Skip to content
Part 20 of 53 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Kuncin da nake ciki da takura kuma shi ne na tasa ni a gaba da Mansur yayi in bar shi ya tura iyayenshi wajen Babana magana ta wuce tsakanina da shi har yaje ya hada ni da Yakumbo Halima, ita kuma ta kira Yaya Dijah ta gaya mata cewar lalle ne ta gaya min in bar Mansur ya tura iyayenshi wajen Babana ayi maganar aurena in kuma ba shi nake so ba to in turo wanda nake son daga nan zuwa watan Sallah in har ba so mu nuna mata ba ita ta haife mu ba, amma ina amfanin wannan zaman da nake yi a gidanmu?

Shi karatun boko ai ba dole ba ne wurin ‘ya mace, na Addini kuwa na same shi daidai gwargwado a gidan mijina ma kuma zan iya yi tunda neman sanin addini ne shi aure ai suturar ‘ya mace ne.

Yanda naga Yaya Dijah ta dauki maganar da karfi na tabbatar zai yi wuya a ce watan Sallah yazo ya wuce ba tare da an titsiye ni na fitar da mijin ba, to ya ya zan yi? Ba da sunan Mansur din zan yi shi da yake son a bada sunan nashi ko kuwa wata hikima zan yi da Mubarak zai san abin da nake ciki?

Cikin hanzari na kawar da wannan tunanin saboda sanin da nayi cewar ba zan taba nuna mishi wani abu ya dame ni game da shi ba, ba zan taba karya ‘yancina na kasancewata halitta mai Daraja da Ubangiji ya karramata da kunya ba, wato halittar da aka yi min na zamowata ‘mace haba, mace ta rasa kunya? Ai kuwa dai tayi rashi mai girma, kalaman Yaya Dijah ke nan kunya ai adon ‘ya mace ne, a bakin Umma na saba jin hakan, don haka na kara kudurawa raina babu wani abin da zai sa in nuna mishi wani abu in dai yaga ci gaba da yin shirun nashi yafi mishi to yaje yayi tayin shiru.

Aka wayi gari a gidanmu da ma sauran gidajen Musulmi na garuruwa daban-daban, hidimar sallah a ke yi, Jama’a sai kaiwa da kawowa suke yi cikin walwala da farin ciki ga dukkan alamu kuma an yi sallar ne cikin walwala da wadata.

Tasa kayan sallar tawa nayi a gabana gaba dayansu ina binsu da kallo daya bayan daya, kafin zuwan sallar niyyata in sanya kayan da Yakumbo Halima tayi min ne ranar sallah don girmamawa a gareta, amma a yau da aka wayi gari ana hidimar sallar ga kuma kayan sallar tawa a gabana sai naji bazan iya kaucewa sanya daya daga cikin kayan sallar da Mubarak yayi min ba duk kuwa da niyyar da nake da ita ta daina mu’amalla da kayanshi.

Duk da hakan sai na ce to tunda yanzu hidimar sallah a ke yi bari in bari bayan sallah na dauki wannan matakin amma yanzu bari in yi adon sallah kawai.

Bakin yadin na sanya wanda jikinshi yafi kama da voil ko silk tasha ado irin na barnina a gaban rigar dan madaidaicin ado da yayi matukar kawata rigar ta zamo gwanin sha’awa, na sanya takalmi da gyale tare da Jaka da suka dace da kayan.

Sannan na dauko ‘yar sarkar da ‘yan kunnena tana sanya ga kuma warwarai da agogo, in tsaya cewa nayi kyau ma bata baki ne kawai, na tsaya gaban dogon yaron Innata da Babah Lantana ta fitar a dalilin hanata saida gadon da nayi na dauko shi na kawo dakin.

Kallon kaina nake yi a cikin shi cikin zuciyata na tabbatar ban taba yin kyau irin na yau din ba, ko ba a gaya min ba kuwa dama nasan ni din mai kyau ce, don kuwa kowa ya ce da Innata nake kama Innata kuwa mata ce da ta rayu mutanen da suka santa suna ba da labarinta.

