Skip to content
Part 18 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Da hannu ya yiwa kattan nuni da suje abin su. Ai kuwa suka fice inda ya taso da sauri Yana kwance daurin da sukayi Halima a hannu tare da daye Mata gum din dake manne a Bakin ta.

“Da kuwa nasan zarto daure min masoyiya kayi da ci uban ka Dan iska aka Gaya maka Daya take da sauran Mata ne?

Halima da idonta ya ciko da HAWAYE ta kasa tsaida su saboda ta San ta gama Shiga uku a hannun wannan Azzalumin kamar yadda tasan Babu ALHERI a kawo ta gidan shi da yayi.

Ya gama kwance ta Yana durawa zarton Ashar. Kafin ya dubeta Yana murmushi. ke kika so ta kaimu ga Haka ba Halima har wani katon banza Yana taba min fatar jikin ki. Dubi gidan Nan naki ne komai da aka zuba gidan Nan domin ke aka zuba shi . Har ga Allah da zuciya ta guda naso Auren ki sai dai wani garnakaki dake kokarin kone Ni yasa na hakura da Auren ki . Na kuma so ki kalli ci gaban da yazowa Mata a yanzu na hada maza biyu Koda Suna da Aure kuwa bare ke da Baki da kowa Amma nauyin fahimta da son lallai sai kin gwada min kin Sha zuhudu yasa Kika kasa ganewa.

“Sonki ba da wasa ya kamani ba Halima ban San Haka yake da saurin dauka ba sai akanki.

Wasila ma da nake mutuwar so Auren Hadi ne tun na iyaye shiyasa ban San yadda son Yake ba sai da na fada komar ki. Nayi iyakar iyawata ki fahimce Ni Amma kin kasa kinja kin kafe Akan bakan ki Nima Kuma Akan nawa bakan nake sai gashi Kuma Allah ya bani Sa a gani gaki saura Dame kuma? Ya fada Yana daga Mata gira.Ta dubeshi cikin fita hayyaci

“Ban taba zaton zaka zame min karfen kafar da kake fada ba sai yanzu da kasa aka kinkimo Ni daga dakin mijina. A yau ne na gama tabbatar da Rashin tsoron Allahn ka Aminu.

“Kina take laifin ki Halima ki hango nawa. “In Ni Rashin tsoron Allah ne ke Kuma zalunci kikayi da Baki duba halin da nake ciki ba kikayi min Haka?

“Me kake nufi da kawo Ni nan? “Rayuwa ! Ya Bata amsa. “Kiyi duk yadda kike so Nan gidan ki ne akwai komai na bukata Ni Kuma din nine mahadi.

Wayar ta da ta dauki tsuwwa yayi maza ya daukota inda sukayi Rige Rige wurin daukar wayar inda ya ga sunan Mai Kano na yawo a fuskar wayar da sauri ya katse Kiran ya Kuma zura ta aljihu ta bishi da ido. Kiyi hakuri akwai lokacin da Zan mayar Miki d wayar ki Amma yanzu zamanta hannun ki akwai matsala. Ya damki hannunta zuwa wani shiryayyen daki Yana nuna Mata a zuwan masaukin ta.

Tana zaune ta rafka tagumi taga ya jona Bonner a wuta kafin ya zuba wani Abu tamkar turaren wuta inda hancin ta ya shako Mata wani matsiyacin kauri a take kanta ya SHIGA juyawa kafin ta mance lissafin ta. Tanaji ya sheke da Dariya inda ta tsinto lamarin da dama Haka aka shirya Haka Kuma aka tsara abinda bata taba yi da yarinta ba sai bayan mutuwar miji Wanda shine silar komai

Washe gari tun kafin ta farka ya fice ya bar gidan inda ta SHIGA Rera Kuma cikin fatan ta hadiyi zuciya ta wuce.

Dame wannan abun yayi Kama? Idan har don Haka yasa aka daukota hakika ya cuceta da dai irin wannan Rayuwar da Yake nufin yi da ita gara ya Aure ta kowane irin garnakaki ne ta yarda ita yayi Kan tafi da Rayuwar ta.

