Skip to content
Part 23 of 48 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Kawai sai dai inuwar mutum ya gani har ya tsorata kafin ta dawo Kan doka da Oda ya Gane Wanda ke Kan shi har Yana kokarin Zama Akan kujera tree seater.

“Me yasa zaka shigo min babu sallama Haka Mai Kano? Ya fada da akwai Alamar Rudewa.

“Nayi sallama Kaine dai baka ji ba.

“Da kata da izinin wa ka shigo Nan? Ya dubeshi Yana mishi kallon tsakiyar ido
“Don Zan shigo gidan Nan sai na nemi izini Baba? Ca nake Nan din gidan mu ne kamar yadda nake kallon ka a matsayin uba.

Lallai wannan yaron ya fini iskanci. Ya fada aran shi.

“Ya aka yi ne yanzu Kuma? Ina fatan baka Sha komai ba kafin kazo min nan bare ka kwata yi min ksfso da marisa irin Wanda kayi min can baya?

Mai Kano yayi murmushi Wanda a zahiri na takaici ne.

“Ko goro bana ci Baba Aminu bare har na Sha wani Abu kamar yadda kake zato.

“Karya kake Mai Kano idan har baka shaye shaye a gidan uban wa ka ganni d wayar Uwar ka da har kazo kake tuhuma ta Akan ta?

Mai Kano ya hade fuska Alamar ba zai laminci zagin iyayen shi da ya Soma ba.

“Kar ka Kuma zagin baban mu dake kwance a kasa. Ina so inyi ta ganin mutumcin ka daga yau zuwa tashin alkiyama. Idan kuwa ka sake na Rantse maka da Allah Zan Rikide kalar da zakayi nadamar sani na. Ya fada Yana Nuna yatsa tamkar zai tsone idon Alh Aminu Wanda ya tsorata da ganin yadda yaron ya juye suffar abin tsoro. Sai ya bishi da kallo kawai.

“Ina wayar mamar mu da nace maka Zan dawo na karba? Ya fada Yana Mika mishi hannu.

“Idan waya kake so Mai Kano muje in siya maka ko wace iri kake so.

Karbi kudin Nan ma Dubu dari biyu ne jeka ka siyi duk kalar da kake so.
Ya fada Yana Miko mishi tulin kudin.

“Nima Ina da kudin siyen kowace irin waya ce Baba ta mahaifiya ta kawai nake so ka bani idan kuwa babu wayar ka bani layin.

“Wai Mai Kano da tsiya sai ka sa Ni na amsa laifin da ba nawa ba?

“To Baba idan ba laifin ka bane laifin waye?

“Ba na so ne na fito maka da abin a bayyane ko nace zan Kai ga hukuma tunda abin duk na gida ne shiyasa kaga Ina biye cikin salama. Na San komai Baba shiru kawai nayi.

Ya dubeshi a Rikice gaba na dukan Tara Tara. “Meye abinda ka sani Mai Kano?

Ya tambaya Yana Jin gumi na neman Rufe shi.

“Duk wani Abu da kake kullawa mahaifiyata Baba Aminu Babu Wanda ban sani ba shiyasa nake binka a sannu tunda Kai din matsayin uba kake gareni.

Amma Kuma na lura kana son nuna min baka San komai ba Haka NE?

Ya Soma nuna shi da yatsa Amma ya kasa furta komai.

“A yau baba ba tuhumar waya kawai ta kawo Ni wurin ka ba tuhumar inda mahaifiya ta take nakeyi maka!

“Shiyasa nace kana shaye shaye Mai Kano. “Wallahi kana shaye shaye.

Ya Kara dauko wasu damin kudin shi kanshi Bai San iyakar nawa ne ya Tula mishi ba saboda har ga Allah yaron ya kada hantar cikin shi.

“Tashi kaje Zan nemeka kwashe kudin kaje dasu na baka in yaso sai ka siyi kayan karawa sama hazo.

Mai kano ya Mike tsaye Yana fadin, “Kamar yaushe Zan dawo? “Fara daukar kudin tukuna Zan neme ka.

“Ba na so! Ya fada Yana ficewa. Ya bishi da kallon mamaki.

Tabbas yaron ya fada mishi ya San komai me Yake zato kenan?

Agurguje ya fito ya leka dakin Halima wadda ke kwance kamar gawar sababi ya fice zuwa gidan lauje.

