Na dawo da baya nasa hannu na dauki bokitin robar da ake wanka da shi, nufina in tari ruwa a bakin famfo in je in yi wankan a haka, nan ma ta ce a jiye min bokitin nan tunda ba uwarki ce ta saya min shi ba.
Na maida shi na ajiye na wuce naje na dauko wani bokitin karfe da ke can gefe na tara shi ina duban ruwan ta bar abinda take yi ta mike ta tsaya tana kallona wai ba nace kar ki taba min wani abina ba ne ko kina nemana ne da magana’?
A hankali cikin natsuwa nace mata wannan ai ba naki ba ne kin ga ni? Bokitin Innarmu ne, abinda kawai na fada kenan ta takarkare ta wanke ni da marin da nayi matukar kaduwa.
Ba na ce ki daina ambaon min sunan shegiyar matar nan a cikin gidan nan a? ban san lokacin da na buda baki na ce wa Babah Lantana “Gaskiya Innarmu ba shegiya ba ce. Sai kawai ta rufe ni da duka.
“Ai dama na gane talke-takenki nema ki ke ki fara zahina kiri-kiri, bayan na bayan idon da kike yi ana gaya min ba ki kuma isa ba don ni nan ko uwar taku ma da tana nan din ba za ta buda baki ta zage ni in kyale ta ba, to balle ke banza a banza.
Duka irin wanda Babah Lantana tayi min bai kwatantuwa don kuwa yi tayi sai da ta gaji ta bari don kanta, babu wanda ya shigo gidan don kawo min agaji, duk da irin ihun da nayi ta kurmawa.
Asabe ma tana daki a zaune ba ta ce mata komai ba. Ina zaunc a tsakar gida bayan matsanancin dukan da Babah Lantana tayi min ban sake komawa dakin ba saboda abinda nake tsoro wana ke kara sa ni zaman nakin ya faru, don haka ina zaune ne kawai a tsakar gidan amma ban iya daina kuka ba.
Ita kuwa Babah Lantana tana ta kai-kawonta tare da fadin “Haba an ce miki ni ina tsoron wani ne? Ni fa da ki ke ganina bana tsoron kowa ina kyaleki ne kawai kina iskancin ina kallonki, amma ba don tsoro ba.
Yi ta zama a nan har uban naki ya dawo yazo ya same ki in ji abinda zai ce, ina ce zaman da ki ke yi a wurin ke nan, in kuma shi wancan dan iskan ne ina nan ina zaman jüran dawowarshi in ga abin da zai yi ko ni ma zai zo ya kirba min naushin ne?”
Sallau yana shigowa gida ya ganni a zaune yayi turus ya zuba min ido yana kallona, cikin tsananin kaduwa ya juya inda Babah Lantana ke zaune tana sakucen naman da taci da tsinken zaburin shara.
“Dukanta ki ka yi Babah, me tayí miki? Ba ta ma fa gama warkewa ba sannan in za ki buge ta ma Babah wannan wane irin duka ne?
Da sauri Babah Lantana ta mike ta kifa mishi mari mai tsananin karfi ta sake kifa mishi wani. Marin har sau uku da ya tsaya wata kila da abin yafi haka.
Juyawa yayi ya fita, ya barta tana fadin, sakarai, matsoraci, shashasha kai kam in ba sa’a nayi rakiya kayi wa maza zuwa duniya don duk wata harkarka ta tsoro ce, na bugeta wanda duk ke da abin yi yazo yayi ina nan ina zaman jiranshi, aikin banza aikin wofi, ni za a kawowa iya shege?
Ina zaune a daki cikin matsanacin hali don wani zazzabin ne ya sake rufe ni, ga bacin rai don na fara gajiya da irin wadannan al’amuran naji dawowan Babana da bayanin da Babah Lantana ke yi na nayi mata rashin kunya itama kuma tayi min hukuncin da ya dace da ni.
Sau dubu kuma in zan mata to sau dubu itama zata yi min in ina son zama lafiya to in kiyayeta gara tun wuri ya jaddada min in ba haka ba kuwa to ita babu ruwanta bai ce mata komai ba.
Washegari da safe tunda na tashi da kyar nayi sallah na koma na kwanta saboda tsamin da jikina yayi ina jin sanda Asabe ta sauko daga kan gado ta take min kafata ban ce mata komai ba.
Ta dawo dakin tana sallah na ji Babah Lantana tana ta kwala mata kira, cikin wani yanayi kamar dai wani abu ya faru, da sauri ta:sallame ta fita sai naji tana ce mata yi sauri ki tafi gidansu Delu ki gani ko a can Sallau ya kwana bai dawo gida ba jiya.