Tayi kuka har kanta yayi ciwo yayin da zazzabi ya lulluveta Ruff ta Fadi Kan shimfida sanyi na kadata yayin da hakoranta ke gwaruwa ta cure wuri guda tana karkarwa

Washe gari Husna da sulaiman suka wayi gari babu mamar su suka SHIGA jaje da Tararrabi suna nemanta kusfa kusfa na gidan Amma shiru Dole suka Rufe gidan suka nufi masanwa suna kukan Rashin sanin inda mahaifiyar su take

Hajiya ta karbesu tana tambayar abinda Yake faruwa. Husna tace “hajiya mamar mu Bata Zo Nan ba?
“Inda tazo da Baki ganta ba? Hajiya ta Fadi tana hararar Husna, “To mun kwanta da ita hajiya da safe Kuma bamu ganta ba, Hajiya taji gabanta ya Sara don tunowa da mafarkin ta na jiya Akan Halima. Da sauri ta jawo wayar ta tana mikowa Husna dake sharar HAWAYE.

“Maza kamo min kawun ku Amadu, Husna ta lalubo nomber shi ta Kira ta mikawa hajiyar

“Amadu kana Ina ? Maza kazo don Allah Wai Halima ce yaran ta suka min wai Bata kwana gida ba.

Kan kace me tuni gida ya Rude da labarin batan Halima, Amadu kanen Halima ne ya ba zamo aka SHIGA jaje da Mika Cigiya Amma dai shiru Wai malam yaci shirwa

Kowa da abinda Yake fade Amma dai da yawa sunfi tafiya Akan miyagun mutanen da ke sibarar mutane ne da sunan neman kudin fansa

Hajiya tafi kowa shiga tashin hankali sai Fadi take, “Ni najawa Halima da na koreta Dama nayi wani mugun mafarki da ita jiya amma Allah ka Bata mafita.

Kwana kusan biyar Mai Kano na Kiran wayar Halima Amma sai yajita akashe inda jikin shi ya gama sanar dashi Babu lafiya. Don Haka ya bugo hanya inda yazo ya samu gidan nasu a kulle Dole ya wuto gidan hajiya inda yayi Arba da Baki Labari yayin kowa ke neman layin na Halima Amma baya samuwa. Duk taurin Rai irin na Mai Kano sai da ya koka musamman ma da Yan kannen shi suka kewaye shi suna kuka Bai San lokacin da shima ya SHIGA Taya su ba.

Hajiya ma dai ta SHIGA taitayin ta bakin ta Kuma ya mutu murus !

Kwana biyu Mai Kano yayi inda yayiwa hajiya sallama ya wuce da nufin zai dawo sati me zuwa

Yana sauka garin Legos ya Kira wani mutum me suna magdo Wanda ya kware wurin yin tracking din wayoyi ya Kuma bashi lamber mahaifiyar shi da son yayi mishi tracking din ta inda yace sai ya kawo kwalin wayar don daukar code din ta type dinta Dole ya hakura har zuwa satin da zai koma katsina.

Alh Aminu ya Zo gidan hajiya da sunan yazo gaishe ta inda Yake samun labarin batan Halima
Ya nuna jimami tamkar zai zubar da HAWAYE ya dubi hajiya

“An sanar da hukuma kuwa hajiya? Tace mishi an dai bada Cigiya kafafen tada labarai….

“Dole za a sanar da hukuma hajiya zanyi iyakar kokari na wurin ganin Halima ta bayyana in ma masu neman dukiya ne Zan biya a fanso ta.

Hajiya har da kuka tana Kara mishi ADDU AR samun Rabon Duniya da na lahira
Ya nemi zai tafi gidan shi da Husna d sulaiman ko don ci gaban karatun su . Da farko hajiya hanawa tayi Wai Bai kamata abar shi da dawainiya Haka ba itace a hakkun kula da yaran. Amma da Yake ya iya yaudara sai ya fake da cewa Amana ba tace Haka ba . Ya’yan mu a zu nashi ne.

“To Amma Aminu kana ganin babu matsala wurin matarka ? Kasan Mata da kullata mussamman lamarin kishi don nasan ta samu labarin abinda ya so faruwa tsakanin ka da Uwar yaran Nan Kar a takura Mata….

“Hajiya gidana har gobe banyi saken da ya Fi karfina ba ki dauka cewar yaran Nan suna gidan uban su ne Zan tsayu har Naga yaran nan basu ce ya zasuyi ba fatana dai ki yarda ki bani su na Rike har Allah ya bayyana Mana mahaifiyar su.

Dole hajiya ta yardar mishi ya kwaso Husna da sulaiman a mota ya nufo gida dasu inda wasila ta dubeshi ta Kuma dubi yaran cikin tsana da tsangwama tamkar zata kyasta musu Ashana ta kone su.

<< Hawaye 17Hawaye 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×