Karar cin tayar da Hajiya Wasila tayi shi ya sanya Halima juyowa ta yiwa kofar gidan zuru da ido don taji ajikin ta nan za a shigo.
Hajiya Wasila ta shigo tana huci gyalenta ma a hannu ta ruko shi tsabar musifa na cinta. Babu ko sallama ta shigo Halima ta bita da kallo
"Ashe kuwa da gaske kike Halima? Don Allah sanar dani gaskiya na jiyo wata magana me kama da Almara wai Aure ke da Aminu.
"Nima fa kamar hakan na jiyo, Hajiya wasila ta kyalkyale da dariyar rainin wayo tana tafa hannuwa.
"Allah na dawo inji kishiyar. . .