Skip to content
Part 27 of 54 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Ya Mike tsaye Yana sauraren abinda lauje ke sanar dashi cikin Rikita da hadewar lissafi.

“Kai lauje Wai gidan uwar wa Zan Nemo matar Nan? Yanzu Haka cikin binciken yadda Zan Nemo ta nake.

“Kazo dai muji yadda Za ayi cewar lauje ya katse wayar ya bar Alh Aminu da bin wayar da kallo kafin ya tashi ya fice zuwa gidan lauje

Safina ta shigo gidan cikin wanka na neman magana Diya ce ga maimuna wadda kanwa ce ga haj wasila Kuma aduk Duniya Babu abinda safina ke kauna irin muhsin yanzu ma tazo ne don yi mishi barka da kammala bautar kasar shi.

Suna zaune shi da Husna wadda yacewa kanshi na ciwo duk ta firgice inda tace Bari taje wurin Anty Amal akwai magani a wurin ta ta karbo mishi.

Ai kuwa ta tafi da sauri wurin Amal wadda ke karatun littafin hausa tana Fadin.

“Anty Amal don Allah ina maganin nan na ciwon Kai Wanda Kika Sha Ranar Nan kike cewa Yana da karfi?

Amal ta dauko shi ta Miko Mata tana fadin. “Kanki ke ciwo kanwata?

“A a Yaya muhsin ne yace min kanshi na ciwo…Amal tayi murmushi.

“Kai ke dai kina da aiki Husna shine duk Kika wani firgice haka? Husna ba ta tsaya sauraren Anty Amal ba ta wuce kaiwa Yaya muhsin maganin inda ta iske zuwan Anty safinar wadda ke zaune dab da Yaya muhsin tamkar zata rungume shi saboda ita wayayyar macec Bata dauki hakan komai ba inda Kuma Husna taji wani Abu a Ranta Amma ta Mika mishi maganin da Ruwan da dauka marar sanyi sai kawai ta juya ta barsu Amma fa Ranta na wani irin suya.

Amal ta kalleta duk ta hade Rai. “Wai duk ciwon ne yasa Kika koma haka wata kalar tausayi?

Amal ta jeho Mata tambayar. “Anty Safina ce tazo Baki ga yadda takewa Yaya muhsin ba kamar zata Rungume shi . Ta fada tare da Jan tsaki ta na kwantawa a gado.

Amal ta kyalkyale da Dariya tana fadin kishi manya Husna har kin San kishi haka? Husna ta tashi zaune tana kallon Amal

“Wallahi Anty ban San meke damuna Akan Yaya muhsin ba. Ina son na zauna nayi ta kallon shi Ina son naji muryar shi Ina son Kuma nayi mishi abinda zai sa shi farin ciki bakiji yadda nakeji ba yanzu da waccan Anty Safinar tazo sai wani lankwashewa take tana daga mishi gira sai kace wata Yar kwaya.

Amal ta kyalkyale da Dariya tana fadin lallai yarinyar Nan kinzo hannu.

“Hannun wa? Husna ta tambaya. Hannun Wanda kike so Mana. ‘Lah nifa ba son shi nake ba Anty.

“Ai duk abinda Kika zano Husna so ya gama bayyana sai dai kiyi taka tsantsan su maza da kike gani ko da su suka nuna suna son ka to sai a hankali bare mace ta Fara nuna tana son namiji yanzu ne zai jizga ki sai ana ja musu aji ko ana Zama lafiya dasu don Haka kija ajinki Kar ki yarda ya Gane kina son shi don Zaki Sha wahalar shi ki Bari shi da kanshi ya furta Miki cewa Yana sonki da Bakin shi Kuma ko shi din ya Fara furtawa kija mishi aji ki nuna kamar Baki son shi don namiji da kike gani Dan kunama ne duk yadda yake son ki to da ya hango wata a waje ke sai dai ace Miki sorry.

“To Amma Anty idan yace Kuma Anty safina yake so nice Yaya zanyi? Ta fada da damuwa a fuskar ta Kuma bilhakki.

Kamar Amal tayi Dariya sai ta gimtse.

“Barshi ko yace Safina Yake so ke din ma naki mijin zai iskeki har gida don ke din Babu namijin da zai kalle ki Bai Kara ba matar manya ce ke.

Husna ta kyalkyale da Dariya tana fadin Ni kuwa gaskiya Anty Yaya muhsin kawai nake so wallahi bayan shi bana son kowa.

