Mai Kano ya zube Agaban Halima cikin girmama wa Yana gaishe ta.
Bakinta washe cikin farin ciki take amsawa inda kamshin mai kanon duk ya karade gidan. Duban shi take cikin kauna irin ta da da mahaifiya ganin zatin shi ya Kara fitowa ga haiba tamkar ya wuce shekarun shi girma na ban mamaki lallai Allah shi kadai yasan abinda ya ajewa mai kanon har ya ki karatu ya zabi kasuwanci.
Ya zuba Mata ido ganin yadda tayi rama.
"Mama me ke damunki kikayi irin wannan rama haka? Tayi murmushi har ga Allah alh Aminu ya zame Mata karfen kafar. . .