Asabe mai gyaran targaɗe muka je ba tare da mun faɗawa kowa ba, dama Mama ce Yakamata mu faɗawa tunda Abba ya kuma fita a daren, to ita kuma ta ɗauki fushi kan abin da Abba Ibrahim ya yi mata, ko ba haka ba ma dama ita ba mace ce mai sakewa da kowa ba idan ba ƴaƴanta ba, su kaɗai suka san kan mahaifiyarsu, ni kuma ba ta ta tawa tun ina ƙarama bare yanzu.

Asabe dattijuwa ce ta daɗe tana gyaran targaɗe shi 𝒚𝒂 sa muka je gidanta, tana taɓa ƙafar ta yi saurin janye hannunta ta ce,

“Wannan ai karaya ce.”

Ni kaɗai na san irin azabar da nake ji bare ma da ta sake taɓa wurin, kamar ƙara hura shi ma ake sai kumbura yake ƙara yi.

Ta kuma kai hannu za ta taɓa cikin zafin nama na janye ƙafar, saboda ni kaɗai na san irin raɗaɗin da nake ji, yaya ta duba ta ce masa.

“Sai dai ku tafi gidan sarkin ɗori ko asibiti.”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”

Na faɗa, take kuma hawayen da ke maƙale cikin idanuna suka fara zuba kamar an kunna famfo.

Alamu sun gwada ran ya Muttaƙa idan ya yi duba ya ɓaci, ya ja tsaki ya fi sau a ƙirga. Hanyar fita ya nufa ko me ya tuna oho dai ban sani ba sai ya dawo, ciro wayarsa ya yi daga aljihu ya fara kira, ban san wa yakira ba, can aka amsa daga ɗaya bangaren, ji na yi ya ce,

“Uncle barka da dare, ya aiki?”

To tunda naji ya ambaci Uncle na san Uncle Abubakar ya kira bayan sun gaisa ya kwashe komi ya faɗa masa, abin ya ɓata masa rai, ga yadda na ji yayan yana ta cewa,

“E wallahi, kowa haka yake cewa, Abba Ibrahim ma ya yi masa magana.”

Kashe wayar ya yi, cikin kuka na ce

“Yaya me Uncle ya ce?”

Ya ce,

“Cewa ya yi na ba shi mintina biyu.”

To ban kuma cewa komai ba, Asabe tana ta jimamin hali irin na Mama, don tuni na faɗa mata yadda abun ya faru, ko yaya abu ya same ni rikicewa nake yi, sai na kasa controlling kaina.

“Babanku shi ya fi kowa laifi, a wannan marra ko ɗa namiji ka zage ƙarfi ka ringa duka bare ƴa mace.”

Ƙarar kiran da ya shigo wayar Ya Muttaka ne ya katse ni ban cewa Asabe komai ba, duk da ina cikin hali na ciwo a ƙafata amma na so kare Abban amma na yi shiru.

“To Uncle bari mu je, E! Da kuɗi a hannuna. To shi kenan zan kira da zarar mun je.”

Asibitin Ƙashi na Dala muka wuce, na gane hakan ne tun lokacin da yaya yake kwatanta wa mai adaidaita sahu inda zai kai mu.

Muna isa cikin asibitin yaya ya kira Uncle a waya ya shaida masa mun je, sannan ya kashe wayar, ya biya mai adaidaita kuɗinsa sannan muka fito sai dai me na kasa taka ƙafar, calak yaya ya ɗauke ni ya ajiye kan wani tudu daga gefe cikin asibitin.

Wayar sa ce ta ɗauki ƙara bayan ya sauke ni, ina iya jiyo abin da na ɗaya ɓangaren da ake wayar da shi ya ce,

“Ku jira a zo a shigo da ku.”

Ba mu jima ba kuwa aka zo da keken majinyata (wheelchair) aka shigar da ni har ciki, mutane sai kallonmu suke yi, ban san dalilin da yasa ake kallonmu ba, kawai na fi alakanta abin da kyawun da Allah ya bamu, sai kuma farar fatar da muke da ita uwa uba kwantaccen gashi irin na fulanin asali da muke da shi, na san kallon da ake yi mana ba zai wuce na hakan ba.

Duk yan gidanmu farare ne saɓanin Haneefa da fatarta take baƙa, wadda bahaushe yake wa laƙabi da (chocolate color)ni har na fi su fari, don kallo ɗaya za ka yi min ka yi zaton ko na haɗa iri da mutanen yankin gabas ta tsakiya. Shi kuma ya Muttaka ya fi ruwa da fulanin asali, Ummee kuma farin Abbanmu gare ta, sauran yan gidan ma duk haka muke, kamar mu ɗaya duka amma dai ni na fita daban a cikinsu, muna da kyau daidai gwargwado.

Wani ɗaki aka shigar dani, nurse ta ce yaya ya jira a waje, jim kaɗan likitan ya ƙaraso hannu ya miƙa wa yaya suka gaisa, bayan ya yi masa bayanin komai sannan ya shigo ciki, da yake ƙofar ɗakin ta gilas ce ina iya gano komai da yake wakana a waje, su na wajen ne dai ba za su iya hango na ciki ba.

Ƙafata ta kunbura sosai dama kuma ina da cikar naman ƙafa, ƙafata ba ramammiya ba ce.

Duk wani abu da ya kamata an yi mini shi cikin kankanin lokaci tunda mutumin abokin Uncle ne na kusa.