Yau kam duk mishikilancin shi da taurin kanshi in ya ganni ba zai iya kame bakinshi yayi shiru ba, sai ya yabi kyan kwalliyata sai ya furta wata kalma da zata zamo mai karfi a tsakanina da shi.

Ina tsaye a wurin ina kara feshe jikina da turare tare da kara kallon kaina a madubin Asabe ta shigo dakin tana zage-zage nayi kamar in tanka mata tunda nasan da ni take yi sai nayi maza na baiwa kaina shawarar kame bakina tare da hanzarta barın gidan don ba zai zamo mata komai ba ta rufe ni da dukan da zai yi dalilin da zata tumurmusa ni ta lalata min kwallioyar sallar tawa ba.

Don haka nayi maza na yafa gyalena na kuma shuri takalmana nayi waje, gidan Umma na nufa zanje in yi mata barka da sallah daga nan taga kwalliyata.

Nayi maza na yamutsa fuska na ce, a’a Umma ni fa ba don kowa nake yi ba, tayi murmushi, au haka ne Maryamu kai wannan kayan sallah naki da kyau suke kai ji wata sarka kai kai kai, wa ya saya miki wannan sarka Mero?

Na shiga dibi-dibi cikin sa’a ta sake tambayata, Dijah ce ko? Nayi maza na ce mata ch, lokacin ne na kara sanin darajar sarkar.

Nabi umarnin Umma na shiga nayi wa Baba barka da sallah a falonshi na fito daidai Mubarak yana shigowa gidan ban daga ido na kalle shi ba balle in gane irin kwalliyar da yayi na dai san kawai na shaki kamshin turarenshi.

Baba ya bani goron sallah, nayi maganar ina nuna mata kudin da ya banin, tayi godiya. Kai wannan kwalliya taki tayi kyau, bani plate guda biyu Umma zan ba wasu, zuciyata ta soma yin nauyi da na soma tunanin har uwarshi ta gane don shi nake yin abubuwa masu yawa amma shi bai gane ba, ko kuma ya gane ya ki nunawa saboda bai da bukatata.

Babu wanda ya ganni bai yabi kwalliyata ba sai shi sai kokarin karbar waina yake yi wai wasu bakin sun kara zuwa mishi.

Iko sai Ubangiji, girman ‘ya mace babu wuya ai duk in da budurwa takai kin kai Maryamu, kin kuma yi kyau irin wanda ba a zaton miki ba.

Nayi murmushi na ce Umma kenan, na juya tare da cewa na tafi, da sauri ya biyo ni wata kila yayi zaton zan tsaya mishi ganin ban nuna alamar hakan ba ya sa shi fara yin magana ina za ki ne haka?

Ban tanka mishi ba, da ke fa nake magana, na sake yin kamar ban ji shi ba, tafiyata kawai nake yi to tsaya mana ki ji maganar da zan gaya miki, cak naja na tsaya saboda abinda zuciyata ke raya min, ya biyo ki ne ya gaya miki wata muhimmiyar magana, zai yabi kwalliyarki ne wata kila ma yayi abin da zai fi hakan dadi a gare ki.

Naja na tsaya ya iso ya same ni, maimakon in ji ya kama hanyar gaya min wata magana mai dadi sai naji ya fara jero min tambayoyi ina za ki ne haka? A hankali na ce mishi gida, to me za ki je kiyi a gidan da ki ke irin wannan saurin? Nayi shiru saboda ban ga kamar zan iya amsa irin wadannan tambayoyin ba.

Muje in kai ki kiyi hoto, ban kalle shi ba na ce na daina yin hoto a daidai lokacin kuma na kama tafiyata cikin zuciyata ina tunanin bai iya komai ba sai sayayyan kaya mai kyau amma bai san yaga kayan jikin wanda ya sayawa ya yaba kwalliyar da aka yi da su din ba, to ko meye amfanin Sanya kayan nashi?

