Kwana uku da tafiyar Babah Lantana sai ga ta ta dawo, tsofaffin kawayenta suka dawo da ita, su Delu da sauran su. Suna kallona ina kallonsu ban ce musu kala ba sai gyada kai suke yi nuna alamar mamaki, in gumu ta gumu kuma su juya suyi kus-kus din su.
Watakila don a kaina suke maganar yasa suke yin kus-kus din don daga baya naji su suna cewa ai dan halal bai manta mafari, to ita Lantana da ta samu fili ta mike kafa sai ta ce babu shegiya sai ni, Ummm in banda dai hannunka bai rubewa. . .