Skip to content
Part 36 of 50 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

.”Husna . Ya Kira sunan ta cikin wata murya da akayiwa Ado da sauti shi kanshi Bai San yayi hakan ba sai don zuciyar shi dake Kara kawata mishi yarinyar

Husna ta juyo da sauri tana amsawa inda Kuma haj wasila ta fito tana neman kyas ta fashe.

Ya Miko Mata katuwar wayar ta kamfanin iPhone 9 plus. Husna ta Mika hannu tana karba da jiran ya fada Mata Wanda zata kaiwa.

“Kece naji ance wayar ki taci screen? Tayi saurin kada kanta.

“Bani bace Daddy Anty Amal ce wayar ta ta lalace Kuma har yanzu Bata canza ba……

“To ki Bata Taki ke sai kiyi amfani da wannan.

Kafin ma tace wani Abu haj wasila ta Mika Mata hannu Alamar ta bata wayar, da sauri kuwa ta Mika Mata.

“Daddy sai dai na Bata wannan din tunda Ni tawa batayi komai ba.

Haj wasila tayiwa Husna nuni da ta wuce ta kuwa wuce da sauri don ita kanta ta gaji da wannan banbancin da Daddy ke nuna wa tsakaninta da Anty Amal.

Ada can komai zaiyi musu tare Yake hadawa duk da haj wasila ba so take Yana hada Mata Amal da Husna ba don kallon da takewa Husna Bai wuce agola ba.

Haj wasila ta Soma tudar da ruwan tijara.

“Idan na fahimce ka yadda kaso hadani da Uwar yarinyar Nan ban yarda ba shine makake kokarin cewa yanzu Yar ta kake so? Na fa gama karantar ka Aminu ai Kai da kanka kasan ba Zan yarda ba tunda uwar ta ma sai da na nuna muku ban yarda ba bare yarta da na San komai Akan ta. To ka dawo cikin hankalin ka ko muhsin da naji Yana kokarin shigewa yarinyar ai ba Zan lamunta ba bare Kai kace ita zaka kawo min a matsayin kishiyar ai kasab Albarka ban siyar ba uwar Husna ma Bata da muhalli a gidana bare wata banzar yarta.

Dukkan maganganun haj wasila Babu wadda ta firgita shi irin Jin Wai muhsin ma son husna yakeyi Amma sai yayi maza ya taka Mata burki.

“Ke ya isheki Haka malama !

“Nayi Miki Kama da yaron ki ko danki da Zaki saka Ni Gaba kina min kwakwazo? Ke dai jahila ce wallahi da har kike tada jijiyoyin wuya Akan Yar yarinya Baki San Diyar Halima da mu azu sunfi nawa Diyan da na Haifa acikina ba saboda Aminci?.

“A idonka ne hakan Amma Kuma Ni ko a aikace ba Zan yarda da hakan ba Kuma mu zuba Mana ku rikida dubu Ina Nan Akan daya.

Bisa Dole ya sawo wata wayar ya bawa Amal Amma haj wasila tace ai ita har ta saka layin ta a wannan sai dai ko ya sake siyowa wata ya baiwa Yar gwal din tashi sunan da haj wasila ta kala Mata kenan.

Ai kuwa Tasha mamaki Domin kuwa wayar da ya siyowa Husna ta linka tasu ba don ta so ba Dole ta karba inda kuma ta Soma ganin canji daga Anty Amal tun bata Gane ba har ta gano.

Soyayyar su da Yaya muhsin taci gaba sosai shakuwar ta karu kaunar ma ta karu kulawar ma ta karu kusan a tare suke cin abinci ita ke Kai shi wurin aiki ta Kuma koma ta dauko shi kamar yanzu dai da ta fito tana Kiran wayar shi don ya kusa makara

“Yaya muhsin ka kusa makara fa? Ta fada lokacin da ta Kira wayar shi yake sanar da ita gashi Nan fitowa..

Kusan tare suka taho da haj wasila tana wurga musu harara.

