Katafaren falon ya lashe duk wata kawar da duniya ke yayi tamkar fadar shugaban kasa. Haske tarwai ya haske ko'ina wanda ba za ka banbance Dare ko Rana ba. Sai dai wani abun haushe wani boyayyen gida ne da ba kowa yasan dashi ba koma ace gidane da ba gaskiya tasa aka kera shi ba. Babu kowa acikin sa sai shi kadai Maigidan sai kuma wani katon Maigadi. Yana zaune a falon Yana waya wadda muryar ke fita ta cikin wayar tamkar a gaban shi yake. Wani mutum ne Mai kyawun sura Amma ta fuskar hali da dabia baiyi. . .