Ina dosar kofar gidanmu na hango Mansur shi kuma yana fitowa daga zauren gidan namu ga alama nemana yaje yi daga in da ya hango ni ya saita kyamararshi ya soma daukana a hoto, kan mu gamu yayi min hotuna da dama.

Muna gamuwa da shi ya soma furta min dadadan kalamanshi masu sanyaya zuciya da sanyata cikin wani hali na natsuwa da farin ciki.

Alfarmarki nazo nema, ta me fa? Ya sake kallona cikin wani yanayi tanfar dai tsoro yake kar ya nemi alfarmar bai samu ba. Cikin natsuwa ya ce min gaishe-gaishen yan uwa da abokan arziki nake so in roke ki muje tare.

Ba wani tsaya yin wani tunani ba na ce mishi muje, dadi ya kama shi don in kara mishi jin dadin kumá na sake ce mishi, jira ni ina zuwa, na wuce na nufi gidanmu da nufin in canza kayan jikina in sanya wanda yayi min.

Cak! Naja na tsaya a cikin zaure ina sauraron maganar da nake ji tana fitowa daga bakin mutumin da zuwanshi gidan namu ya zama ka’ida in bai zo ba wannan satin to sati mai zuwa za ka ganshi ya zo, a yanzu kuma har da tsaraba ya ke zuwa mata da shi

Ba dai kin ce kin ba shi wadannan kajin yaci ba, ta ce eh, to ki gaya mishi kawai ba zai yi jayaiya da ke ba, cikin zuciyata na ce oh’oh shi kam Babana ko me a ke nema a wurinshi kuma yanzu oho? Sanin da nayi Mansur yana jirana shi ne abinda ya hana ni tsayawa in ji zancen nasu sosai, na shiga gida kawai na wuce su na shiga dakina na canza kwalliyata cikin kayan da Mansur yayi min wanda suma suka yi matukar karbata.

Na fito na same shi yana tsaye ni yake jira yana ganina ya saki wani lallausan murmushi, kin san kuwa al’amarinki yana bani mamaki, da sauri na tambaye shi mamakin, sai ya kalle ni ya ce min, to komai ki ka yi kyau ki ke yi Maryamu, komai kika sa yayi miki kyau ko kin taba sanin ke din daban ce da duk wata budurwa da ki ke gani?

Ai ni a wurina da za ki bar ni da na yi wa kaina alfarma na daina kiranki da suna Maryamu in koma kiranki da sunan (Ta fi su) saboda ke din daban ce a cikin ‘yanmata duka.

Murmushi kawai nayi naje na shiga bayan motar da Mansur ya tanada don zuwa gaishe-gaishen yayin da shi da Isiyaku suke gaba.

Babu inda ba mu je ba har gidan Yaya Dijah da Jumare da Yakumbo Halima, shima ta bangarenshi mun je mun gaida tsohuwar Kakarshi ba mu dawo ba sai bayan La’asar.

Ina fitowa daga cikin motar na hangi Mubarak a kofar gidansu ta wajen gidanmu yake fuskantowa abinda na tabbatar shi ne dawowana yake son gani.

Yana hango nin kuwa na ganshi ya dunfaro gidanmu yana tahowa nayi maza na shige cikin zaure don kar ya same ni a waje. Ina shiga sai gashi ya shigo, sannu da zuwa nayi mishi gaisuwar duk da ba dabi’ata ba ce yinta bai bata lokacinshi wajen amsata ba.

Me ke tsakaninki da Mansur? Abinda kawai ya bukaci sani kenan, na dan yi shiru saboda nauyinshi da nake ji, sai naji ya ce min kiyi magana mana, gaya min kawai ai gara in sani, me ke tsakaninki da shi?

Cikin karfin hali da jarumtaka na bude bakina a hankali cikin natsuwa na ce mishi, saurayina ne, to da kyau! Abinda kawai ya fadi kenan ya juya ya fita. Ya bar ni tsaye a cikin zauren sai dai maimakon in wuce in shiga gida nima kasa motsawa nayi a wurin ban san dalili ba har kusan minti uku da fitan shi ina tsaye a inda ya bar ni.

