Duk da kokarin da yaya Dija tayi na ganin na fita gidan ba tare da an ganni ba sai da wasu suka gannin basu kuma ja bakunansu sun yi shiru ba sai da suka yi tambaya, ai dama amaryar tana gidan ne? Sai dai ba su yi sa'a sun sami mai basu amsa ba muka wuce kofar baba Lantana a kulle kamar bata nan nayi maza na kalli yaya Dija na ce mata, tana ciki fa ta kulle kofar ne kawai irin yadda tayi ranar da aka je jeran anti Safara, bata amsa min ba.
A gidan baba Sumaye. . .