Gidan su Delu kuma Baba me zai kai shi can bayan duk wannan abinda aka yi? Yanzu haka yana can wajen abokanshi sun sha a bar su suna ta barci.
Ke wuce kije ki duba min shi mara mutuncin yarinya mai gardamar tsiya kuma Delun kike kira haka gatsau babu sakayawa babu komai?
Asabe ta wuce tana kunkuni haka kawai mutum yaje ya kwana a wurin iskancinshi za a hana ni baccina na safe ace sai na dubo shi sai ka ce wani dan karamin yaro.
To ko ni da aka ce Sallau bai kwana a gida ba nayi mamaki don ba mai irin wannan halin ba ne amma sai na maida lamarin kan yayi fushi ne da abinda uwarshi tayi mishi saboda maganar da yayi mata a kaina tunda na saba ganin yana fushin da ita ta bashi hakuri.
Abu wasa-wasa sai ya soma neman ya zama gaskiya kusan duk inda ake zaton ganin Sallau sai da aka je nemanshi babu shi babu dalilin shi.
A ka wuni ranar babu Sallau, tun ana kokarin danne hankula kar su tashi har dai abin ya gagara a ka shiga tashin hankalin mai tsanani, nema har da Babana a ciki don ko wurin tumatirinshi bai je ba, har wajen yan sanda aka kai riport da kuma asibitoci shiru babu wani motsi.
Har wajen taran dare suna zaune jungum-jumgun a tsakar gida, yayinda ni kuma nake kwance a daki sai naji Babah Lantana tayi Magana cikin sauri duba Asabe naji kamar an shigo zauren gidan nan.
Asabe ta mike tana fadin ke Babah ba za ki bar mutum ya huta ba, dazu ma fa haka ina zaman-zamana ki ka tashe ni wai kin ji kamar an shigo zauren gidan nan to in an shigo menene?
Wani irin mummunan ihu Asaben ta kurma a daidai shiganta cikin zauren, abinda yayi dalilin da Babana da Babah Lantana suka karta a guje don ganin dalilin ihun nata.
Tuni ihun Babah Lantana ya biyo bayan ihun Asabe, Babana kuwa sai faman salati yake yi yana karawa alamar abinda ya ganin yayi matukar razana shi.
Makwabta ku kawo min agaji da iyakacin karfinta take fadin hakan sai dai babu wanda va shigo duk da ana jin ihun nata da kuma kiran agajin da take yi amma shiru, bata kuma daina ba tanfar dai a ce ta mance da irin zaman da take yi da su nasa mu jinta yayiwa kowa kashedi kan shiga gidanta da ake yi bata so.
Ban san yanda aka yi ba naji maganar Baba Baidu cikin zauren yana fadin, a’a bai mutu ba ai ga wannan jijiyar tashi tana harbawa da sauran ranshi, da alama dai shi Baba Baidu ya amsa kiran neman agajin da take yi ya kawo mata.
Ihu Babah Lantana take yi tana karawa bata yi shiru ba har Likitan da Babana yaje ya kira ya iso.
Shigo da Sallau tsakar gida da aka yi yasa na koma ta inda nake hangensu, tabbas in dai ba hatsarin mota yayi ba ko wata kakkarfar dabba ta tattaka shi to wanda duk yayi mishi wannan abinda aka yi mishin ya tabbata mara tausayi.
Likita ya fara taba shi shima ya fara fadin na tuba na tuba ku bar ni kar ku kashe ni, kusan awa biyu Likita yana kanshi ana yi ana danne shi saboda zaburar da yake yi.
Gaba daya jikin nashi ciwo ne wajen targade shida ne da kuma tsagewan kashi guda biyu, bayanin Likita ke nan. Yayi abinda zai yi ya gama ya mike yana fadin, in hali yayi a kai shi asibiti a kara bincike na sosai amma a yanzu dai wadannan da muka gani mun kula da su.
Baba Baidu yayi mishi godiya’ yayinda Babana ya bi bayanshi alamar zai je ya sallame shi, ita kuwa Babah Lantaná sai faman kuka take yi tana fyace majina da bakin zaninta itama Asaben da ba wani shiri sosai suke yi ba kuka take tayi.
Sannu Sallau, sannu ka ji? Sanu, Ubangiji ya baka lafiya maganar Babana ke nan. A hankali. Sallau ya bude baki ya ce “Yauwa Baba, na gode.”