“Ina zakije ne ? Ta jefowa Husna tambayar

“Mami wurin aiki zata kaini ya bawa haj wasila amsa….

“Wane irin Rashin tarbiya ne hakan? Godai godai da Kai zata Rika safarar jelan kaika wurin aiki? Ta juyo tana kallon Husna. “Idan na kuma ganin kin Kai shi Aikin Ranki ne zai baci wuce ki bani wuri.


Da sauri Husna ta juya ta koma ciki. Inda haj wasila ta Raka ta da harara kafin ta juyo ga muhsin.

“Kai Kuma naka salon Haka yazo ? To ka shiga hankalin ka Dani Wallahi in ma wani Abu kake sakawa akan yarinyar can gara ka warware shi don ko Matan Duniya sun Kare ba Zan taba barin ka Auren Husna ba abinda yasa na kyale ka da maganar Safina saboda Naga abin ba mutunci shine kawai Amma da kafin ka dauko min magana sai dai ka wayi gari da Auren Safina Akan ka to ka shiga hankalin ka.

Ta juya ta barshi sake da Baki.

Haka ya SHIGA motar shi ya nufi wurin aiki Yana mamakin mamin tashi Akan abinda take nufi. Shi Kam indai akan Husna ne Wallahi sai dai ta dauki Ran shi Amma Babu gudu babu ja da Baya Akan son Husna.

Da ya samu sarari sai da ya kira Husna Yana Rarrashin ta Akan abinda haj wasila tayi musu Amma ga mamakin shi sai yaji ita Husnar ma kallon hakan takeyi a matsayin tarbiya mamin ke Mata.

Da ya dawo kuwa da sauri ta kinkimo mishi kayan abinci don Bata San kusancin su ke ba a so ba tayi dai zaton zuwa Kai shi aiki ne kawai aka Hana ta ba don Haka sai suka zarce da tsinkar furen soyayya har ta Kai abincin ma sai ta jira shi ya dawo su ci a kwano Daya kuma cikin kulawa ta soyayya suna bawa juna a Baki.

Suna zaune karkashin umbrella iskan maraice na kadawa suna cin abincin Alh Aminu ya shigo gidan cikin mota inda ya hango muhsin na nufar bakin Husna da cokalin abinci inda yaji wani Abu ya daki kirjin shi ya fito motar a zafafe Yana kumfar Baki tamkar zai kifawa muhsin Mari.

“Ashe mutumin banza ka Zama? A gidana zaka nuna wannan dabi ar ta banza? Yayi ta masifa inda ya fafaki Husna ta wuce ciki ta barsu Nan inda Alh Aminu kewa muhsin kashedin Kar ya sake ganin shi da Husna matukar ya sake hakan kuwa to zai bashi mamaki.

Husna take fadawa Anty Amal yadda Daddy ya yi musu inda Amal din ta tabe Baki.

“Husna ki iya takonki don kina dab da fadawa Ruwa. Bana adawa da soyayyar ku da Yaya muhsin Amma zanyi adawa da abinda kike Shirin fada min Baki sani ba. Ba Mami ba Ni kaina ba Zan taba yarda ba bare Kuma Mami don Haka kija jikin ki ina son nayi ta kallon ki amatsayin kanwa ta Kuma me Shirin Auren yayana Amma ban shiryawa kallon ki a matsayin matar uba ba.

A firgice Husna ta dire gaban Amal.

“Don Allah fada min Anty Amal me Kika sani ne Wanda kike tunanin na sani?

Amal ta dafa kafadar ta.

“Husna ke yarinya ce Amma ki lura da wani Abu guda Daya Tak. Duk in kulawa tayi yawa so take Zama kamar yadda Kika damu da kula Yaya muhsin me Hakan ya Zama? Ce mini so. To ki lura da magana ta ki Kuma auna ta ki tace waye ke kulawa da ke irin yadda nake nufi? CE min Daddy kina ga hakan Mai yiwa ne? Husna ta zaro ido bakinta sai karkarwa Yake Amma ta kasa cewa komai.

<< Hawaye 36Hawaye 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×