Sunkuyar da kaina kasa nayi ina kallon faratun yatsuna can cikin zuciyata dai ba zan iya cewa ga takamaiman abinda nake tunani ba.

Motsin da naji ne ya sani dagowa cikin sauri, Mubarak ne ya sake dawowa gabana yayi mummunan faduwa saboda yanayin da na gani a tare da shi, tsoro ya kama ni nan take naji jikina ya dauki rawa, dukana zai yi ko me?

Bacin rai da ke fuskarshi ba mai tsanani ba ne, sai dai da ganin yanayin da ke tare da shi ka san ya shanye wani abu saboda yanda idanuwanshi suka canza launi.

Me ki ka ce min yana tsakaninki da Mansur? Shiru nayi ban iya ce mishi komai ba, kiyi Magana magana ki sake gaya min irin maganar da ki ka gaya min dazu. Wani shirun na sake yi ban tanka mishi ba.

Ai ban san kin iya rashin kunya ba sai yau, kina nufin don kin koyi rashin kunya sai ya zama za ki ta cin fuskata kici mutuncina ki bata min, to ai ban san saurayinki ba ne shi yasa na bar ki kina hidimominki, to anma tunda ke da bakinki ki ka gaya min to ina so in sake ganinki da shi ki ga abinda zai faru.

Ina so in sake ganinki da Mansur ko in ji labarin an ganku tare ki ga yanda zamu kare ni da ke, mara kunya kawai, wacce ko wayo bata da shi, yana fadin hakan yayi shiru sai dai bai juya ya fita ba.

Sake tsare ni yayi yana kallona wani irin kallo da ba zan iya tantance irinshi ba, saboda kainaa a sunkuye yake hawaye suna ta zubo min, yana kuma kallonsu amma bai sa shi tafiya ya kyale ni ba.

Tun kwanaki ki ke nema kiyi min wulakanci me nayi miki? Me nayi miki da ki ke so sai kin bata min rai? Ki gaya min in laifi ne in baki hakuri in kuskure ne in gyara, amma ba zan lamunci, rainin hankali ba daga wurinki.

Ya juya ya fita nima na lallaba na shiga gida na hau gadona na kwanta, kuka sosai na kama yi.

Asabe tana kallona tun tana shiru har ta soma magana ita kadai, in dai namiji ne matsalarki ai kuwa ba ki yi kukan ba tukuna musamman ma wannan dan iskan da ki ka likewa mai kwashe-kwashen tsiya, ban dai tanka mata bá.

Ban sani ba ko kashedin da Mubarak ya yi min ne ya tsorata ni na kasa sake fita tare da Mansur, ban iya sake zuwa ko ina ba sai dai kawai in yi kwalliyata in zauna a gida.

A ‘yan kwanakin da na zauna a gidan nan ne na gane Babana da Babah Lantana ba karamin dasawa suke yi ba, ji da shi Babah Lantana take yi ba kadan ba, ko abinci zai ci sai ta zauna ta tasa shi a gaba yana ci tana kara mishi tana yi mishi wata hira mai dadi da zata sa shi ya ji natsuwa cikin zuciyarshi.

A zuciyata na ce wato itama dai matar nan ta iya komai na kyautatawa raini ne kawai da wulakanci yasa bata yi, ko wanene ta samu yayi mata wa’azin da ta gyara halinta? Oho, tunda ko nima dai wannan sallar sau biyu tana zuba abinci a kwano tana bani, ban karba ba ta sake kawo min soyayyun kaji nan ma naki saboda zuciyata bata kwanta min kan in ci ba, amma duk da haka hakan da tayi yasa al’amura sun dan yi sanyi fiye da da.

