Ina kallo Asabe take fitowa daga wanka ta shafa maina tayi kwalliya da kayan kwalliyata in ta gama ta jawo akwatin kayana ta zabi wanda yayi mata ta daura, bana cewa komai saboda ina tsoron kar maganar da zan yin ya zama sanadin da zamu yi fadan da zata rama cizon.
Sannan in ta gama abinda take yin sai ta mike ta bar komai a hakanshi sai na gyara wanda ni shi ne ma yafi bata min rai.
Rannan da hantsi Mubarak yazo muna tsaye muna magana sai ga Sallau yazo ya wuce mu yana taku dai-dai, ya. . .