Skip to content
Part 16 of 48 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Gabadaya ya nemi nutsuwar shi ya Rasa duk yadda ya dauki lamarin ya wuce Nan. Ashe da gaske son Halima Bai Kama shi don ya bar shi ba.

Kwanaki suna taja inda haj wasila ke lissafe da saura kwana uku wa adin da ya fada ya cika Amma shiru takeji . A lurar da tayi mishi ma kamar baya cikin nutsuwar shi don tuni aka kammala gyara part din amma shiru kake ji .

Tayi murmushi tana fadin muje zuwa dai bawan Allah in dai nice

Kusan kullum kafar shi na tafe hanyar gidan Halima.

Zaryar shi ta ishi Halima har tayi da ta sanin Rashin bin Mai Kano don yadda ta tsani Alh Aminu Bata tsani mutuwar ta Haka ba tunda ya nuna Mata Bakin halin shi. Tayi Rama sosai saboda zullumi. Ya shigo gidan Yana mamakin yadda akayi wannan karon aikin lauje ya kasa tasiri akan Halima Wanda a tarihin lauje kaf Bai taba aiki ba ayi nasara ba sai Akan Halima inda ya Gane ADDU AR da tayi ce lokacin ta tarwatse komai.

Tana Duke gaban inji tana daura hakori ya shigo ta dago kanta tana duban shi tana ambato sunan Ubangiji da neman tsarin shi. Yadda ya kusanto ta ya sa tayi saurin ja da Baya.

“Sai yanzu na yarda da maganar ka ta Kai din zaka zame min karfen kafa. Amma kasani na saka Ubangiji tsakanin mu.

Yayi murmushi Yana Kara tunkaro ta .
“Ai Nima Ubangijin na sako tsakanin mu Halima tunda Allah na kowa ne ba naki bane ke Daya.

“Kwarai kuwa Amma Yana shiga tsakanin na gari da mugu zai kuma SHIGA.

“So ai baya nufin mugunta bare har na zamo mugu. “Kai dai naka na mugunta ne. “Ba tayi aune ba tagan shi dab da ita har suna Jin hucin juna…Sai kawai taganta a kirjin shi ya rungume ta Yana dafe da kugunta….

Mamakin ta bai kwantantuwa. Cikin fushi ta Soma kicin kicin kwatar kanta amma ta Gane Bai Rike ta don ya saki ba. Sai taji HAWAYE na bin idonta don yadda ya Soma da yi Mata Haka tana tsoron ya haike Mata wata Rana Abu ne Mai sauki.

“A yanzu ne na Gane baka tsoron Allah! “Na Rantse maka da Allah idan baka sake Ni ba zanyi maka abinda zakayi nadamar sani na…

“Komai Zakiyi min Halima bana nadamar sanin ki ai so ba karya ne ba. Ya fada Yana sakin ta cikin fushi take nuna mishi hanya. “Fita daga gidan Nan Wallahi ko yanzu na Tara maka mutane…

“Idan mutanen sun Zo zance ke Kika gayyato Ni San kuwa ba fita Zakiyi ba tunda sun San Baki da miji.

Kallon shi take tana mamakin yadda ya zamo da sharrin da Yake nufar ta dashi. Yayi murmushi Yana kallon ta tana share HAWAYE inda ya fita Yana Bata hakuri Yana Kuma fadin ba zai Daina bibiyar ta ba har sai ta yarda da kudirin shi. Fitar shi ya bata damar yanke shawarar barin gidan kawai don in ba hakan tayi ba to wata Rana zaiyi nasara Akan ta ko Kuma ya darsa zargi a zukatan Al umma

Don Haka duk wani Abu da zata bukata ita da Husna da sulaiman ta hade shi wuri guda suna tasowa makaranta ta kulle gida suka nufi masanwa gidan hajiya

Hajiyar ta gansu kamar daga sama ta dubeta a sheke kafin tace

“Me Kuma fa ? Kika kwaso Kaya kamar wata Yar gudun hijira? Ta zauna tana gaishe da hajiyar….

“Wai meye dalilin wannan hijirar ne? Ta Soma sanar da hajiyar halin da take ciki da irin garnakakin da Yake kawo Mata…

Hajiya ta tabe Baki”Da dai kin hakura da Jaye Jaye Kan bawan Allahn Nan Halima tunda bakiyi to Kar ki dauki alhakin shi . Kuma ai dama tun farko nace ki dawo gida Kika ce Sana ar ki tunda Kika zabi Sana ar ki don Haka Ni bani da wurin ajeki a gidan nan ki tashi sahun ki a likkafa ki koma don ba Zaki ja min zagi ba dama mutane sai yawo dake suke suna fadin maganganu bare Kuma yaron Nan Aminu dake ganin girma na idan yaji kinzo Nan ai zai dauka na Goya Miki baya ne don ki wulakanta shi don Haka tashi ki koma inda Kika fito

Halima ta dubi Hajiya idonta na zubar Hawaye ta Soma bawa hajiyar hakuri

“Ki yi hakuri Hajiya na rantse miki da Allah banyiwa mutumin Nan kage ko sharri ba. Ya ci ace hajiya kinfi kowa sanin hali na tunda Kika ga nazo Nan din akwai matsala ne tunda shekaru Ashirin da Aure na hajiya na taba zuwa gida da sunan zama? Ki yi min afuwa na zauna zuwa lokacin da Zan samu nutsuwa zan koma ne.

Wani Abu Mai Kama da tausayi ya ratsa hajiyar har ta yarda ta Amince Halima ta zauna gida har tsayin sati Hudu yayin da Alh Aminu yayi zaryar zuwa gidan Halima Yana iske gidan a Rufe har dai ya Gane ta faku ne saboda shi

Halima ke fadawa Hajiyar dake ta tsegumin ita ta kori Alhaji Aminu.

“Da ace Ni na koreshi hajiya da yazo ya Gaya Miki abinda nayi mishi Amma Kinga da Yake Babu gaskiya a lamarin shi yaushe Rabon da ki ga keyar shi? Kuma idan har gaskiya yake kullawa tsawon wannan lokacin da bana gida ai yakama ta yazo wurin ki yaji inda nake Amma shiru.

Hajiya ta yi shiru tana Nazarin maganar Halima inda ta Soma shinshino gaskiya Amma da Yake an gama yaudarar ta da kudi sai tace

“To tunda kin kore shi a na me ya neme ki? Da dai abin na Arziki ne zai damu da neman ki Amma yanzu in zaki yi nisan da ya wuce birnin sin meye damuwar shi . Dole Halima tayi shiru don tasan Hajiyar ba zata fuskance ta ba.

Kawai sai jiyo sallama suka yi inda Alhaji Aminu ya bayyana a gidan hajiyar cikin mamaki Halima ke kallon shi hajiya Kuma tayi mishi marhabun lale tana shimfida mishi tabarma suka shiga gaisawa…

<< Hawaye 15Hawaye 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×