Skip to content
Part 25 of 47 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

A guje ya baro gidan lauje ko bankwana basuyi ba. Tafe yake Yana tunanin abinda ya haddasa mishi wuta a gida. Ba komai yakeji ba irin Halima dake cikin gidan tana baccin da ake sakar Mata.

Zaruruwan suka hade mishi suka kulle mishi fiye da Rikicewar sarka ta yadda har ciki ya bayyana ga Halima ba tare da ya ankare cewa ba a son ya hada jini da iyalan mu azu ba sai yanzu d Zubaina ta sanar dashi.

Aguje Yake gudu da son ya isa gidan fatan shi dai yayi ido Hudu da Halima a cikin gidan . Ba damuwar shice abinda wutar ta lashe ba a gidan.

A a cikin Halima wanda Zubaina tace Kar ya wuce gobe ajikin ta idan kuwa ya wuce to wuta zata tashi wadda zata kone su har shi Alh Aminun.

A Rude ya ci uban burki a kofar gidan Wanda jiniyar kwana kwana ke sanar dashi sun iso har suna bakin kokarin su

Tuni kuwa akayi nasarar kashe wutar yayin da gidan yayi Baki Kirin komai kuma ya ci wuta har ya zamo gawayi

Ya kutsa kanshi cikin gidan inda ya nufi dakin da yayiwa Halima masauki tun kafin ya karasa ya hango gaba Daya Rufin dakin ya Rikito kasa babu Kuma komai a filin dakin sai gawayin gadon dakin da kujrrun dakin hatta TV plasma taci wuta

Sai dai ga mamakin shi babu ko sawun Halima bare yayi tunanin tana daga cikin ta adin wutar. Babu ma wani Abu nata da zai iya kararwa Wanda wutar taci.

Ga mamakin shi sai yaji zuciyar shi na wassafo mishi Mai Kano da abinda lauje da Zubaina suka fada Akan shi. Lallai ne akwai Alamar tambaya akan sanadin wutar

Fadar cewa ga irin firgicin da yake ciki baya misaltuwa inda ya fito da sauri ya koma gidan Laujen Yana zayyano mishi Bai ga Halima ba.

“Ai abinda na fada maka kenan tun farko ashr baka kiyaye ba?

“Wannan musibar da kake ganin ta Soma yi maka sallama Kar dada Kar ka Raga ta samo asali ne daga haduwar jininka da matar mu azu tuni dama na fada maka haduwar jininka ba me yuwa bane har Kuma kaji kukan da Zubaina ta bayyana tanayi akan hakan. “Yanzu ita Halimar taci wuta kenan ko kuwa guduwa tayi? To duk ma inda Halima ta SHIGA kayi kokarin lalubota kafin wuta ta tashi akan ku.

“Yanzu lauje meye abinyi?

“Abinyi kawai ka Nemo matar Nan ka Kuma yi gaggawar zubar da cikin dake jikinta.

“A Ina Zan nemota ? Ban fa San inda ta SHIGA ba ko tana Raye ko ta ci wuta gidan uban wa Zan sani? Ya fada Yana an takawa Laujen Ashar.

Lauje ya kyalkyale da Dariya Yana fadin. “Tuba nake mutumina Bari na Kira Zubaina wata Kil tana da masaniya Akan inda zaka samu Halima. Ya hada garwashi Yana watsa garin maganin a wuta Amma shiru kakeji suka dubi juna a tare.

“Ka kagi dai Taki amsa Kiran Ina ganin yaron can da ya Soma yi maka barazana bana ko shakka Yana da masaniya Akan abinda ke faruwa don Haka jeka ka lalube shi in ma wani Abu Yake so ka bashi ya sanar da Kai inda matar Nan take don tunda kaga Zubaina Taki amsa Kiran Nan akwai gagarumar matsala don ban fidda zargin yaron can ne ya haddasa maka gobara a gida ba shiyasa nace maka yafi karfin ka ya fika iya fada da kulla makirci Daya kenan daga cikin makircinsa

Alh Aminu ya sharce zufa Yana durawa Mai Kano Ashar.

“Na Rantse maka lauje duk hatsabibancin shi sai na kure malejin shi a yau Zan bazama neman kafiri duk gidan uban da Yake sai na Nemo shi . A yadda nayi nasara Akan Uwar shi da Uban shi shima sai nayi Akan sa.

“Kar ka zarme da yawa mutumina ba kullum take juma a ba kamar yadda ba ko yaushe akwana lafiya ba. Ka bi yaron can a sannu da hila da yaudara ba Wai ware kwanji ba nashi kwanjin ya Fi naka shifa yaro ne sabon jini matashi ne Mai hamasa.

“Duka Zan hade yarintar tashi da hamasar inci uwar su Wallahi ya hada an taka mishi Ashar.

Ya Mike aguje yanufi gida inda ya iske muhsin ya kammala aikin bautar kasar da yajeyi ya Kuma dawo da dunmbun nasara.

Ya Miko mishi takardar me dauke da kyakkyawan sakamakon Yana neman ADDU AR shi
Ya dubi takardar Yana Miko mishi fuska murtuk.

“Babu wani Aikin gwamnati da zakayi alhalin ga kamfanoni na Nan suna bukatar irinka don Haka Kai zakaci gaba da kular min da ksmfanina na Nan na sarrafa Auduga da takin zamani.

“Daddy baka duba takardar sosai ba ne? Har fa Zan Fara aiki da babbar kotun jihar Nan saboda LLB din da na samu.

“LLB din banza suka baka? Kai duk Aikin Duniya ka Rasa na yi sai lauya ? Ka kuwa San me kalmar lauya take nufi? To makaryaci ake nufi Wanda ya iya lauya magana ya maida ta zance ya Kuma iya lauye gaskiya ya Mai da ita karya ko karya ta koma gaskiya don haka tashi a gabana na gama magana babu gidan uban da zakaje wani aikin banza alhalin na kashe kudina don kazo ka taimakeni Allah yasa ka sake Zo min da wani zancen banza kaga yadda zanyi da Kai Dan iska kawai.

Muhsin ya Mike Ranshi a bace Yana Jin Babu yadda Za ayi ya iya Barin aikin Nan da ya Rayu da burin yaga ya Kai matsayin da zai Dora hular Nan da Rigar sai kawai yanzu ace ba Haka ba?

Husna da taci uban Ado da kwalliya tana jiran shigowar sa ya shigo fuska babu sassauci.

“Ta karaso tana kafe shi da ido shima ya kafeta da ido Yana mamakin girman Husna shekara Daya Tak Amma ta samu sauyi Mai yawa inda kibiyoyin masu fitar da masu me dauke da wani sirri sukayi fitar burtu zuwa idanun su kafin Kuma suka kyalkyale da Dariya

Husna ta kawo mishi wani cake Wanda ta hada mishi as a gift din murnar ya kammala bautar kasar shi lafiya ya karba Yana tsareta da idanu har kunya na kamata. Inda Amal ta shigo tana Kare musu kallo.

“Wai dama cake din Nan Yaya muhsy Kai akayiwa har nace Zan gutsura aka hanani? Lallai abun ya Zo inji masu tsoron wanka.

“To ina Ruwan ki Uwar saka ido? Cewar muhsin yayin da Husna ta Rufe idonta tana Jin kunyar Anty Amal.

“A a bude idonko kanwata meye abin kunya? “Jeki da Allah Kar ki takura Mana zamuyi magana tsaka uwar kilbibi.

Amal ta kyalkyale da Dariya tana fadin idan tayi tsami ai zanji.

<< Hawaye 24Hawaye 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×