Kwana bakwai a ka yi Babana ya fara fita, Babah Lantanan ce kuwa ta ce babu in da za shi sai an kwana bakwai, ya zauna shima ya huta a cikin iyalinshi.

Rannan ya fita ya dawo naji shi yana ce mata yau dai kasuwar ta dan yi nauyi ga abinda a ka samu, na kasa kunne in ji abinda zata ce mishi tunda kullum ya dawo ya ce mata babu kasuwa fada take kamawa tayi ta sababi tana fadin ya dai boye kudinne kawai amma wane irin rashin kasuwa bayan dazu ta wuce ta wurin taga yara sun kewaye shi suna sayen abubuwa?

Abin mamaki sai naji yau ta ce inishi to ai yau da gobe kenan, Mallam a ka ce wai kayan Ubangiji in babu kasuwa ai sai ka dawo gidanka ka hau sabon gadonka kayi kwanciyarka ka wataya.

Ta soma zuba mishi abinci yana ci yayinda ni kuma can cikin zuciyata nake fadin to da haka kike yi mishi wa zai damu da rashin kirkinki balle har aje ana yi miki rashin kunya.

Suna cikin hirarsu nima ina sha’anina a daki sai na jiwota tana tambayarshi, to in kirata ne ka gaya mata? Yayi shiru bai amsa ba, in ban da uh’uh din da na ji ya fada, don haka na kara kasa kunne wajen sauraron magana tasa sosai don na gane da ni a cikin zancen nata.

To amma ai yau ne kayi alkawarin gaya mata, da safe ka ce a’a yanzu da yamma ka sake cewa uh’uh to me ka ke nufi? Ko za ka saba alkawari ne? Dattijo da saba alkawari? Ya sake yin shiru.

Ai fa aikinka ke nan in ana magana da kai kayi gum da baki kamar wani mai cin najasa, taja wani mummunan tsaki alamar dai ranta ya soma baci, ko ma ya riga ya bacin, ai dama nasan karya ka ke yi ba za ka iya gaya mata ba ka ce za ka iya, abin bakin ciki wai uba yana tsoron ‘yarshi.

To in ba za ka iya gaya mata ba ni in gaya mata tunda ni kam ai ba tsoronta nake ji ba yayi maza ya ce mata uh’uh to in kira maka ita? Yayi shiru ba ga ta can a daki ba? Kai Mallam kai kam ba ka da dattaku, kai tir!

Kalaman nata suka sanya ni naji wani iri, ga bakaken maganganun da take ta gayawa Babana ina ji, ban da haka kuma na tabbata ko wace irin magana Babah Lantana take son ya gaya min to ba mai sauki ba ce, kan haka sai naji maganganun nata sun sanya tsigar jikina yana tashi.

Ban iya ci gaba da zaman da nake yi ba, mikewa nayi na fito nazo na durkusa a gabanshi cikin natsuwa da girmamawa na ce mishi gaya min maganar da ta matsu in ji Baba, ko menene gaya min kawai zan iya dauka.

Ai kai Mahaifina ne, kai ka rene ni ka kuma yi min duk alherin da uba ke yiwa da, na kuma godewa Ubangiji kana sona ba ka yarda ka bayar da rikona ga kowa ba, don haka babu wani dalili da zai sa ka rinka sa ranar gaya min wata Magana kana dagawa tunda dai kasan dole ne zan ji ta to gaya min kawai zan fi jin sauki in na ji ta a bakinka maimakon a ce wani ne zai gaya min.

A hankali ya dago ido ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min aure zan yi miki Yaacuwuna, na daga ido na kalle shi, damuwa ce karara a fuskarshi ko ni da ya ce zai aurar ba tare da nasan mijin da yake nufin banin ba babu irin wannan damuwar a tare dani, tunda dai nasan a tsakanin biyu ne za a yi daya, ko a baiwa Mubarak ni ko Mansur, wanda duk aka yi da shi zan zauna tunda su dukansu ina da dalilan da za su sa ni zama da su.

<< Halin Rayuwa 19Halin Rayuwa 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×