Da sauri Babah Lantana ta kara matsawa kusa da shi tana tayi mishi magana saboda ganin da tayi ya dawo cikin hayyacinshi. Da kyar ya yarda ya buda baki ya bata amsar tambayar da ta dame shi da ita “Su Agogo ne. gabana yayi mummunan faduwa jin ya ambaci sunan da Mubarak ya ambata a matsayin wanda zai sa yayi mishi maganin abin.
Su waye su Agogo? Ta sake bukatar sani, bai ce komai ba sai da ta gaji da tambayar cikin natsuwa ta soma yi cikin karaji da tashin hankali sannan ya bata amsa ki tambayi Asabe tasan shi.
Da sauri Asabe ta daka mishi tsawa kai kul kasa sunana a Cikin abin ku da waui rubabben bakinka.
Gaba daya kowa yayi shiru daga inda nake dai ina jiwo mishin Sallau ba kuma san ba dadi ba ne ya kawo hakan can cikin zuciyata kuma ina tunanin Asabe da dan uwanta Sallau babu halin su hadu wuri daya sai sun yi fada na tuna ni da Yaya Dijah na ce to ko don mu ba mu da uwa ne yasa muke son juna oho?
Zuwa can Sallau ya sake gajiya da tambayoyin uwar ta shi ya ce, to in na gaya miki abinda yasa Agogo suka yi min haka me za ki yi? Ba kin ce ko sama da kasa zata hadu ba za ki daina dukan Mairo ba, to wannan abinda a ka yi min ai ba komai ba ne kan abin da ki ka ce, don haka gobe ma ki sake dukanta.
Shawarar da na baki ba ki dauka ba ne yaja min wannan wahalar gobe ma in kin sake za su sake da har sun je sun kama mijin Babah Delu da ki ke cewa wanki ne suka sake shi saboda ya gaya musu babu abinda ya hada ku in ban da zaman gidan haya, yanzu ma kuma bakwa tare don in sun baki shawara ba kya dauka.
In ban da halin da Sallau ke ciki watakila da Babah Lantana ta gwabe mishi bakinshi a dalilin wannan bayanin nashi, nmaimakon haka kurma ihu mai tsanani tayi, ta yi kuka irin na fitar hankali, bayan ta tambayi Sallau yanzu saboda wannan shegiyar yarinyar a ka yi maka wannan azabar?
Bai musa ba bai ce mata uffan ba, to ai kuwa ba zan daina dukantä ba, sai dai… kan ta karasa taji ya ce mata to nuna min kawai inda dangin ubana suke tunda shi kin ce min wai ya mutu in dai da gaske ina da shi ai ba zai rasa dangi ba don ni Babah Delu ta ce min duk abinda ki ke gaya min kar..
Kan ya karasa tayi maza ta tarke shi da mari a kan ciwon nashi, ni dama kashe ni kawai ki ka yi da yafi min tunda dai duk wahalar da nake sha a rayuwata ke ki ke ja min.
Wannan din ma ke ce na kuma san za ki sake ja min wani tunda sun ce sau goma ki ka buge ta sau goma za su rama mata a kaina, to ba gara kawai ki nuna min in da ubana yake ba.
Ganewan da Babah Lantana tayi cewar Mubarak ne yasa a ka yi wa danta irin wannan matsanancin dukan duka kuma irin na rashin tausayi, a matsayin kashe di mai karfi gareta kan abin da take yi min na azabtarwa yayi matukar tayar mata da hankali.
Ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, don bakin ciki ta rasa me zata yi ta dauki fansa kan wannan abinda yayi mata? Tayi kuka tayi kuka har sai da ta kwanta ciwo wanda ban taba ganin ta kwanta da sunan ciwo ba sai a wannan lokacin.
Kwana biyu ita ma tana fama da kanta, rannan ta samu sauki ta fito tana zaune a tsakar gida kan turminta ashar take durawa Mubarak tana fadin tana nan tana jiran dawowarshi yayin da ni kuma take ta faman tsine min albarka.
Asabe ta gaji ta ce mata, to ya dai tsaya a kan zagin kar kije ki sake jawowa mutane wata fitinar don ke ba kya jin shawara.
Wani abin mamaki shi ne, Asabe sai ta kwaso kowacce irin magana ta yabawa Babah Lantana tana kallonta ba za ta ce mata komai ba, amma Sallau duk da kasancewarshi da namiji kuma shi ne babba bata yi mishi lamunin hakan.