Mai Kano ya wuce zuwa gidan hajiya suka gaisa take Kara jaddada mishi kokarin da Alhaji Aminu yakeyi.

“Kokarin banza yake yi shege Dan iska? Ya fada da Amon murya har Yana firgita hajiya

“Kai Mai Kano ka San me kake fada kuwa? Ya jefa mata harara ya ki tankawa.

“Amma dai Kai butulu ne Wallahi duk wannan abin da yake baka ga kokarin shi ba har kake zagin shi saboda Uwar ka ta gama famfa ka akanshi?

“Yo kokarin me Yake? Wa ma ya sako shi a cikin lamarin mu ko mun kasa ne?
Hajiya ta Rike Baki kafin tace.

“Tashi ka tafi marar kunya in ubanka ne zaka gaya mishi Haka? Duk abinda kasan ka fada mishi kamar uban ka ka fadawa.

“Ubana da ban shi da ban Kar ma ki sake hada min shi da shi Dan iska kawai Kuma na Rantse Miki sai na farke cikin mutumin can na fito da Yan hanjin shi waje.

Ya Mike Yana Shirin ficewa kafin ya juyo ya tambayi inda Husna da sulaiman suke.

“Suna gidan mutumin da kake zagi Wanda ya Rufa muku Asiri Amma da Yake shidan ya fitsare zuciyar ka shine har kake fadin zaka farka cikin shi to Allah ya baka sa a tunda kaje Legos fa inda ake jefar da gawar mutum a bola meye ba zaks iya aikatawa ba?

Tamkar ta watsa mishi Ruwan zafi fadin cewa Wai su husnar suna gidan Gayen can.

Da sauri ya fice ya nufi gidan Alhaji Aminu inda ya wuce kanshi tsaye har cikin falon Hajiya wasila ya shiga Yana muzurai

“Kai Nan gidan uban ka ne da zaka shigo min kanka tsaye ? Koko iskancin da ka koyo a Legos ne zaka nuna min. Ya dubi hajiya wasila cikin fushi.

“Ban Rasa gatan uba ba bare har wannan shegen gidan ya burgeni. Kinfi kowa sanin uwata da ubana kina zaton nazo ne don in kalli gidan nan ko ya burgeni? Ni fa duk a matsiyata nake kallon ku keda me gidan. Ko kina zaton kunyi abinda zanzo ina Yar murya ku bani? Matsiyata irin ku ?

Tayi mutuwar zaune don batayi zaton hakan da ga gareshi ba. Tana sake da Baki har husna da tajiyo har gagin shi ta taho aguje ita da sulaiman suka rungume shi suna tambayar maman su.

“Maza kuje ku hado kayan ku muje dama Kuna Nan har waccan shegiyar ke kallon Alfarma tayi muku? Da sauri suka nufi daki suka kwaso kayan su don a zaton su maman su ta bayyana

Suka kwaso kayan su fago guda suna ta murna ya tusa su gaba kafin ya juyo ya kalli haj wasila

“Na Rantse Miki ke da shegen mijin ki nine ajalin ku idan ya dawo ki fada mishi Haka.

Ya fice ya barta Baki sake. Hajiya ta ganshi da yaran da uban Kaya

“Uban marasa mutunci zuwa kayi ka taho dasu saboda Kai butulu ne?

“Ke ce Baki San kowaye mutumin can ba da shi ya kamata ki Kira uban marasa mutunci koma ki kirashi da kakan marasa mutunci don Haka Zan wuce da Husna da sulaiman can Legos kafin na dawo na kaddamar wa shegen mutumin can don na Rantse Miki sai na farke cikin shi Yasin.

“Karya kake babu inda zakaje dasu karamin marar kunya

Da sauri ta Kira Amadu yazo tace ya maida yaran gidan Alh Aminu ya Kuma bashi hakurin abinda Mai Kano yayi mishi

Yana kallo aka fice da su Husna zuwa gidan Alh Aminu.

Shima ficewa yayi da jakar shi zuwa gidan su don ba zai taba Barin garin katsina ba tare da ya San matsayin da suke shi da Alh Aminu ba.

Kwananshi biyu a garin ya gama Shirin yadda zaiyi sai kawai ya dauki galan din da ya siyo fetur ya Kuma lalubi ashana ya fice ya tari napep zuwa unguwar sardauna Estate.

<< Hawaye 22Hawaye 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×