Kowa ya daukewa kowa wuta tsakanin haj wasila da Alh Aminu. Ita dai damuwar ta shigowar Halima gidan ta don tafi kowa sanin Alh Aminu yafita duk wata hauka da iya kulla tsiya . Son shi take tamkar tayi hauka shi yasa Bata son wata mace ta shigo da sunan kishiyar ta . Musamman da ta tabbatar Halima tafi ta komai da mace tun kahon ita mace ce.
Yayin da shi Kuma Alh Aminu yake shakkar tunkarar mahaifiyar Halima din don Yana ganin kamar itama ba zata bashi goyon bayan Auren Halimar ba tunda su mata da manyan su da yaran su. . .