“To ki dai ja ajinki Kar ki sake ki nuna mishi kina son shi ki Bari ya furta da Bakin shi. “To shikenan in Sha Allah zanyi hakan

Safina ta shigo dakin tana Kiran Amal kafin ta dubi Husna a sheke ta watsar tana Jan tsaki tana duban Amal

“Wacece Husna a Nan gidan? Ta tambaye Amal. Amal din ta nuna Mata Husna gata Nan wani Abu? Ta Kuma duban Husna a lalace.

“Ke kije Sweetie na Kiran ki. Husna tace. “Waye Kuma sweetie? Yaya muhsin take nufi inji Amal
Husna ta tashi ta barsu inda safina ke fadin Amal ga Amanar Sweetie na Nan a hannun ki don kallon da Naga Yana yiwa yarinyar can ban yarda dashi ba. Ta fada tana biyo bayan Husna. Husna ta hade fuska ta Isa tana fadin gani.

Ya dubeta kamar ya fashe da Dariya sai Kuma ya nuna Mata kusa dashi yace ta zauna don ya karanto mugun kishi a idon ta.

Safina ta iso tana fadin Wai yazo yayi Mata Rakiya.

“Kefa kin cika matsala ba Ni nace ki tafi ba kaina na ciwo? Ta kalli husna tana fadin
“Ka sallami yarinyar Nan ta tashi daga gabanka.

“Ba tare Kika iske mu ba? Umarni kike bani ko shawara uwata? Haka ta fice tana Jin kishin yarinya husna
Ya Raka ta da kallo kafin yaja tsaki Yana fadin sakarai shashasha

Ya maido kallon shi ga husna dake ta cika tana batsewa tamkar fulawar da taji yest. Yayi murmushi
“Me ya faru ne mutuniyar?

“Babu kamai. “A a ke dai fada min gaskiya.

Tayi shiru tana sauraren shi inda ya zuba Mata ido Yana kallon ta Yana Jin sonta na ratsa jinin jikin shi a yau Kuma Yake kokarin amayar Mata da abinda ke Ran shi don ya hango kishin safina a kwayar idanunta.

“Kinga safina ? Ta daga Kai Alamar Eh. “Idan nace ki zano min Mata Zaki iya zabo min ita a matsayin matar Aure na? Idan Kan son ta Yaya ai ba matsala bace Kuma meye aibunta? Ta fada tana boye kishinta.

“A duk Duniya husna mace Daya Tak nake so Kuma Idan Kika ganta nasan kema sai ta burgeki da ita nake kwana da ita nake tashi.

“Zan so kuwa na ganta Yaya muhsin don inji ko zata burgeni din Amma idan safina ta fita fa?

“Kai bana zaton safina zata Fi ta Bari na fasalta Maki yadda take kusan komai naku iri Daya ne tafiyar ku da tsayin ku muryar ku hatta sunan ku ma iri Daya ne.

Tayi murmushi tana Rufe fuska. Kafin tajiyo sautin shi dab kunnen ta

“Husna ba kowa nake so ba sai ke din da kanki na Dade ina dawainiya da sonki a zuciya ta Allah yasa ba bara a kufai nake ba.

Ta Mike da Shirin barin wurin ya Riko hannun ta ta jiyo suka hada ido.

“Banji abinda Kika ce ba Husna? Tayi saurin dauke kanta. “To ai Ni kunyar ka nakeji Yaya muhsin…

“Ai kunya Kuma ta Kare Husna tunda har bayyana Miki Asirin zuciya ta ko? Kalma Daya fa ce zaki fada min Kuma bata da wahala.

“Mece ce kalmar to? “Cewa kawai Zakiyi ina son ka Yaya muhsin. Ta Rufe idonta kafin tace
“Ina sonka Wallahi.

Sai Kuma ta sheka aguje ta barshi da yi Mata Rakiya da murmushi Yana shafar sumar kanshi.

Ta SHIGA dakin ta fada Kan Anty Amal tana fadin albishirin ki Anty ?

“Goro fari kwalele. “Yanzun Nan Yaya muhsin ya furta da Bakin shi Ni yake so ba Anty Safina ba.

“Kai nayi Miki murna husna Amma dai a kula da aji Kar abada Mata don yadda kike dokin Nan komai Zaki iya.

“To Anty tunda ya furta Kuma wane aji Zan ja mishi Dan bawan Allah? Bari ma in Kai mishi Dan abin motsa Baki sai ta tashi ta fice zuwa kicin ta dauko dambun nama da lemu Mai sanyi ta nufi inda yake ta faman cike ciken takardu

Amal dai sai Rike baki tayi tana mamaki

<< Hawaye 26Hawaye 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×