Na sha azaba, wai a haka ma don an zo akan lokaci ne ya sa ban ji zafi sosai ba, da na kwana zan iya suma yadda ba ni da dauriyar nan, na yi kuka har na gode Allah, yunwar da nake ji ma daina jinta na yi, yawun bakina ya ɗauke kaf!

Ba mu tafi gida a ranar ba sai da na kwana biyu, wannan kuma alfarma ce ta dalilin Uncle Abubakar ne.

Takwara kullum ta zo sai mun yi kuka, haka idan za mu rabu cike da kewa, daɗinta dai ba ta tafiya sai an yi magriba da isha’i.

Umman su takwara ta yi rawar gani, har abinci ta sa a kawo min, haka ma uba na Abba Ibrahim, ga kuma aunty Lami ita ma tana ta hidima.

Mama ba ta zo ba, dama ban yi tsammanin ganinta ba.

Abba kuwa kullum sau biyu yake zuwa, ya zo da safe ya zo da dare idan ya dawo daga aiki ko kasuwa, ba’a karɓi ko kwandalarsa ba.

Uncle ne ya yi komai duk da ba ya ƙasar amma ya bada gudunmawa sosai.

Dr yana ta tsokana ta wai raguwa ce ni, shi ya yi mana komai har aka sallame ni, Dr Bashir kenan, yana da mutunci, ga karrama ɗan adam.

Ranar sallama ne Aunty take tambayata,

“Yanzu gida za a mayar da ke ko za ki bi ni mu wuce Hotoro?”

Ban yi tunanin komai ba na ce, “Aunty gidanki zan je.”

Ta ce,

“Alhamdulillah! Nima hakan ne a raina, ba na son takura miki ne ya sa na tambaye ki.”

Aunty Lami ƙanwar Abbanmu ce ita ma dai uba ɗaya suka haɗa da Abba, tana sona don tun ina ƙarama ni tata ce, halin Abba ne ya sa ta rabu da ja na a jiki, wannan soyayyar ta samu ne kasancewar gidan su Abba ba ƴan ubanci.

Motar mijinta ce ta zo ta ɗauke mu bayan sallar azahar, nan da nan muka isa Hotoro da yake ta cikin gari muka shigo, daga masallacin juma’a muka miƙe titin gidan sarki, ina kallon kofar gida muka wuce muka haura State road, zuwa tarauni sai gamu a kwanar maggi, muka hau kan titin Hotoro, bakin get ɗin gidan muka tsaya bayan mijinta ya yi horn mai-gadi ya buɗe muka shiga ciki.

Fatima ce tsaye sanye da baƙar abaya, ta yane kanta da ƙaramin ruwan tokar mayafi da alamu jiran zuwanmu take yi, jin tsayuwar motar Daddynsu ya sa su Nana da Abdul-Rahman fitowa da gudu suna mana oyoyo.

Na ji daɗin ganin yaran, saboda a duniya idan aka cire gidan su takwara sai gidan Aunty Lami ne kaɗai suke ɗauke min baƙin ciki idan na je.

Su ma sun ji daɗin ganina sosai, Nana sai tambayata take,

“Yaya ciwo kika ji? Yana miki zafi?.”

Aunty ta ce, “Ku bata wuri don Allah, kada ku fama mata ƙafar.”

Cewa ta kuma yi “Au a ƙafa ta ji ciwo.”

Auntyn ta ce “E! bamu hanya.”

Shiga muka yi cikin, gidan yana matuƙar burge ni, sosai ginin yana da ban sha’awa. Ɗakinta na ƙasa muka sauka, falo biyu ne a ƙasa sai wasu ɗakunan biyu duk da gado a ciki, falon farko ya ɗauki saitin kujeru peach sai ƙatuwar tv plasma daga bangon Yamma, daga baya bangon arewa kuma dinning table ne baƙi da kujeru zagaye da shi su ma baƙaƙe ne, daga tsakiyar bangon gabas kuma kofa ce, idan ka shiga cikinta za ta sada ka da kofar da za ka dawo farfajiya farko ta shigowa gidan daga yamma kuma ƙofar toilet ce.

Idan ka koma baya kuwa ƙofar da muka shigo sarari ne sai kofar kicin da kuma ƙofar ɗaya falon nata, sai kuma ƙafar bene da ta sakko duka dai a cikin wannan sarari, ƙasan matakalar bene kuma deep freezer ce katuwa sai wata kwana da aka ƙawata ta da fulawoyi kala-kala tun daga ƙasa har sama.

Sosai dai gidan ya yi kyau, wannan ya sa nake son zuwa can don kayan ado na burge ni, ina sha’awar gidan da ya ƙawatu da kayan decoration Sosai.

Ɗakunan baccinsu duka a sama suke, katafaren falo ne a saman, ɗakin daddy na daga wani suƙullufin loko a cikin falon, idan ba ka sani ba ma sai ka zaci ɗan gurin shan iska ne kawai alhalin kuma da ƙofa a ciki. Daga gaban sararin kuma sai ɗakin Aunty sannan na yaran daga can ƙarshe, sai kuma wani ɗaki shi ma, ta ƙawata shi da tuntaye irin na gidan sarauta, kowane ɗaki a saman yana da toilet abin dai sai wanda ya gani.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Halimatus Sa’adiya 2Halimatus Sa’adiya 4 >>

2 thoughts on “Halimatus Sa’adiyya 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×